Connect with us

SIYASA

2019: Hana Sanya Fosta Ba Zai Hana Mu Cin Zabe Ba, Inji ADP

Published

on

An kira ga ‘yan takarkaru da ke sha’awar tsaya takarar mukaman siyasa a zabuka masu zuwa musman a inuwar ADP da su hada kai su zauna lafiya. Domin rashin hadin kai da yada bambance bslambance a tsakanin ‘yan takara bai haddasa komai sai koma bayan jam’iyya. Shugaban jam’iyyar ADP na jihar Neja, Kwamared Tanimu Sarki Kwamba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karban takarar neman takara da dan takarar kujerar gwamnan Neja, Barista Bello Bawa Bwari.

Sarki Kwamba ya jawo hankalin shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su kaucewa daukar bangare na ‘yan takarar gwamna domin duk kansu na su ne, yace muna da ‘yan takarar kujerar gwamna guda uku a jam’iyyar nan ba a yi zaben fidda gwani ba, duk kansu kuma ‘yayan jam’iyya ne ya zama wajibi mu rungume su gaba daya hakan ne zai ba mu hadin kai da samun nasara a babban zabe mai zuwa.

Da yake karin haske, kodinetan kamfen din Barista Bello Bwarin, Alhaji Isah Laje, ya bayyana cewar hana sanya fostan ‘yan takara ba zai hana su kafa gwamnatin APC a jihar ba, yace yanzu wai sanya allon dan takara sai ka biya naira miliyan daya a jihar nan, wanda a dokokin kasar nan ba bu inda aka ce dan kana sha’awar yin takara sai ka biya kudi za ka tallata kan ka.

Abinda muke tambayar gwamnatin jiha, shi ne kudin faris kulub da aka kasa yin aikin raya kasa da su, shi ne yau ake lalubar ‘yan adawa su kawo kudin da ba su ne suka ci ba dan tsoron kar a lalubo su bayan sun bada mulki alhalin ba a san yadda aka kashe su ba. Neman kudi a hannun ‘yan takara na jam’iyyun adawa ba shi ne zai sa gwamnatin ta zarce ba.

A na shi jawabi, dan takarar, Barista Bello Bawa Bwari, ya bayyana cewar shi ba irin ‘yan siyasar nan ba ne marar alkawali, duk alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, in har Allah ya ba shi wannan kujerar zai tabbatar ya mayar da hankalin sa wajen ayyukan raya kasa, ilimi, kiwon lafiya da harkar noma.

Yace ADP ba jam’iyyar adawa ba ce face mafita ga halin da jihar Neja ke ciki, zamu bullo da hanyoyin da zasu dakile fatara, talauci da rashin aiki da ke zama barazana mata da matasan mu. Ina kira ga mata da su fito dan yin takarar siyasa domin fom dinsu kyauta ne, sune jigo kuma kashin bayan cigaban kowace irin al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: