• Zan Iya Yi Wa Buhari Kwaf Daya –Kwankwaso
• Ko Gundumarka Ba Ka Iya Kawowa –Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya mayarwa da Kwankwaso martani kan kalaman da ya yi na cewa matukar PDP ta ba shi tikiti zai yi wa Buhari kwaf daya.
Gwamnan ya ce, ko kauyen da ya fito, Kwankwaso ba zai iya cin zabe ba balle ya iya kayar da Buhari a zabe mai zuwa na 2019.
Ganduje ya ce, ta karewa Kwankwaso a siyasar Kano, ba shi da madafa ko kadan, sai dai kame-kame.
Gwamna Ganduje ya yi wannan martani ne a wata takardar manema labarai da Kwamishinan yada labaran jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a jiya. Gandujen ya ce; “Kwankwaso ya rikici a siyasa, domin ba shi da madafa ko kadan, balle wata kwarewar da zai iya yin amfani da ita wurin mulkar Nijeriya.
“Wadannan kalamai da Kwankwaso yayi sun tabbatar da cewa ya rikici, neman dama yake yi da zai dawo da kansa cikin siyasa, da neman suna a wurin al’umma.
“Shekaru uku kenan yana bacci a majalisa ba tare da yin wani abu da zai sauya rayuwar al’umma ba. wanda wannan kadai ya isa ya nuna cewa ba shi da wani abu da zai iya tsinana wa ‘yan Nijeriya.” inji takardar.
A shekaran jiya ne Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya sha alwashin yi wa shugaba Buhari kwaf-daya a babban zaben 2019, matukar dai Jam’iyyar adawa ta PDP za ta ba shi tikitin yi mata takarar shugabancin kasarnan.
Cikin wata tattaunawar da Kwankwaso, ya yi da Mawallafin Mujallar, ‘Obation Magazine,’ ya bayyana tabbacin karfin da yake da shi na siyasa, wanda da shi ne zai baras da shugaba Buhari.
“PDP tana bukatar wani zazzafan dan takara ne da zai fito daga dayan Jihohin nan uku da sunan su ya fara da ‘K,’ Kano, Katsina da Kaduna, domin ta cinye zaben da za a yi a shekara mai zuwa. Domin a nan ne kuri’un suke. Zai yi wahala su ci zabe, matukar suka tsayar da wani daga wajen wannan yankin.
“Zan iya ba su tabbacin dankara Buhari a kasa, matukar suka ba ni daman hakan…”
Da yake bayyana dalilinsa na kin halartar babban taron Jam’iyyar ta APC, Kwankwaso cewa ya yi, ai a fili yake, akwai mutanan da sam ba sa son ganin fuskata a wajen taron.
“Ai duk wanda ya san mutuncin kansa, bai kamata ya tilasta kansa a wajen da ba a bukatarsa ba.”
Kan ko har yanzun yana cikin Jam’iyyar ta APC kuwa? Kwankwason cewa ya yi, “Yanzun ba ni cikin kowace Jam’iyya, ina kuma iya shiga duk inda na so, amma dai na san PDP ce babbar Jam’iyyar da za ta iya yin hamayya, matukar kuma za su amince su yi abin da ya dace, cikin sauki za su iya kayar da Buhari, amma in suka dankara wa mutane dantakarar da suka ga dama, tabbas za su ci kasa.
Sanata Kwankwaso, ya yi ikirarin shi ya shirya Jam’iyyar ta APC a Jihar Kano, wanda hakan ne ya baiwa shugaba Buhari nasarar cinye zabe, ya kuma yi nu ni da cewa, har yanzun kuma yana da wannan karfin da zai iya yin bazata wajen lashe kowane irin zabe.
Kwankwaso ya ce, mawuyacin abu ne Buhari ya sake samun irin nasarar da ya samu a Jihar ta Kano, alhalin yana yakarsa da wanda ya gada, Ibrahim Shekarau.