2019: ‘Yan Nijeriya Na Tare Da Ni –Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, ya yanke shawarar sake tsayawa takara ne a karo na biyu saboda ya tabbatar da ‘yan Nijeriya suna tare da shi. Buhari ya ce, sakamakon kokarin da ya yi ne ya sanya ‘yan Nijeriyan suke a shirye da su kare shi su kuma sake zaben sa a 2019.

Shugaba Buhari ya ce, ainihin ‘yan Nijeriya suna yaba wa kokarin gwamnatin sa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a sa’ilin da yake amsa wata tambaya lokacin da yake ganawa da al’umman Nijeriya mazauna kasar Togo, a ofishin jakadancin kasarnan da ke Lome, Togo.

Babban mai taimaka wa Shugaban kasan kan harkokin manema labarai, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, inda ya jiwo Shugaban na fadin, yawancin ‘yan Nijeriya suna yaba wa gwamnatin na shi.

Da yake bayyana jin dadinsa kan yadda ya ga ‘yan Nijeriyan sun yiwo takakka daga yankuna biyar na kasar ta Togo domin su tarbe shi a Lome, Buhari ya ce, ya ji dadin irin yabon da ya ji suna yi wa gwamnatin na shi.

Ya kuma tabbatar masu da cewa, gwamnatin na shi tana nan kyam kan kokarin cika alkawura ukun da ta yi a zamanin neman kuri’u, na cewa za ta tabbatar da tsaro, ta inganta tattalin arziki sannan ta yaki cin hanci da rashawa.

Shugaban ya ce, idan da a ce gwamnatin da ta shude ta yi aiki da ko da kashi 25 ne na kudin mai da ta samu, da ‘yan Nijeriya ba za su koka da komai ba a yau.

Ya kawo misali da dala bilyan 16 da aka ce an kashe kan samar da hasken lantarki, amma kuma har yanzun ‘yan Nijeriya ba su ga lantarkin ba.

Ya kuma tabbatar masu da aniyar gwamnatin na shi na samar da manyan ayyuka a cikin kasa da bayar da basuka ga manoma, wanda hakan ya yi dalilin rage yawan shinkafar da ake shigowa da ita da kashi 90.

“Ina tabbatar maku, mun sami ci gaba kan harkar tsaro, domin a yanzun haka wasu manoman da aka kore su daga gonakinsu duk sun koma gonakin nasu.

Cikin jawabinsa na maraba, jakadan Nijeriya a kasar Togo, Joseph Iji, cewa ya yi duk ‘yan Nijeriya kusan milyan biyu da suke kasar ta Togo, masu bin doka ne, suna kuma zaune lafiya.

Sai dai, ya janyo hankalin Shugaban kasan kan yadda ofishin kasannan da ke Togo din ba ya iya bayar da Fasfo, wanda hakan ya sanya masu bukata sai dai su tafi kasashen Ghana ko Jamhuriyan Benin.

 

Exit mobile version