Connect with us

LABARAI

2019: Babu Wata Jam’iyyar Adawa Da Ke Firgita APC —Lai Mohammed

Published

on

Ministan Yada labarai, Lai Mohammed ya ce, Shakka babu, Jam’iyyar APC ce za ta lashe babban zaben 2019, domin babu wata Jam’iyyar da ke wata jayayya da ita mai karfi.
Lai ya fadi hakan ne sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Benin ranar Asabar, inda ya shugabanci daurin auren dan kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki na Jihar ta Edo, Mariam Abubakar.
Ya ce, Jam’iyyar PDP wacce ya kamata a ce ita ce ma za ta iya wata ‘yar adawa, kanta ba a hade yake ba.
Ya danganta dalilan da za su sanya APC ta ci zabe a 2019 da ayyukan da ta gudanar a shekaru uku baya.
“Muna da tabbacin mutane za su zabi wadanda suka yi masu aiki ne, har yanzun gwamnati ba ta fasa yin aiki ba, za kuma mu ci gaba da gudanar da ayyukan ga ‘yan Nijeriya.
“Gaskiya ni ban ga wata adawa daga Jam’iyyar PDP ba, ‘yan jarida ne kawai suke kiran ta da abokiyar hamayya.
“Muna ta ganin labaran bogi na ta watsuwa, amma mun iya taka masu burki, mun bayyanar da su.
“Amma kar mu manta, labaran bogi ba a nan kasar kadai ake kirkiran su ba. Amma in ba a yi hankali da su ba suna iya hada mutane fada da junan su.
“Gwamnatin tarayya ta kaddamar da yaki kan labaran karya saboda ta san illar su, ta san cewa wasu batagarin suna amfani da wannan hanyar wajen hada fada a tsakanin gwamnati da al’umman ta,” in ji Lai Mohammed.
Ministan ya shawarci ma’auratan da su kasance masu hakuri da juna. Sannan ya kwatanta aure a matsayin cibiyan sanya daidaito da bin juna a cikin al’umma.
“Yi tunanin al’umma ba tare da dabi’ar aure ba a cikinta, ai ba yanda za a sami hadin kai da biyayya a cikin ta.”

Advertisement

labarai