Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

2019: Gwamnonin PDP Na Goyon Bayan Garzayawar Atiku Kotun Koli

by
3 years ago
in LABARAI
2 min read
PDP Ta Ba Matawallen Maradun Tikitin Takarar Gwamnan Zamfara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya sun ba da kwarin gwiwar cewa jam’iyya ta daukaka shari’ar zaben Shugaban Kasa da aka yi a makon da ya gabata. A wani jawabi da gwamnonin jam’iyyar su ka fitar ta bakin Shugabansu Mai girma gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, sun nemi a koma kotu domin a cewarsu ta haka za a ceto damukaradiyya.

Jawabin ya nuna cewa muddin PDP ba ta daukaka kara ba, za a bar damukaradiyya cikin wani irin rudani don haka su ka nemi zuwa kotun koli domin a soke zaben bana, abin da kotu ba ta taba yi ba. Wannan na zuwa ne bayan gwamna Nyesom Wike na PDP ya fito gaban duniya ya taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar nasarar da ya samu a gaban kotun da ya saurari karar zaben na 2019.

PDP ta yi wannan jawabi ne Hedikwatarta da ke babban birnin Abuja ta hannun gwamnan jihar Bayelsa inda ta ke cewa bayan dogon tunani, ta gano ya kamata su daukaka kara a kotun gaba. Gwamnonin su ke cewa: “Ba mu yi wa kan mu da jam’iyyarmu adalci ba idan mu ka juya kai a lokacin da damukaradiyya da mutanen Najeriya su ke fuskantar mummunan hawan kawara.” Dickson ya kara da cewa: “Mu na sa rai cewa kotun koli za ta rubuta sunanta a tarihi ta hanyar goge dattin da aka goga mata, kuma ta san cewa martabar ta a idanun jama’a ya na lilo a kasar.”

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Zazzau Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Jama’atu Na Kai Karar Sarkinta

Kamfanin Simintin Dangote Ya Samu Ribar Biliyan 410 A Wata Uku

Gwamnan gwamnonin na PDP ya tufe jawabin na sa da cewa wannan shi ne matsayarsu inda ya kara jaddada goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar da Peter Obi a babban zaben na 2019.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kakakin Majalisar Wakilai Zai Koyar A Sakandaren Katsina

Next Post

Abuja Ba Ta Fuskantar Mamayar Masu Garkuwa, Cewar ‘Yan Sanda

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Zazzau Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Jama’atu Na Kai Karar Sarkinta

Masarautar Zazzau Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Jama’atu Na Kai Karar Sarkinta

by Abubakar Abba
3 hours ago
0

...

Kamfanin Simintin Dangote Ya Samu Ribar Biliyan 410 A Wata Uku

Kamfanin Simintin Dangote Ya Samu Ribar Biliyan 410 A Wata Uku

by
7 hours ago
0

...

Mutum 5 Sun Mutu Kan Rikicin ‘Yan Kasuwa Da ‘Yan Babura A Abuja

Mutum 5 Sun Mutu Kan Rikicin ‘Yan Kasuwa Da ‘Yan Babura A Abuja

by
8 hours ago
0

...

Ministar Kudi Ta Dakatar Da AKanta Janar Na Kasa Kan Zargin Badakalar Biliyan 80

Ministar Kudi Ta Dakatar Da AKanta Janar Na Kasa Kan Zargin Badakalar Biliyan 80

by
9 hours ago
0

...

Next Post
shugaban rundunar yan sanda

Abuja Ba Ta Fuskantar Mamayar Masu Garkuwa, Cewar ‘Yan Sanda

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: