Nasir S Gwangwazo" />

2019: Matasan Arewa Na Son PDP Ta Nemi Afuwar Aliyu Manji

Majalisar Zumunta da Ci gaban Jam’iyyar PDP ta Gamayyar Matasan Arewa mai suna ‘PDP Northern Youths Alliance Group’ ta bukaci jam’iyyar PDP ta kasa da ta hanzarta neman afuwa tare da bayar da hakuri ga daya daga cikin jigogin jam’iyyar PDP a Arewa maso Gabashin Najeriya, Alhaji Aliyu Manji, wanda ya taba tsayawa takarar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa a yankin Arewa.

Shugaban Majalisar Kungiyar ta Matasa na yankin, Alhaji Mustafa Mallah Goni, ne ya bayyana haka a lokacin gudanar da taron hadin kai da ci gaban yankin Arewa maso Gabas na jam’iyyar PDP a garin Bauchi.

Majalisar Matasan ta nemi da a gaggauta nemo hanyoyin gyaran kura-kuran da aka tafka a lokacin zaben sabbabin shugabanin jam’iyyar na kasa a Abuja ta hanyar sulhuntawa da neman gafara ga wadanda aka yiwa rashin adalci a lokacin.

Wadannan kuwa sun kunshi irin gwarzon matasan PDP na Arewa maso Gabas, Alhaji Aliyu Manji da sauran wadanda suka yi fama, don ganin PDP ta ci gaba tun a lokacin zuwanta.

Goni ya bayyana cewa, an yi ba daidai ba ga wasu sannanun ’yan jam’iyyar PDP da ke amfani da kudadensu da lokacinsu wajen bunkasa jam’iyyar PDP a yankin Arewa, musamman daga yankin Gabas wanda ya kunshi jihohin Gombe, Taraba, Yobe, Borno, Adamawa da Bauchi, amma har yanzu babu wani mataki na bayar da hakuri da aka yi ko biyansu haddin wahalhalunsu ga PDP.

Alhaji Mallah ya ce, idan an yi la’akari da wadanda suka yi takara a mukamai daban-daban, musamman irin mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa na yankin arewa; ba wanda aka yiwa rashin adalci tamkar Alhaji Aliyu Manji daga jihar Taraba, wanda bayan karbar kudinsa da PDP ta yi, aka hana ma sa tsayawa takara ba tare da an biya shi diyyar wahalarsa ko ba shi magana a ka yi ba.

“An cuci Aliyu Manji, bayan sayar masa da fom ya cika ya kamala komi, daga baya saboda manyan PDP ba su son ya shiga takara, su ka hana ma sa tsayawa ba tare da hujja ba, aka hana masa kudinsa babu bayani ko neman ya yi hakuri. Da karfi da yaji aka yi ma sa. Akwai irinsu Inna Ciroma da Bappa Mahmud da sauransu wadanda ba a yiwa adalci a lokacin zaben na kasa ba, saboda neman biyan bukatar wasu.

“Wadanan su ne ’yan jam’iyyar PDP na gaskiya da zahiri wadanda suke fadi-tashi kusan kullum da dukiyoyinsu da karfinsu ga ci gaban PDP a Arewa maso Gabas, su ne su ke tsaye ga tabbatar da hakkin jama’a, amma PDP ta yi watsi da su, ba komai da ake yi da su, saboda rashin adalci daga wasu daga cikin shugabanin PDP na Abuja,” in ji Malah Goni.

Dangane da haka ya nemi shugaban jam’iyyar PDP na kasa Mr Uche Secondus da ya samar da kwamitin dattawa da zai tuntubi wadanan mutanen da suke da muhimmanci ga PDP a Arewa maso Gabas.

Alhaji Mallah Goni ya bayyana akwai takaici dangane da yadda wasu ’yan koren siyasa ke kokarin wargaza hadin kai da darajar PDP a Arewacin kasar.

 

Exit mobile version