2019: PDP Ta Sha Alwashin Karɓe Kujerar Ganduje

Daga Abdullahi Muhammad, Sheka

An bayyana nasarar da Jam’iyyar PDP ke samu wajen karɓar dubban ‘yan jam’iyyu daban-daban a Jihar Kano da cewa al’amari ne da ke tabbatar da kammala shirye-shiryen karɓe kujerar Gwamnan Kano daga Hannun Jam’iyyar APC mai mulki, sakamakon gazawar da ta yi wajen cika alƙawuran da aka yi wa jama’a a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Wannan bayani ya fito daga bakin tsohon wakili a majalisar wakilai ta tarayya daga Ƙaramar hukumar Kumbotso Alhaji Bala Bayco lokacin da yake jawabi ga wasu dandazon matasa da suka yi iƙirarain yar da ƙwallon mangwaro su huta da ƙuda.

Alhaji Bala Bayco ya ci gaba da cewa, alamu sun nuna jama’ar Kano sun gaji da gasa masu aya a hannu da mulkin da APC ke yi, saboda haka suka fara haɗa komatsensu domin shiga cikin jirgin fiton al’umma wanda Alhaji Ibrahim Al-Amin ke tuƙawa, ya ce duk wanda ya san Al-amin ya san siyasa yake don nemawa jama’a mafita ba don neman kuɗi ba, ko  a jawaban da ya gabatar alokacin komarwarsa Jam’iyyar PDP ya bayyana cewa babban dalilin barin Jam’iyyarsa APC shi ne yadda jam’iyya ta kasa taɓuka komai kan batun talauci da matsin rayuwa da  al’umma ke fama dashi. Wannan kalamai na Ibrahim Al-amin ne ya ƙara mana ƙaimin ci gaba da tattaro jama’a masu ra’ayi irin namu na nemawa al’umma hanya mai ɓulle wa.

Ya ce yanzu haka shirye shirye sun yi nisa na ƙara karɓar wasu dandazon jama’a daga ƙananan hukumomi masu yawa, wanda idan aka gudanar da wannan bikin  muna tabbatarwa da jama’a cewa shi kenan an yi jana’izar APC a Kano. Aƙarshe Bala Bayco ya ƙara gode wa matasa waɗanda suka yi fitar ɗango domin shaida bikin komarwar Ibrahim Al-amin Little cikin Jam’iyyar PDP, muna fatan Allah ya ci gaba da haɗa Kanmu baki ɗaya.

 

Exit mobile version