Connect with us

SIYASA

2019: Waye Sabon Gwamnan Jihar Yobe?

Published

on

Zaben shekarar 2007 da ya gabata, Marigayi Sanata Mamman B. Ali, shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyar ANPP a wancan lokacin. Alhaji Ibrahim Gaidam ne mataimakinsa. Marigayi Sanata Mamman B. Ali, ya yi Sanata na tsawon shekaru 8, tun daga 1999 har zuwa 2007. Yana wakiltar Yobe ta Kudu, wato Potiskum, Fika, Nangere da Fune (Zone B). Bayan ya hau karagar mulkin jihar Yobe a matsayin zababben Gwamna, Alhaji Ibrahim Gaidam kuma mataimakinsa. Kwatsam! Ranar 26 ga watan Janairu na shekarar 2009 sai Allah ya yiwa Gwamna Mamman B. Ali rasuwa. Bayan an kammala jana’izar marigayi gwamnan a mahaifarsa dake garin Potiskum, sai aka rantsar da mataimakinsa, Alhaji Ibrahim Gaidam a matsayin sabon gwamnan jihar Yobe, shi kuma sai ya dauko kanin marigayi gwamnan a matsayin mataimakinsa, Injiniya Abubakar D. Ali.
Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam, bayan ya kammala shekaru biyun da aka zabe shi tare da marigayi Gwamnan, Sanata Mamman B. Ali, sai ya sake fitowa takarar neman kujerar gwamnan jihar Yobe a shekarar 2011. Inda ya lashe zaben, wanda hakan ya sake ba shi damar ci gaba da zama a kujerar gwamnan jihar Yobe. A zaben 2015 ya sake fitowa takara a karkashin jam’iyar APC, inda nan ma ya sake lashe zaben, wanda hakan ya sa ya zama shi ne gwamna na farko da ya taba yin shekaru 10 a matsayin gwamna a tarihin Dimokradiyya a Nijeriya.
A wannan zabe na 2019 mai zuwa Alhaji Ibrahim Gaidam zai sauka daga kujerar gwamnan jihar Yobe, sai dai har zuwa yanzu Gwamna Gaidam bai ayyana wanda zai ga je shi ba. Wannan abu ya daurewa al’ummar jihar Yobe kai, ganin ana dab da fara zaben fidda gwani, amma har yanzu gwamna Gaidam bai bayyana sunan wanda zai maye gurbinsa ba.
Jama’a da dama suna ta hasashe, wasu su ce, wane gwamna zai tayar. Wasu kuma su ce, a’a wane ne. Haka dai ake ta cece-kuce akan dan takarar da gwamnan zai tayar. Babu wanda yasan dalilin da ya hana gwamnan bayyana sunan dan takarar da zai ga je shi. Akwai ‘yan takara dayawa da suka nuna sha’awarsu na tsayawa takarar gwamnan jihar Yobe daga jam’iyar APC mai mulkin jihar. Da kuma Jam’iyar PDP. Wasu tuni har sun ayyana kansu, sun buga Fostoci ana likawa a fadin jihar Yobe, ana ta yawo da motoci mai dauke da hotunansu. Wasu kuma sun yi likimo har zuwa yanzu ba su bayyana kansu ba.
Sai dai a makon da ya gabata, shugaban jam’iyar APC a jihar Yobe, Alhaji Adamu Chillariye tare da sakatarensa Alhaji Abubakar Bakabe, sun kira taron manema labarai a Sakateriyar ‘yan jarida dake garin Damaturu, inda suka bayyana cewa “Kwamitin zababbu na jam’iyar APC a jihar Yobe, har yanzu bai bayyana sunan dan takara ba a zaben 2019 mai zuwa. Duk wanda ya ce shugabannin jam’iyar APC na jihar Yobe suna bayan wani dan takara, to karya ya ke. Mu dai muna bayan wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani da za a yi kwanan nan” inji su.
Daga cikin wadanda ake kyautata zaton suna cikin ‘yan takarar neman kujerar gwamnan jihar Yoben, amma ba su bayyana kansu ba, akwai mataimakin gwamnan jihar Yoben na yanzu, Injiniya Abubakar D. Aliyu. Wanda kuma shi kanine uwa daya, uba daya da marigayi tsohon gwamnan Yobe, Sanata Mamman B. Ali. Sannan akwai Sakataren gwamnatin jihar Yobe, Alhaji Baba Malam Wali da kuma kakakin majalisar jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo. Sannan akwai Alhaji Lawan Shettima Ali, wanda shi ne kwamishinan ayyuka da zirga-zirga na jihar Yobe a yanzu haka. Akwai kuma sugaban ma’aikata na jihar Yobe, Alhaji Saleh Abubakar da kwamishinan ilimi na jihar Yobe, Alhaji Mohammed Lamin.
