Hajiya Fatima Yawale Dasin, baya ga kasancewarta ‘yar gani-kashenin shugaba Muhammadu Buhari, fitatciyar ‘yar siyasace da ta jima ana fafatawa da ita a jihar Adamawa, ta kuma tsaya takaran kujeru amatakai da dama a karamar hukumar Fufore, yanzu haka dai itace mataimakiyar shugaban jam’iyyar APC ta Adamawa ta tsakiya. LEADERSHIP Ayau ta samu zantawa da ita kan al’amura da dama, musamman gazawar da’ake ganin APC tayi na shawokan matsalolin kasa da shirinta na tsayawa takarar kujerar ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar Fufore/Gurin da Song a majalisar wakilai ta kasa.
Hajiya wasu na ganin kamar ba wani abun azo agani da gwamnatin apc ta tabuka cikin shekaru biyu me za ki ce?
To, Alhamdulillahi, shekaru biyu na jami’iyyar APC kan karagar mulki ta yi rawar gani, Adamawa gaskiya mun samu canji, duk wanda ya shigo Adamawa cikin shekaru biyun nan ya san lallai Adamawa ta canja, da bamu da hanyoyi masu kyau yanzu Alhamdu lillahi hanyoyi ga wutan kan hanya ‘Street light’, idan ka shigo cikin gari gaskiya ka san lallai Bindow ya yi aiki, mun gode masa.
Eh, jiya mun yi mitin dashi (Bindow), mu jam’iyya Kenan, ya yi alkawari zai biyu kuma an fara biya tun a jiya din. Don haka ina ganin in sha Allahu zai biya duk basussukan da ma’aikata ke bin gwamnati nan bada jimawa ba, da izinin Allah.
Kinyi maganar APC ta yi rawar gani cikin shekaru biyu, ko za ki bayyana wasu ci gaba da aka samu a shekaru biyun?
Eh, kowa ya san APC ta yi rawar gani, musamman mu mutanen arewa maso gabas kowa ya san abin da ke faruwa a Arewa maso Yamma, batun Boko Haram da sauransu, lokaci daya Baba Buhari bai yi shekara daya ba ya gama das u, wannan Alhamdulillahi, ka duba matan Chibok ba lokacinshi aka sace su ba amma cikin yardan Allah yanzu haka an karbo sama da 100, ka ga shima abin yabawa ne, sannan mun ga canji na rayuwa da yawa a mulkin Baba Buhari, idan ba a gode mishi ba gaskiya sai dai mutum ya yi shiru, ni Alhamdu lillahi na gamsu da mulkin Buhari duk wani talaka kuma ya gamsu da mulkin Buhari, mun gode Allah muna mishi Addu’ar ya cigaba da ayyukan da ya ke yi.
Koke-koke da talauci sai karuwa suke a wajen jama’a kuma a karkashin wannan gwamnatin da kike karewa, ba ki ganin shagube kawai kike yiwa ‘yan Nijeriya?
