Balarabe Abdullahi" />

2019; An Bukaci Malaman Jihar Kaduna Da Su Kauce Wa Kalaman Batanci

An bayyana yadda wasu da suke kirar kansu malamai ke fitowa miraratan suna goyon bayan ‘yan siyasa tare da furta kalaman da suke zubar da mutuncin da cewar abin kunya ne ga wadannan malamai da suke jihar Kaduna.
Wani mai tsokaci kan al’amurran yau da kullun mai suna Alhaji Haruna Koca ya bayyana wannan damuwa ta sa a lokacin da ya zanta da wakilinmu da ke Zariya, na yadda kafin zaben shugaban kasa da kuma na majalisun tarayya da kuma na wakilai, malaman suka kama bakinsu, amma da aka motsa domin yin zaben gwamna da na majalisar jiha a mako mai zuwa, sai suka fara motsawa da kuma furta maganganun da ba su dace a ce malamai ne ke furta kalaman ba.
Alhaji Haruna Koca ya ci gaba da cewar, kowa ya san malami babu inda ya ke sauke nauyin da Allah ya dora ma sa sai a munbari, amma saboda abubuwanda suka taso a zabubbukan shekara ta 2015, sai wasu malamai suka canza salon bayyana wasu ra’ayoyinsu a kafafen watsa labara, da
kuma kalaman babu abin da suke yi sai zubar da mutuncin malaman. Ya kara da cewar,bai dace saboda kwadayin abin duniya, a wayi gari malamin da ked a kima a cikin al’umma, ya fito ya na cewar, jam’iyya ka za ta musulmi ne ta kaza kuma ta kirista ne, wanda dukkanin wadannan kalamai, kalamai ne da suke rarraba kan al’ummar jihar Kaduna tare da bayar da gudunmuwar yadda za a yi tashin – tashina a lokutan zabubbuka ma su zuwa a asabar din nan mai zuwa.
A nan ne Alhaji Haruna Koca ya shawarci wadannan malamai da lokaci bai wuce ba, su bayyana wa al’umma su jam’iyya mai alamar kaza suke, daga nan, kamar yadda ya ce, duk kalaman da suka bayyana, babu wani da zai kallesu da wani kaikaiyi a zuciyarsa.
A karshen ganawar wakilinmu da Alhaji Haruna Koca ya shawarci malaman da suke furta kalaman da za su iya wargaza zaman lafiya da kuma fahimtar juna da aka samu a tsakanin al’ummar jihar, da su ci gaba da rike matsayinsu na malamai da hakkinsu ne su bayyana gaskiyar al’umma, kamar yadda mai kowa mai komi ya dora ma su a matsayinsu na malamai da al’umma ke ganin girmansu ba.

Exit mobile version