2019: PDP Ta Fara Laluben Wanda Zai Rike Mata Tuta A Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne Kwamitin amintattu na Jam’iyyar PDP, ya shelanta cewa, Jam’iyyar na su ta fara bincikawa da kuma laluben wanda zai rike mata Tuta a wajen takarar Shugabancin Kasarnan a shekarar 2019, a inda ta bayyana cewa, duk ta yadda za a dama a kuma shanye, sai ta fitar da dan takarar da ya fi kowa cancanta, wanda zai iya tunkara ya kuma kifar da duk wanda Jam’iyyar da ke mulki a halin yanzun ta APC, za ta tsayar a wajen zaben.

Wannan sanarwar ta kwamitin amintattun Jam’iyyar, ta zo ne a daidai lokacin da Kakakin Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, ya sanarwa duniya da cewa, a yanzun fa fatalwar karairayi da kuma alkawuran da Jam’iyyar APC, ta yi wa al’ummar kasar nan ne suke hana APC,din runtsawa, domin a cewarsa, babu su, ba kuma alamun samuwarsu. A lokacin da Sanata Walid Jibril, yake magana wajen tarbar mambobin Jam’iyyar da ke mazabun birnin Tarayya Abuja, wadanda suka kawo masa ziyarar sabunta abota wacce suke kaiwa manyan Jam’iyyar na su ta PDP.

Sanata Jibril, ya bayyana cikakken goyon bayan kwamitin amintattun ga maziyartan, ya kuma kirayi daukacin magoya bayan Jam’iyyar a duk fadin kasarnan da su goyi bayan kokarin da Jam’iyyar ke yi na fitar da mutum guda daga cikin jerin mutanan da suka fito da maitarsu a fili na son Jam’iyyar ta mika masu tutar yi mata takarar. A cewarsa, PDP, ba za ta taba tsayar da duk wanda ta tabbatar da ba zai iya tabukawa al’ummar kasarnan komai ba.

“Duk mun aminta da cewa, Shugaban Kasarnan tilas ne ya fito daga shiyyar Arewa. Don haka ina son ku taimaka wa Arewan wajen zakulo Shugaban da ya fi kowa cancanta, ba wanda zai zo ya kara lalata lamurra ba kamar yadda suke a halin yanzun.

Da yake bayyana farin cikinsa bisa dawowar da Mataimakin Shugaban Kasarnan, Atiku Abubakar, ya yi cikin Jam’iyyar a matsayin babban abin farin ciki ne, sai Sanata Walid, ya kirayi wasu daga cikin tsaffin jiga-jigan Jam’iyyar ta PDP, irin su, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso da ire-iren su, da su hanzarta bin sawun Atikun cikin hanzari.

“Ko mun ki, ko mun so, dawowar Atiku cikin Jam’iyyar namu, babban abin farin ciki ne. a lokacin da Atiku, ya fice daga Jam’iyyar APC, ya barta ne salun alun, sabanin wasunmu, a lokacin da suke barin Jam’iyyarmu, su har keta katunan shaidan Jam’iyyarmu suka yi. Kun ga shi bai yi hakan ba, ina kuma yi wa Jam’iyyar APC, murnar hakan.

“Duk karairayin da muke gayawa ‘Yan Nijeriya cewa Jam’iyyar APC, na yi masu, yanzun fatalwarsu ne ke binsu. Mun sha gayawa ‘Yan Nijeriya, cewa wannan gwamnatin fa ta APC, makaryaciya ce, APC, Jam’iyya ce kawai ta farfaganda kadai. A maganan da nake yi da ku yanzun haka, ita kanta Jam’iyyar ta APC, ba ta san inda ta nufa ba, ba kuma ma ta san inda ta sa gaba ba a maganan tallafi, sun ce tallafi zalunci ne, da ‘Yan Nijeriya suka burma a cikin wannan karyar na su, yanzun kuma ga shi gwamnatin na su ta Tarayya ta dawo tana biyan tallafin, har yanzun kuma ba su iya wanke kansu daga cuwa-cuwar da suke tafkawa ba a sashen na Man Fetur da dangoginsa. Komai na su yaudara ce kawai,” in ji Sanata Walid Jibril.

Exit mobile version