Yusuf Shuaibu" />

2019: Masu Sa Ido Sun Yaba Da Yadda A Ka Gudanar Da Zabe

Masu saka ida a kan zabe tare da kungiyoyin farar hula suna ci gaba da magana a kan yadda babban zaben na ranar Asabar ya gudana. Kungiyoyin sun yaba da yadda zaben ya gudana.
Kungiyar lauyoyi na Nijeriya wacce ta yi magana a kan dage zabe, inda ta zargi hukumar zabe a kan tana kokarin kawo rikici.
Kungiyar ‘Centre for Law Enforcement and Education, (CLEEN)’ ta bayyana cewa, ta saka ido a wurare da dama a lokacin wannan zabe. Shugaban kungiyar Benso Olugbuo, ya bayyana cewa jami’an tsaro tare da sauran hukumomi sun isa runfunar zabe tun da wuri. “Rahoton da muka samu daga wajen wakilanmu a fadin kasar nan ya nuna mana cewa jami’an tasro sun isa runfunar zabe tun da wuri,” in ji Mista Olugbuo.
“Alal misali, kashi 21 cikin 100 sun isa runfunar zabe tun da misalin karfe 7 na safe, yayin da kasha 44 suka isa da misalin karfe 7.59. kashi 31 na jami’an tsaro su isa ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na safe daga baya.”
Game da isar jami’an tsaro, kungiyar CLEEN ta bayyana cewa, a wasu runfunar zabe an ijiye jami’an tsaro da yawa, yayin da kuma wasu runfunar aka ijiye guda daya. “Kungiyar CLEEN ta kara da cewa, kashi 39 na runfunar zabe an girke jami’an tsaro uku ko kuma fiye da haka domi su kare masu jefa kuri’a tare da kayayyakin zabe da kuma kare doka da oda.
“Bugu da kari kuma, kashi 31 na runfunar zabe an girke jami’an tsaro guda biyu ne kawai, domin su kare masu saka ido kayayyakin zabe da kuma kare doka da oda a wannan yankin. Masu saka idanmu sun bayyana cewa, wasu daga cikin runfunar zaben suna karkashin kulawar ‘yan sanda. Wannan shaida dai mun samo su ne daga hannun masu saka idanunmu, kashi 27 na runfunar zabe jami’an ‘yan sanda guda daya ne aka girke,” in ji kungiyar.
Kungiyar CLEEN ta bayyana cewa, ma’aikatan zaben sun nuna da’a wajen gudanar da aikin sui, kashi 80 na mazu zabe sun samu tsaro lokacin da ake zaben.
A wani lamari irin wannan dai, kungiyar Transition Monitoring Group (TMG), tare da masu saka ido kan zabe, sun bayar da rahoto a ranar Asabar da yamma tare da wata kungiya mai suna Human and Enbironmental Debelopment Agenda (HEDA).
A bayanan kunyiyoyin guda uka wanda shugaba Abiola Akiyode-Afolabi da kuma Suraju Olanrewaju suka rattaba hannu, sun lissafa abubuwa kamar haka,
“Ma’aikatan zabe da kuma kayayyakin zaben sun isa latti a wasu mazambu da sanar da sakamokon zaben latti shi ya janyo rikici a wasu mazabu. “Tursasa wa masu zabe, yunkurin tarwatsa zabe, amshi sakamakon zabe na ‘yan barandar siyasa, yin amfani da kayan sojoji ko kuma na ‘yan sanda a wasu wurare.”
Kungiyoyin sun kuma bayyana cewa, tsayawar da na’urar tantace masu zabe a wasu wuraran shi ma ya kawo rikici.
Wasu kungiyoyin kamar na Youth Initiatibe for Adbocacy, Growth da kuma Adbancement (YIAGA), sun bayyana cewa an samu karancin fitowar masu zabe na ranar Asabar. Kungiyoyin dai sun bayyana wannan lamarin ne ga manema labarai a ranar Asabar. Sun bayyana cewa shaidar da suka samu ya nuna masu cewa wannan zabe bai kammala ba. Wannan ya nuna irin yadda ‘yan Nijeriya suka rabu da harkokin siyasa. “Kungiyar YIAGA AFRICA ta yi kira ga dukkan manyan jam’iyyu a kan wannan zabe, su kara kaimi wajen ballo da tsari wanda zai amfani yankunansu,” in ji Mutanen Nijeriya.”

Exit mobile version