Connect with us

SIYASA

2019: Za Mu Zabi Wanda Ya Ke Taimakonmu A Lafia Da Obi -Alhaji Ali Garkuwa

Published

on

Alhaji Ali Garkuwa fitacen dan siyasa ne wanda aka dade ana damawa da shi cikin harkar siyasa masamman a mazaber Lafia da Obi.
Wanda a shekarar 2011 ya zama Jagorar yakin neman zaben Hon. Dakta Haruna Joseph Kigbu a mazabar Lafia da Obi ya kuma kaishi ga cin nasarar lashe zabe.
Haka zalika a shekarar 2015 ya jagoranci tafiyar dan uwansa Abubakar Sarki Dahiru a yakin neman zaben Dan Majalisar mai wakiltar Lafia da Obi inda ya taimaka aka yi nasara.
Yanzu shi ne Sarkin yakin neman zaben mai gidansa na farko Hon. Joseph Haruna Kigbu wanda ya sake komawa takarar neman kujerar Majalisar wakilai na tarayya a mazabar Lafia da Obi a babban zabe mai zuwa a 2019.
Alhaji Ali Garkuwa ya bayyana dalilinsa na sake jan ragamar yakin neman zaben Hon. Dakta Haruna Joseph Kigbu wanda akewa lakabi da (Daktan Talakawa), da irin alheri da Daktan Talakawa ya ke yi wa al’umma lokacin da yake kan kujerar dama yanzu haka.
Da farko masu karatu za su so su ji sunanka da mukamin ka wajen yakin neman zaben Hon. Haruna Joseph Kigbu Daktan Talakawa?
Suna na Alhaji Ali Garkuwa daga garin Lafia nine Jagorar yankin neman zaben Hon. Joseph Haruna Kigbu Daktan Talakawa dan takarar kujerar Majalisar wakilai na tarayya a mazabar Lafia da Obi Wanda a baya ya tabayi daga shekarar 2011 zuwa 2015 kuma munaga ayyukan alheri da ya aikatawa al’umma.
Wanne dalili ne ya sanya ka kara kasancewa Jagorar yankin neman zaben Hon. Joseph Haruna Kigbu?
Wannan ba shi ne farau ba saboda a shekarar 2011ni ne Jagoran yankin neman zaben shi kuma munyi nasara a shekarar 2015 ban kasance tare da shiba saboda akwai dan uwana da ake jira mai yamman Lafiya Abubakar Sarki Dahiru wanda shima ya fito neman wannan kujerar a lokacin mun rabu da Daktan Talakawa Lafiya babu fada babu zagi ba Dan komai ba sai dan saboda kalmar da hausawa ke cewa da arziki a gidan wani gara a gidanka.
Bayan dan uwan nawa yayi nasara yana kan kujerar sai muka ga abubuwan gara jiya da yau, shiyasa na sake komawa wajen abokin tafiyata Wanda yanayi kuma al’umma suna gani muma munajin dadi .saboda idan ka zama mainemawa mutum jama’a to idan anyi nasara kuma ana aikin alheri kaine za ka ji dadi saboda jama’a za su yaba maka.
Hon. Haruna Kigbu ya taba yin Dan Majalisar mazabar Lafia da Obi a shekarar 2011 zuwa 2015 ko zaka iya bayyana abubuwan da al’umma suka amfana dashi?
Abin da ya bani sha’awa na sake dawowa wajen Dakta Haruna Joseph Kigbu mutumne da baya nuna bambamci ko daya baya nuna bambamcin kabila ko na addini.baya kuma kyamar al’umma. Kuma yanajin shawara.
A shekarar farko na zamanshi a Majalisa aikin da ya farayi shi ne gina Buhul rijiyar burtsase a Masallacin Idi na garin Lafia kuma yayi fenti muka sake kaishi Tudun Kwari yayi masu Rijiyar Burtsatse muka sake zuwa unguwar Maina ya gina Rijiyar Burtsatse a Masallaci mu ka zo Kilema gidan Nakasassu ya gina masu dakuna biyar da zaure kaga ai gidan Makafai ai Musulmai ne a gurin. Sannan ya samar da Babban injin wutan lantarki a Unguwar Liman duk wannan aiki cikin shekara daya yayita kuma ni na jagoranci yin wadannan ayyukan.
Sanan akwai abubuwan da mukanmu munji labari ne yayisu suna dayawa a gurare daban-daban masamman karkara. Kuma wadanan abubuwan anyiwa al’umma ne kaga kenan wannan mutum ba mutum ne da za a yar dashiba saboda ayyukan da yakeyi al’umma ne ke amfana .
