2019: Idan An Zabe Ni Zan Habaka Ayyukan Noma A Yobe – Mai Mala Buni

Dan takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, ya dauki alkawari da cewar, idan ya samu nasarar dare kujerar gwamnatin jihar- a wannan zabe mai zuwa, zai kawo gagarumin sauyi a sha’anin noma ta hanyar hada hannu da karfe da gwamnatin tarayya a haujin.
Mai Mala ya bayyana kakan a garin Damagun, a lokacin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC, tare da ankarar da cewa, wadannan muhimman tsare-tsare a sha’anin noma, wanda gwamnatin sa za ta aiwatar, idan ya samu nasara- da bayyana cewa za su yi tasiri wajen karfafa jama’ar jihar da bunkasa ci gaban jama’ar.
Ya bayar da misali dangane da tsarin gwamnatin tarayya na baiwa manoma bashi, da ke gudana na a fadin kasar nan ‘Anchor Borrowers Programme’ (ABP) shirin da ya ce ya bunkasa aikin noma da ci gaban yan kasa, inda ya shaidar da cewa akwai bukatar bunkasa shi, a matakin jihar.
Har wala yau kuma, Alhaji Buni ya sha alwashin hadaka ayyukan noman rani a fadamun da Allah ya albarkaci jihar dasu, inda ya ce wannan zai bayar da damar bunkasa samar da kayan abinci tare da tattalin arzikin jama’a.
“Kuma za mu tabbatar da cewa mun yi amfani da matasan mu gadan-gadan a ayyukan farfado da ci gaban tattalin arziki tare da cin gajiyar fasahar da Allah ya uface musu, wajen amfanar da al’umma”. Inji Yallabai.
“Sannan kuma wannan gwamnatin matasa ce, kuma ko shakka babu, matasa ne za su yi kane-kane a rike manyan mukamai a cikinta, domin su bayar da gagarumar gudumawa a ci gaban al’ummar jihar su”.
A hannu guda kuma, dan takarar gwamnan jihar Yoben, ya yi alkawarin dora ayyukan gwamnatin sa daga inda gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ta tsaya.
“Kuma za mu dora ayyukan mu ne daga nasarorin da gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ya samu a bangarorin kiwon lafiya, ilimi, samar da gidaje da makamantan su”. Inji Buni.
Mai Mala Buni ya bukaci al’ummar jihar da cewa su zabi ilahirin yan takarar jam’iyya APC, a wannan zabe mai zuwa. Ya ce, hakan ne zai baiwa bangarorin gwamnati mai zuwa damar gudanar da ayyukan su kafada da kafada, kuma a cikin tsanaki.

Exit mobile version