Connect with us

LABARAI

Alkalin Alkalan Jihar Sakkwato Ya Yi Ritaya

Published

on

Babban alkalin jihar Sakkwato, Mai Shari’a Bello Abass yayi ritaya daga aiki bayan cimma wa’adin ajiye aiki kamar yadda dokokin aikin gwamnati ta tanadar.
Rahotanni sun bayyana cewa Mai shari’a Abbas,  wanda aka rantsar a matsayin alkain alkalan jihar shekaru biyu da suka gabata yayi murabus ne bayan da ya ciki skekaru 65 da haihuwa.
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da amincewa da mai Shari’a Abass a matsayin  Alkali mai gaskiya da adalci, Tambuwal ya bayyana haka ne a yayin bikin da aka shirya don karrama alkalin.
Gwamna Tambuwal ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Bashir Garba ne a yayin wannan biki, wanda ya bayyana Alkali Abass a matsayin mutum mai tsantseni, sanin ya kamata, sannan kuma kwararre ne a sha’anin sharia.
Shima kwamishinan shari’a na jihar Sakkwato, kuma babban lauyan gwamnati, Barista Sulaiman Usman ya jinjina ma Alkali Abass tare da yabawa da rawar daya taka a sha’anin sharia a zamanin da yake aiki ta hanyar gaggauta yanke hukuncin adalci.
Da yake nasa jawabi, Alkali Abass ya bayyana godiyarsa ga dukkanin mutanen da yayi aiki dasu wadanda suka basi gudunmuwa a aikinsa, musamman gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya bayyana shi a matsayin ginshikin samun nasararorin da yayi.
An nada Abass mukamin Alkalin Alkalan jihar Sakkwato ne a shekarar 2016 bayan tsohuwar Alkalin Alkalai Aisha Dahiru ta yi ritaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!