A’a babu, ka duba gwamntin PDP ta shekara 16 a cikin wannan shekarun ba abin da ta ke yi in banda sata, kai dan Nijeriya ne ka sani ba sai an gaya maka ba ka san irin barnan da PDP ta yi, kuma kana ganin kudaden da Buhari yake kwatowa yanzu a hanun mutane, za ka ga mutum yaje ya tona kabari ya zuba kudin al’umma a ciki, ai duk dan Nijeriya da yake kuka da wannan gwamnatin bai yi mana adalci ba, duk wani mutum da zai yi kuka da mulkin Buhari bai yiwa kanshi adalci ba, ka duba kudaden da’ake kwatowa ai kudaden talakawa ne, da mukazo gwamnatin mun samu babu komai a cikinta ba don Allah yasa Buhari wani irin mutum bane da bamusan me zai kasance ba, kuma da PDP ne ta dawo ina tabbatar maka da yanzu mu Adamawa watakila ba ma nan kuma talakan da yake kuka da ba zai iya bude baki ya yi magana ba domin sai in akwai rai da lafiya ake batun abinci, so duk wani surutun da ake yi wallahi dan adam ne da ba za ka iya mishi ba, ni gwamnatin Buhari ba don ina ciki ko don ni ‘Die-hard’ na Buhari bane nake magana ina magana ne akan gaskiya, Buhari Alhamdu lillahi ya kawo mana zaman lafiya Buhari ya kawo mana canji a Nijeriya mun gode mishi, kuma na tabbata daga shekaran nan kowa zai ga canji a kasa don ma rashin lafiyarshin nan ne, amma zuwa 2018 zai gama kwace kudin ‘yan Nijeriya da a sace kuma zai yi musu aiki dashi, abinci zai wadatu duk abubuwan da ake kuka akai zai ragu, don ‘yan kasuwanmu suna daya daga cikin masu sake jefa jama’a cikin kuncin rayuwa, wai dala ya hau abin da zaka saya akan kudi kalilan sai ya gagare ka saye, ko suna neman riba ne ko don su batawa baba Buhari suna ne…
Don haka ‘yan kasuwa suna daya daga cikin masu kara tsadar rayuwa ga jama’a, so mutane su ji tsoron Allah, Buhari ya zo ya taimakemu ne Buhari bai zo ya tara kudi ba don abin duniya bashi ne damuwar Buhari ba.
A bangaren ku mata misali me za ki bayyana da kike ganin za ku yabawa gwamnatin a kai?
Mata da dama na koke-koken cewa ba a yi da su a wannan gwamnatin?
Eh to, yanzu kaman a Adamawa, muna da mata biyu a majalisar dokokin jihar kuma muna da mace daya a ta wakilai muna kuma Sanata, sannan a kwamishinoni akwai mata a cikin masu ba Bindow shawara, haka kuma a tarayya mukamai manya-manya mata sun rike Alhamdulillahi, ni a nawa ganin Buhari ya yi kokari ta nan, kuma in ka duba matan arewa ba su da yawa a gwamnatin da ta wuce amma yanzu haka matan arewa da yawa sun shiga wannan gwamnatin, Alhamdu lillahi mun godewa Baba.
Kamar me za ki nuna cewa gwamnatin tarayya ta yi domin tallafawa mata a yankin arewa maso gabas?
A kwai sosai ma kuwa, mace da tana gida idan mijinta ko danta ya fita hankalinta a tashe, ni da ko masallacin juma’a dana zai tafi ina kokwanto amma yanzu Alhamdullahi ko wani lokaci yaranmu suna fita mazajenmu suna fita kuma suna dawowa gida lafiya wannan ma abun alfahari ne, da kai namiji baka isa ka fita waje ba kana yawo kana dar-dar saboda halin da muka shiga a Northeast, amma cikin kankanin lokaci Allah ya kawo mana sauki, dama mun roki Allah ya kawo mana Buhari Allah ya kawoshi Allah ya share mana hawayenmu Buhari ya share mana hawaye.
Sannan batun noma kai kanka kasan an samu canji, ka duba da ba wanda ya damu da noma amma ka duba yanzu a haka irin noma rani da na daminan da’akayi da irin ci gaban da’aka samu, wanda inda za’a ci gaba da haka wallahi babu wanda zai nemi abinci a kasar waje, sannan batun wutar lantarki ni rabon da inga wuta haka tun 1991-2, amma yanzu wuta Alhamdulillahi awa 24 muna da wuta, ka duba hanyoyi a Federal wanda Buhari ya yi, sannan akwai tallafi wanda ake yiwa mata ta ministry of women affairs an kawonan jihar mun fara, za ayi a jihohin bakwai da matsala ‘yan bindiga ya faru da su yanda za a tallafawa mata, mun baiwa mata sun cike fam kuma na san za a ga wannan kudin a cikin asusun domin mata su dogara da kansu, kaga wannan tsarin bamu taba ganin irinsa ba.