Sannan akwai Injiniya Mustapha Maihajja, wanda shi ne babban Darakta a hukumar NEMA ta kasa da Alhaji Mai Mala Buni, tsohon sakataren jam’iyar APC a jihar Yobe, sannan sakataren jam’iyar APC na kasa a yanzu. Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ita ma tana daya daga cikin wadanda suke da sha’awar tsayawa takarar gwamna a jihar Yobe a zaben 2019 mai zuwa.
Idan muka juyo kan wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara kuwa, har sun buga fastoci ana ta likawa a garuruwa akwai, Alhaji Ibrahim Mohammed Bomoi (Bala Basa) daga Potiskum. Tsohon ma’aikaci ne (Bursar) a Kwalejin horar da Malamai ta gwamnatin tarayya dake garin Potiskum (FCE-T Potiskum), sannan tsohon Darakta a FCDA. Yanzu kuma babban dan kasuwa ne. Shi ana masa ganin sabo ne a harkar Siyasa, kuma wanda ya shigo harkar siyasar da kafar dama. Yana cikin na farko-farko wanda ya fara bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Yobe. Yana da dangantaka ta kut da kut da gwamna Ibrahim Gaidam, har ana cewa ma shi ne ya cusa masa ra’ayin shiga siyasa.
Alhaji Aji Kolomi (Ajiko) daga Gujba. Tsohon ma’aikacin gwamnati ne, wanda ya yi aiki a bangarori daban-daban a tsakanin jihohin Yobe da Borno. Shi ma yanzu haka hotunansa na tsayawa takarar gwamnan jihar Yobe sun karade ko’ina a fadin jihar Yobe. Alhaji Sidi Yakubu Karasuwa, gogagge kuma kwararren dan siyasa ne tun daga shekarar 1999 ake damawa da shi a siyasar jihar Yobe. Shi ne tsohon shugaban Jam’iyar ANPP a jihar Yobe. Ya rike shugaban karamar hukumar Karasuwa, ya yi kwamishinan Ilimi, Gidaje da na Ruwa. Yanzu kuma shi ne dan majalisar tarayya mai wakiltar Karasuwa, Machina, Nguru da Yusufari. Sannan akwai Malam Umar Ali, daga Potiskum. Tsohon ma’aikacin gwamnati ne, amma yanzu hamshakin dan kasuwa ne, shi ma yana cikin ‘yan takarar neman kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyar APC. Akwai kuma Alhaji Yusuf Adamu Jajere, wanda shi ma yanzu fostocinsa sun fara karade garuruwa.
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, daga Gashuwa. Tsohon Malami a Jami’ar Maiduguri, kuma Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa (Zone C), sannan shi ne shugaban majalisar Dattijai (Senate leader) a yanzu haka. Tun a shekarar 1999 ake damawa da shi a majalisar tarayya. Ya yi dan majalisar tarayya mai wakiltar Bade da Jakusko daga shekarar 1999 zuwa 2007. Sannan ya zama dan majalisar dattijai tun daga shekarar 2007 har zuwa yanzu. Sanata Ahmad Lawan yana daga cikin wadanda suka tsaya tsayin daka, sai da Alhaji Ibrahim Gaidam ya lashe zaben shekarar 2015. Wadannan duk a karkashin Jam’iyar APC suke neman tsayawa takara.
A bangaren jam’iyar PDP kuwa, Alhaji Adamu Maina Waziri ne, tsohon ministan ‘yan Sanda. Tun a shekarar 1999 ya ke fitowa takarar neman gwamnan jihar Yobe, amma bai taba nasara ba, kuma bai taba sarewa ba. Sannan bai taba canza sheka zuwa wata jam’iyar ba. Sannan akwai Malam Ibrahim Talba, daga Nangere. Tsohon sakataren dindindin na gwamnatin tarayya, yana daya daga cikin wanda suke neman kujerar gwamnan jihar Yobe karkashin jam’iyar PDP. Cikin watan Satumba mai kamawa ne dai za a yi zaben fidda gwani, domin kowa ya san matsayinsa. Zaben 2019, ko wanene sabon gwamnan jihar Yobe?

Ibrahim El-Tafseer Potiskum
08032076472
(eltafseer15@gmail.com)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: