Yasir Ramadan Gwale" />

2019: Daga Ayyana Tsayawar Shugaba Buhari, Sai Kuma Me?

A wannan makon Shugaba Buhari a wajan wani babban taron jiga-jigan jam’iyyar APC, shugaban ya bayyana musu aniyarsa ta sake tsayawa neman zabe a shekarar zabe ta 2019 dake taje a badi. Wannan batu bai zo da mamaki ba, domin da yawa daman ana tsammanin faruwar hakan.

Tun kafin wannan lokaci da Shugaban ya ayyana cewar zai yi takara a zabe mai, tuni masu neman gindin zama, da ‘yan bani na iya, da kuma masu tunanin za su iya ci gaba da al’adar nan ta labewa a bayan Shugaba Buhari su ci zabe suke ta batun idan har yaki bayyana cewar zai tsaya takara to za su maka shi a kotu.

Kusan za a iya cewar yanzu Shugaba Buhari ya katse hanzarin duk wani mai son yin takarar Shugaban kasa musamman a jam’iyyarsa ta APC, wadda ake ganin akwai mutanen da suka nuna sha’awarsu ta yin takara a wannan zabe da yake tafe.

Cikin masu nuna irin wannan sha’awa akwai tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki (duk da yace bai ayyana zai yi takara ba) Ana ganin wadannan da ma wasu za su iya neman karawa a zaben fitar da gwani tare da Shugaba Buhari a zaben da za a yi.

Zamu yi waiwaye kan zaben baya da kuma irin yadda ‘yan Nijeriya suka ci moriya ko akasinta a wannan mulki na Shugaba Buhari a zangon farko. A shekarar zabe ta 2015, da yawan masu neman mukamai a kujerun Sanata da Gwamna da ‘yan majalisun tarayya, sun shiga rigar Buhari ne, inda suka dinga nuna cewar su nasa ne, zabensu kamar zabensa ne, domin shi za su taya aiki.

Amma daga bisani, bayan Shugaba Buhari ya shimfida mulki suka yi wancakali da wannan taguwa ta Buhari da suka sanya. EH, gaskiya ne, ba daidai bane ‘yan majalisun kasa da Gwamnoni su zama ‘yan amshin shatar Shugaban kasa ba, su zama ba ra’ayin al’ummarsu bane a gabansu, kawai me Shugaban kasa yake si shi za a yi ko da kuwa ba shi ne ya dace ba.

Wasu ‘yan majalisun, sun shiga rigar Buhari suka ci zabe, amma daga bisani suka zo babu wanda suke yin adawa ko hamayya da shi sai Shugaba Buhari, duk kuwa da cewar adawa ba wai ana yinta bane domin ci gaban kasa, illa kawai domin wasu bukatun kai.

Bayan haka kuma, Shugaban kasa ya sani, duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ya makogoro ba. Mutanen Arewa su ne suka bashi kaso 70 na kuri’un da yaci zabe da su, amma bisa irin yadda mutane ke yin korafi, shi ne an bar mutanen Arewa wajen cin moriyar ayyukan raya kasa,inda yankunan Yarabawa suka fi kowa rabauta da ayyukan raya kasa na wannan Gwamnati.

Dole ne mutanen Arewa su yi korafi, domin tun da ake yin Gwamnati tun daga 1999 zuwa yau, babu wata Gwamnati da dan Arewa yake jin cewar tasa e 100 bisa 100 kamar wannan, domin mutane suna ganin Buhari ne zai kula da bukatun wannan yanki fiye da duk wani Shugaba da aka taba yi, amma kuma abin yazo da baza ta.

Ya kamata Shugaban kasa ya sani cewar, matukar ba’a juya ko karkata akalar yin ayyuka kamar yadda aka yi a yankin kudu maso yamma zuwa ARewa ba, to mutanen Arewa ba za su taba yafewa Buhari  ba, domin sun fito kwai da kwarkwata suka zabe shi domin cire musu she daga wuta, amma kuma yayi wancakali da dukkan bukatun yankin, wasu mutane da suka raba kafa wajen zabensa sune suke samun moriyar ayyukan raya kasa.

Lallai muna bukatar ganin manya manyan ayyuka wadan da Arewa za ta yi bugun gaba da su wajen nuna cewar dan ta dan Arewa shi ne ya kawo su, ba wani bare ba. Tundaga harkokin ilimi da lafiya da raya kasa, tituna da masana’antu da sauransu.

Sannan kuma, dole Shugaba Buhari ya kiyaye kawowa mutane gurbatattun ‘yan majalisa da Gwamnoni, domin abinda ya farau a baya, wasu suka sanya Sugaba Buhari ya dinga yi musu yakin neman zabe da kansa, suna ta yayatawa a gidajen Radiyo na jihohinsu, karshe suka azo suka zama abokan gabar al’ummar da suke Shugabanta, suna yin abinda aba shi ne zabin al’umma ba, sun fi baiwa bukatunsu fifiko.

Tilas ne, Shgaban kasa yayi takaa tsantsan, wajen marawa irin wadannan baragurbi baya da sunan cewar su ‘yan jam’iyyar Shugaban kasa. Saboda haka kuma, yanzu kan mage ya waye, ya kamata jama’a su bude idonsu, su dena bin innarududu, su tsaya su zabi mutanen kirki wadan da za su tausaya musu su jikansu, a kowacce jam’iyya suke ba lallai sai jam’iyyar da Shugaban kasa yake ciki ba.

Ko ina akwai mutanen kirki kuma akwai baragurbi. Dan haka mutane su gane cewar, koma bayan tunani ne mutum ya dauka jam’iyya kaza ita kadai ce ta mutanen kirki, jam’iyya kaza kuma ta barayi ko mutanen banza, wannana ba gaskiya bane, wasa ne kawai da hankalin jama’ah, kuma babu abinda yake sabbaba irin haka sai jahilcin masu zabe.

Domin babu yadda za a yi, ace idan a jam’iyya kaza ne ba zaka zabi mutum ba, amma idan jam’iyya kaza ne sai ka zabe shi, wannan ya zama wasa da hankali kenan, mutanen anza da dama sun fito daga wasu gurare sun shiga jam’iyya tare da Buhari, an zabe su, sun koma yadda suke a matsayin barayi mabarnata masu ci da gumin talakawa.

Lokaci yayi da za a daina yaudarar masu zabe da sunanBuhari, ko jam’iyyar buhari, inda duk kaga mutumin kirki wanda gaskiyarsa da amanarsa suka bayyana, ko a wacce jam’iyya yake shi ne mutumin da ya kamata a zaba ba tare da wani la’akari da cewar jam’iyyarsa ta saba da ta Buhari ba.

Exit mobile version