Muhammad Maitela" />

2019: An Yi Kira Ga Matasa Su Guji Bangar Siyasa

An bukaci matasa su guji ayyukan tarzoma da bangar siyasa, a ruguntsumin manyan zabuka masu zuwa, tare da kiran bai-daya ga yan siyasa da cewa, su ji tsoron Allah; su daina amfani da sabbin jinin wajen rura wutar hatsaniya ta hanyar saya wa matasa kayan maye.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar muryar talaka, na arewa maso-gabas, Alhaji Saleh Bakoro, Sabon Fegi Damaturu, a zantawar sa da wakilin mu a babban birnin jihar. Ya ce ganin wadannan manyan zabuka suna karatowa, ya zama dole su yi wannan kira tare da ankarar da sauran al’umma.
“Ya zama wajibi a daidai wannan lokaci mu yi kira ga matasa da cewa kar su yarda wani dan siyasa ya yi amfani dasu wajen bangar siyasa; domin cimma burin kashin kan sa, alhali yayan sa suna can gida kwance a gidajen alfarma tare da hawa daka-dakan motoci, suna fantama wa. Saboda haka, kar ka yarda a rude ka da kudi komai yawan su wajen tada zaune tsaye”.
“Har wala yau kuma, muna kira tare da bayar da shawara ga baki dayan al’ummar jihar Yobe da cewa a baiwa jami’an tsaro hadin kai, a lokacin gudanar da zaben, domin samun nasarar aiwatar da shi cikin nutsuwa. Domin halin da ake ciki yanzu shi ne, kowanne dan Nijeriya fatan sa shi ne a kammala wannan zaben cikin kwanciyar hankali”. Inji shi.
Da ya karkata kiran sa zuwa ga yan siyasa, Saleh ya bukace su da cewa, su ji tsoron gamuwa da Allah, su dena zama sanadin gurbata rayuwar ya’yan wasu, wanda ya ce yin biris da wannan halin, to suma ya’yan su ba za su tsallake tarkon shaidan ba.
“Domin a musulunci babban kuskure ne mutum ya cutar da rayuwar wani, kuma idan kai ba ka son ka zama mutumin banza, to don me zaka zama musanabin wani ya zama mutumin banza. Wanda bisa hakikanin gaskiya dole a yiwa yan siyasa wannan kashedin, domin a lokuta da dama su ne ke da hannu wajen gurbata tarbiyyar matasa, alhalin sun boye nasu ya’yan”. Ta bakin shi.
Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa rashin aikin yi ga matasa, yana taka rawa wajen aikata manyan laifuka a cikin al’umma: “kamar yadda masana suka tabbatar, kan cewa akwai alaka tsakanin rashin aikin yi da ayyukan tarzoma, wanda idan ka kalli halin da muke ciki a yankin arewa maso-gabas. Saboda haka muna kira ga gwamnatocin tarayya da jiha, su kara kaimi wajen samarwa matasa aikin yi, saboda gaskiya har yanzu da sauran rina a kaba”.
“Kuma muna da kyakkyawar fatan bayan kammala wannan zaben mai zuwa, sabuwar gwamnatin jihar Yobe a karkashin Alhaji Mai Mala Buni ta tashi haikan wajen kirkiro ayyukan yi da hanyoyin rage zaman kashe wanda ga matasa. Dalili, muna kallon sa matashi wanda muke zaton zai baiwa mars da kunya ta bangaren bunkasa rayuwar sabbin jini”.
Sannan ya ce, “kuma a iya sanin mu da Alhaji Mai Mala, shi ne mun san shi jajirtaccen mutum ne, kuma kwararren dan siyasa wanda zai dora daga inda Gwamna Gaidam ya tsaya a ayyukan raya wannan jiha ta mu ta Yobe”.

Exit mobile version