To yaya batun kiwon Lafiya tunda ana yi masa lakabi da Daktan Talakawa?
Bangaren aikin kiwon Lafiya Daktan Talakawa ya taka mahimmiyar rawa saboda bangarensa ne an yi wa al’umma aiki kyauta a lokuta daban-daban masu fama da cutar ido anyi masu aiki ido ya warke suna gani.masu cutar kunni anyi masu aiki sunaji cututuka da dama anyi tiyata wasu an basu magunguna mai tsada.
Ko a kwannannan Daktan Talakawa yayi irin wannan aikin da ya saba na kiwon Lafiya dama tuntuni yanayi da ya je Majalisa ma yanayi da baya Majalisa ma yanayi. Kamar yadda na fada kwnanan anyi a cikin garin Lafia a Asibitin kofar Fada anyiwa mutum sama da dubu hudu, duk da cewa a farko an bayyana cewa za a yi wa mutum dubu hudune to sai muka ga jama’a sunyi yawa ana ta karuwa sai mukabashi shawara a kara yawan kati sai aka kara.al’umman da suka amfana suna dayawa . akwai wani bawan Allah da yaje Asibitin Gwamnati an yanka masa kudi har Naira 200,000 za ayi masa Tiyata kuma bashi da kudin amma anan anyi masa tiyata an bashi magani duk a kyauta. Duk wani unguwa da kasani a Lafia babu inda wani nasu bai amfana da wannan tallafin na kiwon Lafiya ba. Ka ga wannan ai babban aikine na taimakon Talakawa a kwana uku ayiwa mutum 5,350 magani kyauta masu cuta daban-daban kuma akasari talakawa .saboda haka mu a zaben 2019 al’umma su zabe wanda ya saba taimakonsu ba wanda zai ce zai taimakesu ba.
Kawai Asibitin da Dakta Haruna Joseph Kigbu yake ginawa wanda aka sa wa suna Asibitin talakawa kana ganin cewa talakawa za su amfana da wannan Asibitin?
Wannan Asibitin ba Talakawa dake yankin Kudancin Jihar Nasarawa ba kawai har da duk fadin Jihar dama wasu jihohin al’umma za su amfana.. Kuma ba sai lallai Talakawa ba har ma da masu kudi. Saboda harkan Lafiya ba talaka kadai cuta ke kamawa ba har ma da masu mulki da masu kudi.
Kuma Dakta Kigbu ya tabbatar mana cewa wannan Asibitin kwararun likitoci za a sanyasu har ma da wasu daga kasar wajen za su dawo nan suna aiki. Ina tabbatar maka karshen wannan shekarar za a bude wannan Asibitin saboda an kammala komai pinti ya rage kuma na’urorin da sauran kayayyaki duk suna kasa. Kuma za a budene da fara aikin kyauta . kuma idan an fara biyan kudi ina tabbatar maka daga kota ina zakatarar ana zuwa wannan Asibitin saboda saukinshi.idan a Asibitin Gwamnati ko wani Asibitin za a chaje mutum kudi Naira 50,000 ne to a nan bazai wuce Naira 15,000 ko Naira 20,000 ba insha Allah.
Saboda haka ina kira ga al’umman mazabar Lafia da Obi su sanya a fefe su duba tsakanin wanada yake kai da wadanda suke nema da Dakta Kigbu suga waye ya cancanta su zabe saboda yanzu siyasa ta canza babu batun wayen nawa ko addini na ko kabilana a’a waye mai taimakona shi ne wanda zai taimakeku shi zaku zabe.
To yaya batun tallafi da Dakta Kigbu ke yi?
Ai batun tallafi ba a magana saboda al’umma da kansu suke magana taimakawa da yakeyi hata ni kaina Dakta Kigbu ya bani motar daba kowani dan siyasa yake hawaba bare yayi kyauta.
Kuma lokacin da yake dan Majalisa ya raba mota suna haura 85 mashin sama da 150 ga keken guragu da injunan nika da sauransu . Batun Rijiyar Burtsatse ko injunan wutan lantarki da aka sanya a gurare ba a lisafi.
Advertisement

labarai