Daga Mubarak Umar, Abuja
A cikin makon da ya gabata wasu rahotanni suke zagayawa cewar wata kungiya da ba a gama tantance sahihancinta ba, ta bukaci Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fito takakar Shugaban Kasa a zaben 2019, a ra’ayinsu, babu mutumin da ya dace da wannan kujera sama da shi. Labarin ya tayar da kura matuka musamman a shafukan sada zumunta, inda ta kai mutane suna musayar ra’ayi game da wannan batu.
Sai dai Mataimakin Shugaban Kasar Farfesa Yemi Osinbajo, ya nesanta kansa da kungiyoyi masu kiraye-kirayen ya fito takarar Shugabancin Kasa.
Wannan jawabin dai ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Osinbajo, Mista Laolu Akande, inda ya wallafa a shafinsa na tiwita ‘Twitter’.
“Shafukan da suke yada wannan labari na batun kiraye-kiraye da wasu kungiyoyi ke yi na Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya takara a 2019, shiririta ne kawai. Saboda haka kada mutane su dauki wannan lamari da muhimmanci, domin ba shi da tushe ballantana makama.” A cewar Akande.