Ku ‘yan jam’iyyar ma wasunku na kukan ba a yi da ku?
Alhamdulillahi ana yi da mu jam’iyya. Mu mune Buhari tun ANPP har zuwa CPC zuwa APC yanzu, mu ne APC domin mu muka samar da APC, duk wanda yace maka ba a yi da jam’iyya yana waje ne bai san me ake yi ba; amma mu da muke cikin jam’iyya mun san me ake ciki, yanzu Kaman a jiha na gwamna kullum yana cewa muyi hakori bari ya yi aiki na shekara biyu, idan ya yi aiki na shekara biyu zai dawo yawaiwayi jama’a mu dama burin jam’iyya bawai a bamu kudi ko wani abu ba, a’a, a yaba mana gwamnanmu ko shugaban kasarmu cewa sun yi aiki shi ne a gabanmu, kuma Alhamdu lillahi Buhari ya yi aiki Bindow ya yi aiki, shi yasa muke musu fatan su maimaita mana dukansu, ni addu’a na Allah ya bawa Buhari lafiya ya bamu nisan kwana 2019 mu sake zabenshi ya zarce mana Nijeriya ta dawo daidai don daukan da yake ciki yanzu ya fara wankewa.
Me ya baki sha’awar shiga harkar siyasa ne?
Gaskiya na shiga siyasa saboda Buhari ne. ni tun ina yarinya lokacin da Buhari yake mulkin soja akwai abu biyu da yayi wanda suka burgeni, na daya ranar Asabar Karuwai suna fita suna yin shara kowa ya san abubuwan da suke yi ba shi da kyau, na biyu ya hana yara talla wadannan suna daga cikin abin da ya sa Buhari ya shiga raina tun ina yarinya karama. Kuma ni siyasa gadonta na yi domin babana dan siyasa ne, amma siyasarshi baitaba bani sha’awa ba; saboda PDP ya ke yi hatta ciyaman na PDP ya rike, lokacin zaben Buhari da Obasanjo na biyu na ce ba zan zabi Obasanjo ba yace dole zan zaba na ce saidai kada inyi zaben kwata-kwata Mamana ta ce a barni na zabi wanda na ke so, na je na zabe Buhari lokacin ne na fara yin zabe a rayuwana. To na rasa me zanyi na taimakawa Buhari don haka na shiga siyasa na shiga fatin da yake a ANPP a lokacin ban taba zuwa fati ofis ba, amma duk wata harka na Buhari ina cire kudina in taimaka dashi, har aka zo CPC a kananan hukumomi 21 mu muka bude ofishin CPC da kudinmu mukayi komai na Buhari har gobe kuma inakai, ko na wa in dai ina dashi zan kashe akan Buhari saboda mutum ne mai gaskiya kuma ni duk inda gaskiya ta ke ina wurin.
Kamar menene burinki a siyasa?
Burina yanzu haka ina da muradin na taimakawa matasa da mata, na tsaya zabe ba sau daya, ba sau biyu ba.Yadda Buhari ya yi ta faduwa ya na hakuri haka nima, a 2019 zan sake tsayawa saboda in ga na tallafawa matasa da mata. Su san menene dimokradiyya don mu a Fufore/Gurin bamu san menene dimokradiyya ba har yanzu, ina son in kawo canji a san menene dan majalisa zai iya yiwa mazabarsa, ni burina na ga matasa suna cikin walwala sun samu aikin yi. Za ka ga wani yaron yana son yin karatu ba shi da halin yi za ka ga yaro yana da buri masu kyau a zuciyarshi amma babu hali, sai ya shiga shaye-shaye ina son in Allah ya bamu wannan kujerar mu kawar da wadannan, don haka na tsaya 2015 amma da yake kasan idan kuna tafiya a tare, daya zai janyewa daya to don haka na janye ma wani, amma wannan karon, shekarar 2019, shekara ta ce. Ni ce zan zama memba ba zan janyewa kowa ba.