Umar A Hunkuyi" />

2019 : Atiku Na Da Karfin Cin Zaben Fid Da Gwani A Jam’iyyar PDP

Wata kungiiya mai goyon bayan takarar Atiku Abubakar, mai suna, ‘Nigeria Democratic Forum for Atiku Abubakar, SEND-FFAA,’ a jiya ta ce, ta kammala tsara duk yadda Atikun zai lashe kuri’un shiyyar Kudu maso gabas a babban zaben 2019. A cewar kungiyar, tsohon mataimakin Shugaban kasan, Atiku Abubakar, yana da karfin da zai iya kwace shugabancin kasar nan daga Jam’iyyar APC a babban zaben da ke tafe, tana kuma da tabbacin Atikun zai iya kai kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.
Da suke magana da manema labarai a Abakaliki, shugaban kungiyar na kasa, Dakta Chukwu John Aja, cewa ya yi, kungiyar ta kammala tsara dubarun da Atikun zai lashe babban zaben cikin sauki da zaran ya sami tikitin tsayawa takarar daga Jam’iyyar PDP. Aja wanda ya kwatanta Atiku da mara nu na bambanci, ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, bayyanar Atiku a matsayin dan takarar shugabancin kasar nan alheri ne mai girma, musamman ga al’umman Ibo da kuma kasar nan bakidayanta, matukar ya lashe zaben na 2019.
“Atiku ne wanda zai iya magance dukkanin matsalolin da suke addaban kasar nan, zai kuma wanzar da hadin kan kasa musamman ta wajen raba mukaman gwamnati da sauran nade-naden hukumomin gwamnati a matakan gwamnatin tarayya.

Exit mobile version