Bello Hamza" />

2019: Mun Shirya Tsaf Don Koma Wa Fadar Shugaban Kasa –PDP

Shugaban jam’iyyar PDP ta kasa Prince Uche Secondus ya ce, jam’iyyar ta gama shirye-shiryen lashe zabe tare da komawa Fadar Aso Rock.  Mista  Secondus ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya zasu rungumi jam’iyyar hannu biyu-biyu bayan  gyare-gyare da canza wa jam’iyyar alkibla da ake yi, zasu kuma gagguta jefa musu kuri’a a zabukan dake tafe.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yayin da yake karban bakoncin shugabannin majalisun dokokin jihohin da PDP ke mulki a ofishinsa dake Abuja.

Mista Secondus ya musu bayanin aikace-aikacen da shugabannin jam’iyyar da aka zaba a watan Disamba, ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya zasu yi murna da tsare-tsaren da ake gudanarwa na canza wa jam’iyyar alkibla domin samun nasara.

Mista Ike Abonyi, jami’in watsa labaran Mista Secondus ya sanar da haka a wata takardar manema labarai da ya sa wa hannu, Shugaban jam’iyyar ya ce, “Shirye shiryen da muke yi na canza wa jam’iyyar alkibla zai mayar damu jam’iyyar adawa mai karfi da zata kwace mulki a shekarar 2019”

“Mun zagaye fadin tarayyar kasar nan, mun kuma lura da cewa ‘yan Nijeriya da dama na shukin ganin jam’iyyar PDP ta dawo kan karagar mulkin kasar nan, ziyarar namu ya kuma nuna mana cewa gwamnonin jam’iyyar PDP ne kadai ke cika alkawuran da suka yi wa mutanesu kuma jama’a na murna da haka.

“A jihohin Abia da  Delta da na Bayalsa da muka ziyarta kwanannan, gwamnonin PDP sun ciri tuta, hakan ya sa jama’a ke tururuwa zuwa jam’iyyar daga jam’iyyar mai mulki na APC”

Prince Secondus ya kuma ce, shugabannin majalisun dokokin jihohin na da mahinmanci saboda kusancinsu da jama’a a kokarin da ake yi na sake farfado da jam’iyyar.

“Ya kamata ku kasance tare da jama’a domin wannan karon muna shirin mayar da jam’iyyar ne ga mutane, kune kuma kuka fi kusa a harkokin yau da kullum na mutane kasar nan”

Shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana wa shugabanin majalisun dokokin jihohin da PDP ke mulki cewa, jam’iyyar PDP na shirin fito da hadakan da zai rungumi matasa domin sune jagororinmu nan gaba.

Tun da farko, shugaban kungiyar shugabannin majalisar dokokin jam’iyyun PDP kuma shugaban majalisar dokokin jihar Delta Sheriff Oborebworio, ya bayyana cewa,sun kawo wa shugaban jam’iyyar ziyarar ne domin taya shi murna da nuna amincewarsu a kan kokarinsa na sake yi wa jam’iyyar garanbawul. Shugabannin majalisun jihohin da suka samu hakarta sun hada da Kola Oluwawole na jihar Ekiti da Nwaruku Francis na jihar Ebonyi da  Ikuniyi- Olajide Ibani na jihar Ribas da Chekwendu Kalu na jihar Abia da Nasiru Abubakar Nono na jihar Gombe da kuma John Gaul Lebo na jihar Cross Riba.

Exit mobile version