Connect with us

SIYASA

2019: ’Yan Takarar Da Za Su Fafata A Zawarcin Kujerar Gwamnan Borno

Published

on

A yayin da kakar babban zaben 2019 ke karatowa, lamurra ke dada zafafa a tsakanin masu sha’awar mukaman siyasa daban-daban, a kasar nan. Ana sa ran mutum 16 ne ke zawarcin kujerar gwamnan jihar Borno, a karkashin lemar jam’iyyar APC, a kakar zabe mai zuwan- a kokarin kasancewa magajin gwamna Shettima, da yake zangon sa na biyu.

Wasu daga cikin adadin, sun sayi fam din nuna sha’awar tsayawa takarar, a shelkwatar uwar jam’iyyar ta kasa. Wanda hakan ya zo ne ta dalilin matakin gum da bakin da Gwamna Kashin Shettima ya dauka ne, wajen nuna wanda zai goya wa baya a zahiri.

A watan da ya gabata, an hakaito kalaman gwamana Shettima wanda a ciki ya bayyana cewa, ba zai tsoma baki ba wajen tsayar da mutumin da zai gaji kujerar sa ba, inda ya ce, wannan zabi ne na Allah.

Sai dai a cikin wasu kalaman shaguben wanka da kamar jirwai, da Kashim Shettima ya yi, inda ya caccaki wasu gungun yan siyasar jihar Borno, da ya kira su da masu tserewa su bar al’ummar jihar zuwa Abuja, tun bayan barkewar tarzomar rikicin Boko Haram, kuma ba tare da kula gida ba; yau kimanin shekaru 9, sannan babu wanda ya tallafa wa jama’ar, ko da shinkafa.

Har wala yau kuma, ya bayyana irin wadancan yan siyasa da cewa bai kamata a amince musu jagorancin al’ummar jihar Borno ba.

A hannu guda kuma, goma (10) daga cikin su sun sayi fam din takarar- bayan kasa samun sulhu da daidaiton ra’ayoyi a tsakanin yan takarar, a matakin jam’yya.

Wata majiya ta shedar da cewa, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a Borno- da suka kunshi Gwamna Shettima da kan sa, kwamishinonin sa tare da manyan jami’an gwamnati, sun gudanar da wani zaman sulhu a Abuja, domin fitar da dan takara, a ranar Lahadin da ta gabata.

Zaman tattaunawar sulhun, ya tattaro mutanen da ake kallon su na gaba-gaba, wajen samun goyon bayan masu ruwa da tsaki a APC jihar Borno, daga ciki akwai kwamishinonin gwamna Shettima, yaran sa, abokanai, sanatoci masu ci yanzu da tsuffi, da makamantan su.

Yan takarar kujerar gwamnan jihar Borno a wannan zaben, sun kunshi:

Sanata Kaka Bashir Garbai, dan majalisar dattijai, mai wakiltar tsakiyar Borno, ya bayyana aniyar sa wajen takarar kujerar gwamnan, bayan biyan kudin fam din takarar.

Sanata Garbai, wanda tsohon kwamishinan kula da kananan hukumomi a jihar Borno, wanda suke a shiyya daya da gwamna Shettima. Majiyoyi sun nakalto cewa akwai yuwuwar musanyar kujerun, da zarar Kashim ya nuna sha’awar zuwa zauren majalisar dattijai.

Sanata Abubakar Kyari, dan majalisar dattijai wanda yake wakiltar arewacin jihar Borno, a zauren majalisar dattijai, shi ma ya tabbatar da aniyar sa wajen kasancewa magajin kujerar- bayan Shettima. Ya bayyana sha’awar sa a sa’ilin da ya karbi fam din, a sakatariyar uwar jam’iyyar.

Sanata Kyari, wanda tsohon kwamishina ne a ma’aikatu daban-daban, kuma tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Borno a mulkin Kashim Shettima- tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, inda daga bisani ya zarce zuwa zauren majalisar dattibai.

Na uku a jerin mutanen da ke gaba-gaba wajen shinshinar wannan kujera; lamba ta daya a jihar Borno, shi ne Hon. Kaka Shehu, Babban Antoni, kuma kwamishinan Shari’a, a wannan gwamnati mai ci yanzu a jihar Borno. Wanda aka hakaito shi yana cewa yana sa ran tsintar dami a kala, wajen samun tikitin takarar dare kujerar gwamnan jihar a babban zabe mai zuwa.

Daga cikin yan takarar akwai Alhaji Mohammed Makinta, wanda ya rike mukamin kwamishina a lokacin marigayi gwamna Mala Kachalla. Shi ma ya bayyana aniyar takarar kujerar, a lokacin da ya sayi fam din.

Wasu majiyoyin sun lissafta cewa shi ma Jekadan Nijeriya zuwa kasar China; Ambassador Baba Ahmed Jidda, kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Borno, a matsayin wanda ya sayi fam din tsaya wa takarar, a karkashin jam’iyyar APC, a wannan zabe mai zuwa.

Bugu da kari kuma, tsohon mataimakin gwamnan jihar Borno, Adamu Dibal, a zamanin tsohon gwamna, Sanata Ali Modu Sheriff, ya shaidar da cewa yana sha’awar shiga sahun masu zawarcin kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

Mista Dibal, dan asalin yankin kudancin jihar Borno, shiyyar da ke fadi-tashi wajen ganin kujerar mulkin jihar ya zagaya yankin.

A hannu guda kuma, shi ma tsohon kwamishina a ma’aikatar ayyuka a jihar Borno, Adamu Lawan Zaufanjimba, ya ayyana sha’awar takarar kujerar, ta hanyar sayen fam din.

A cikin jerin wadanda za su fafata a zawarcin kujerar, akwai Farfesa Babagana Zulum, kwamishina a ma’aikatar kula da sake farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya tagayyara a jihar, shi ma ya hau layin masu bukatar APC ta damka musu tutar takarar.

Haka zalika kuma, shi ma karamin ministan ayyuka a tarayya, Baba Shehuri, ya nuna sha’awar neman wanda zai gaji Kashim Shettima a karagar gwamnan, a karkashin jam’iyyar APC, a zabe mai zuwa.

Sanata Abba Aji, shi ma ya bayyana aniyar sa kan batun takarar matsayin gwamnan jihar Borno a cikin wata tattaunawa da manema labarai suka yi dashi, inda ya bayar da tabbacin cewa yana muradin ya gaji kujerar da Shettima yake danawa a yanzu. Duk da ya ce, har yanzu bai sayi fam din ba, dalili shi ne yana son ya ga yadda ta kaya a dambarwar da ta tayar da kura kan zaben fidda gwani.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: