Rabiu Ali Indabawa" />

2019: Gwamnonin PDP Na Goyon Bayan Garzayawar Atiku Kotun Koli

Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya sun ba da kwarin gwiwar cewa jam’iyya ta daukaka shari’ar zaben Shugaban Kasa da aka yi a makon da ya gabata. A wani jawabi da gwamnonin jam’iyyar su ka fitar ta bakin Shugabansu Mai girma gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, sun nemi a koma kotu domin a cewarsu ta haka za a ceto damukaradiyya.

Jawabin ya nuna cewa muddin PDP ba ta daukaka kara ba, za a bar damukaradiyya cikin wani irin rudani don haka su ka nemi zuwa kotun koli domin a soke zaben bana, abin da kotu ba ta taba yi ba. Wannan na zuwa ne bayan gwamna Nyesom Wike na PDP ya fito gaban duniya ya taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar nasarar da ya samu a gaban kotun da ya saurari karar zaben na 2019.

PDP ta yi wannan jawabi ne Hedikwatarta da ke babban birnin Abuja ta hannun gwamnan jihar Bayelsa inda ta ke cewa bayan dogon tunani, ta gano ya kamata su daukaka kara a kotun gaba. Gwamnonin su ke cewa: “Ba mu yi wa kan mu da jam’iyyarmu adalci ba idan mu ka juya kai a lokacin da damukaradiyya da mutanen Najeriya su ke fuskantar mummunan hawan kawara.” Dickson ya kara da cewa: “Mu na sa rai cewa kotun koli za ta rubuta sunanta a tarihi ta hanyar goge dattin da aka goga mata, kuma ta san cewa martabar ta a idanun jama’a ya na lilo a kasar.”

Gwamnan gwamnonin na PDP ya tufe jawabin na sa da cewa wannan shi ne matsayarsu inda ya kara jaddada goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar da Peter Obi a babban zaben na 2019.

Exit mobile version