Connect with us

HANGEN NESA

2019: Kifar Da Gwamnatin Buhari Ne Babban Kuskuren Da Talakawa Za Su Yi

Published

on

Duk da cewa akwai wasu kurakurai da Gwamnatin Baba Buhari take tafkawa, amma ‘yar manuniya ce a fili samun wanda zai ci gaba da irin ayyukan Shugaba Buhari na da wahala. Wanda karshe idan ba a yi karatun ta nutsu ba, dawo da jam’iyyar PDP kan mulki, zai iya dawo da mu gidan jiya.

Da kyar TALAKAWA suka kifar da gwamnatin jam’iyyar da akace sai tayi shekara 60 akan mulki, bayan ta rugurguza duk wani ci gaba da ake tunanin samu daga 1999 har zuwa 2015. P. D. P ta aikata kwamacala, tayi wannan wadaka da kudin al’umma tare da sace lalitar gwamnati, bayan karya komadar harkokin lafiya, ilimi da tsaro. Shekaru akalla sha shida suna kan mulki babu wani abu da suka tsinana banda cin fuskar TALAKAWA tare da juya musu baya, bayan asarar dubunnan rayuka da aka yi karkashin Gwamnatinsu, wanda a tarihin dimokradiyya za a dade ba’a manta da wannan ta’adi da barnar da aka yiba.

Idan muka kalli tsahon shekaru uku da Shugaba Buhari yayi, yayi kokari wajen maida hankali kan tattalin arzikin kasa, duk da cewar an shiga halin ha’ula’i a tattalin arzikin kasar, amma gyara harkar noma, zai taimaka wajen rage radadin talauci da ake fama dashi a kasar.

Idan har shirin gwamnati na maida hankali kan noma fiye da harkar man fetur ya cimma nasara, kasar mu za ta kasance tilo a Afrika da za ta iya ciyar da al’ummar ta har ma ta yi kasuwancin sa zuwa wasu kasashe, sannan hakan zai kawo karshen siyo kayan masarufi daga kasashen ketare, sannan zai bada damar rage farashin kayan masarufi wanda talaka zai iya ciyar da iyalin sa arana sau uku.

Sannan hakan zai rage yawan hauhawar farashin kayan masarufi. Wannan shi ne babbar illar da gwamnatin PDP tayi mana wajen dogara da dakon kayan masarufi daga ketare masu tsada, alhalin munada manoman da za su iya noma abinda muke bukata, sannan Allah yahore mana kasar nomar da zamu iya noma dukkanin wani kalar kayan masarufi da ake shigo dashi.

Babban abinda kowace Gwamnati ta ginu shi ne hanyar samar da tattalin arzikin da TALAKAWA za su amfana, dogaro da harkar mai abu ne da aka dade ana yi, amma akwai manyan kasashe da suke ciyar da kasar su da kasuwanci na kashin kansu batare da dogara da man ba. Duk kasar da dogaron samun kudin shigarta ya kasance yana rawa, talauci da fatara sune za su dirar wa wannan al’ummar, sannan dukkanin wani bangare da yake da mahimmanci zai samu ragwanci ta hanyar da za a kasa cimma bukatun talakawa, kamar ilimi da tsaro.

Tanadin da yake kasar nan daga nan zuwa 2025 shi ne, yanda kasar za ta iya cimma muradun ta bayan darajar man fetur ta fadi war was a duniya. Gwamnatin PDP batada wani shiri don tunkarar inda za ta durfafa bayan darajar man fetur tafadi a duniya, yayin da suka maida hankali wajen gina kawunansu dana makusantansu, suka dinga siyan manyan gidaje a kasashen ketare tare da cilla kudaden su manyan bankunan duniya don shirin kota kwana, alhalin sunada masaniya kan irin halin da kasar za ta shiga. Basu dauki darasi daga kasar Amurka ba, wacce ta tanadi shirin tada komadar tattalin arzikin ta lokacin Shugaba Barrack Obama.

Duk da Shugaba Buhari yasamu kasar cikin halin rashin tsaro tare da samun raguwar farashi man fetur kan kowace ganga. Karkatar hankalinsa wajen harkar noma shi ne wata hikima da har aka samar da dawwamammen tsaro ba kamar lokacin Gwamnatin Mai Malafa ba, anyi amfani da sakonnin sirri, da kuma amfani da kwarewa don ragewa barandan Boko Haram karfi.

Kwatsam sai ga rikice-rikice na manoma da makiyaya, sace-sacen al’umma da kuma kisan kiyashi a zamfara da birnin gwari, dukansu idan muka kwatanta da wata biyar da suka wuce da yanzu, munsan sauki yasamu, kuma hare-haren bama-bamai sun zama tarihi. Tsaro a yanzu zamu iya cewa yafara samun gindin zama idan shima aka kwatanta da Gwamnatin baya.

Kokarin da Shugaba Buhari yake kusan yana samun tangarda ne kawai daga wasu makusantansa wadanda ba kasar ce gabansu ba, wannan shiyake kawo kwan gaba kwan baya a wasu bangarorin musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa. Ilimi har kawo yanzu yakasa samun wani tagomashin daya dace saboda rashin kwarewa ta Ministan Ilimin kasar.

Shirin kara karfin samuwar wutar lantarki da Shugaba Buhari yake na daya daga cikin manyan ayyuka da Gwamnatin PDP ta kasa tsahon shekaru 16, bayan wadakar biliyoyin nairori da Gwamnatin Obasanjo tayi da kuma badakalar Halliburton, wannan kadai yanuna yanda akaci amanar talakawa aka karkatar da kudaden su. Samar da injinan hakar man fetur suma wani shirine na Gwamnatin Buhari wanda zai taimaka wajen rage cinkoson samar da man fetur a kasar, wanda hakan na cikin dalilan karancin man da kuma tsadar farashinsa ga TALAKAWA.

Kokarin hada alakar kasuwanci da kasashen sin da morokko, zai taimaka wajen kara habakar tattalin arkizin kasar nan, wanda hakan zai taimakawa gwamnati wajen cimma muradun sauya rayuwar al’umma.

Allah Ubangiji ya taimaki kasar mu.

Advertisement

labarai