Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben shekara ta 2019 duk da jinkirin da ta samu wajen amince wa da kasafin kudinta.
Haka kuma Hukumar ta ce jinkirin sa hannu a dokar da aka gyara shi ma ba zai hana ruwa gudu ba wajen yin wannan zabe mai zuwa.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka ga manema labarai a wajen wani taron kara wa juna sani wanda ya gudana a Abuja jiya Juma’a.
Ya ce Hukumar ta tattauna da ma’aikatar kudi domin samar da kudaden da za a gudanar da wannan zabe kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma ci gaba da cewa, tuni Hukumar ta bayar da kwangilar sayo kayan aikin da za a gudanar da wannan zabe da su. “Muna kuma fatan cewa a cikin makon farko na watan Disamba wadannan kaya za su iso.
“Za kuma a yi wannan zaben ne ranar 16 ga watan Fabarairu zuwa 2 ga watan Maris, saboda haka muna ganin ba za mu sha wahala ba.