Khalid Idris Doya" />

2019: Na Fito Takarar Gwamnan Bauchi Ne Domin Ceto Jihar Daga Halin Da Take Ciki -Sanata Gumba

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A a cikin makon jiya a ranar Alhamsi ne, Sanata Adamu Ibrahim Gumba ya ayyana bukatarsa na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe, Sanatan wanda ya ayyana bukatarsa ta tsayawa tarakar a karkashin jam’iyyar PDP.

Da yake bayani wa uwar jam’iyyar a matakin jihar, kan neman ta ba shi damar tsayawa wannan takarar a karkashin Jam’iyyar, Sanata Adamu Ibrahim Gumba ya bayyana cewar ya fito ne domin ceto jihar Bauchi daga halin da ta tsinci kanta na tabarbarewar tattalin arziki, rashin aikin yi da suka yi katutu wa jihar.

Sanatan ya bayyana cewar idan ya samu damar kasancewa gwamnan jihar Bauchi zai fi maida hankula kan fannoni uku domin a cewarsa an tafi an bar jihar Bauchi a kan wadannan fannonin “Kiwon Lafiya, harkar Gona da ya gama lalacewa a jihar nan, sannan kuma zan maida hankali kan sha’anin ilimi. wadannan ukun su ne manyan ababen da zan fi maida hankulana kansu idan na samu wannan kujerar ta gwamnan jihar Bauchi,” In ji Shi.

Sai ya bukaci jam’iyyar ta mara masa baya domin ya samu kaiwa ga wannan matakin don ciyar da jihar gaba.

Tun da fari ma, ya shaida wa uwar jam’iyyar cewar shi asalinsa ya jima yana bauta wa jihar Bauchi tun daga karam’in ma’aikaci har sama, kana har ya zo ya kasance Sanata, don haka ne ya bayyana cewar yana da masaniyar matsalolin Bauchi da kuma hanyoyin magancewa don haka ne ya fito domin ceto jihar ta bakinsa, “Abun da ya sa na ke son na yi takarar gwamna, ni din nan na fara aiki a jihar Bauchi tun ina malamin makaranta, na hau har na zama Sakataren gudanarwa, har ta kai na zama Babban Sakataren dindindin, na kare aiki a jihar Bauchi a matsayin shugaban ma’aikatan jiha, don haka babu wani aikin gwamnati a jihar Bauchi da ni ban sani ba, na kuma san yadda za a yi domin kyautata jihar”. In Ji Gumba.

Da yake amsar bukatarsa, Shugaban jam’iyyar PDP a matakin jihar Bauchi Hamza Ibrahim Akuyam ya jinjina wa dan tarakar a bisa nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a iyuwar jam’iyyar ta PDP, yana mai cewa jam’iyyar za ta bi dukkanin hanyoyin da suka dace domin amsar mulki a jihar don kyautata wa jama’an jihar rayuwarsu.

Shugaban sai ya bayyana cewar za su duba bukatar da dan takarar hanu biyu-biyu, ya kuma gode masa kwarai a bisa nuna sha’awarsa na tsayawan.

Da yake ganawa da manema labaru bayan kammala gabatar da bukatarsa a sakariyar jam’iyyar, Adamu Ibrahim Gumba ya bayyana cewar kishin jihar da kuma nema wa jama’an jihar mafita ne ya sanya shi fitowa neman kujerar, yake cewa “Noma ita ce tushen arzikinmu gaba daya, an ma an lalata ta, an watsar da ita. Idan ka duba ko lokacin da na yi Sanata abun da na fi bayar da karfi a kai shi ne nomar rani, samar wa talakawa abun yi wanda zai azurta su, su samu kudi, su samu abinci da abun da za su yi sutura da shi.

“Na koya musu nomar ranin nan, kuma idan ka lura a kasar nan muna da albarkatun kasa wadanda idan aka inganta su za a samu ci gaba sosai. Misali muna da Tattatasai, Attarihu su Tumatur. Ni babban bakin cikina ma shi ne gwamnati ba ta kafa musu kamfani da za a ke sayen wadannan amfanin ana sarrafa su ba; manoma suna yawan yin asara,”

Ya ce, zai samar da kamfanoni da na’urorin da za su sarrafa wadannan albarkatun domin inganta tattalin arziki “Don haka idan na samu dama, wannan gwamnatin da zan nemi na zama gwamna, irin gudunmawar da za mu bayar zan yi kokarin samar da na’urar sarrafa tumatur da su tattasai, albasa da su tarihu a jihar Bauchi domin bunkasa tattalin arzikin jihar,” Ya shaida.

Da yake mika bukatarsa a gaban jam’iyyar, ya fara ne da kawo tahirinsa da kuma cikakken manufa da dalilansa na neman tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe, ya samu tarba daga uwar jam’iyyar da kuma wasu jiga-jigai.

 

Exit mobile version