Connect with us

MAKALAR YAU

Musulunci Da Daidaito A Shekarun Aure (III)

Published

on

Ci gaba daga makon da ya gabata…

Daidaito A Shekarun Aure
Ya kamata a gane cewa abin da yake kuskure ne to sunansa kuskure ko a cikin Ka’aba a kai ko kuma a cocin katolika. Da kuskuren na Nijeriya da na Russia duk kuskure ne. Banbancin kawai shi ne mu mun fi damuwa da matsalarmu ba wai sai mun tafi nemo laifin wasu ba. Don an samu a cikin turawa suna aikata wani abu da illa ne a zamantakewarmu to bai kamata mu halattawa kanmu ba tun da mun riga mun san illar hakan. Don ana kuskure a wata kasa shi kenan sai ya zama daidai a kasarmu? Don ana kuskure a wani addinin sai mu aikata kenan? Lord Resistance Army (Kiristoci) a Uganda sun yi abin da Boko Haram (musulmi) suke a Nijeriya, shi kenan sai a ce a bar maganar BH a tafi ta LRA tun da wani addinin ma akwai yan ta’adda?
Aure fa ba na mutum daya ba ne. Aure tsakanin “miji” da “mata” ake yi. Duk kuma abin da za’a yi tsakanin mutum biyu to a na bukatar duba hakkokin su duka biyun ne ba na mutum daya ba. Ko kasuwanci idan har zai kai ga garari ko a cuci daya to musulunci ya hana balle kuma aure da so ake a mutu ana tare. An tabbatar da mace mai kananun shekaru na iya fuskantar matsaloli wajen haihuwa da zai kai ga rasa ranta idan ba a yi sa’a ba. Ya kamata a dinga lura da wasu abubuwan kafin aure don kada a fada wani gararin. Yanzu ai babu inda a Musulunci aka ce sai an yi gwaji sannan za a yi aure. To amma saboda rashin gwajin jinin kan iya janyo matsala har ta kai an kusa samun ittifaki akan cewa sai an yi gwajin kafin a yi aure. To amma me yasa ba za a yi irin wannan nazari akan auren karamar yarinyar da ake so a yiwa aure ba? Don me shi namijin kadai ake kallo ba a la’akari da shekarun yarinyar?
Yanzu game da babban mutum ya auri yar karamar yarinya a duba wani babban ginshiki a aure, jima’i. Bincike ya nuna mace tana kara jin son jima’i daga shekara 18 yana kara sama har sai ta kai 40. Daga nan kuma sai son ya yi kasa. Namiji yana fin wannan shekarun amma shi ma ba ya wuce 60 sai komai ya ja baya. Yanzu mu duba mutumin nan mai shekara 70 (ko 60 ma) da ya auri mai shekara 15 (ko 20 din). Lokacin da ita yarinyar za ta kai shekarun da zata bukaci jima’i a kalla sau biyu a sati, shi ba lallai ya iya tsyawa kulata ko sau daya a wata ba! Daga karshe wa aka cuta kenan? Shin idan yarinyar dole ta sanya ta nemi wasu hanyoyin da za ta biya bukatunta waye ya janyo? Shin wannan auren ba ya cikin garari? Idan kuma an kamata tana neman wani yaron karshe duk akanta bala’i zai sauka alhalin ga babban dalili nan tun farko an ce sai an yi.
Dan shekara 70+ ya auri yar shekara 15. Yar shekara 12 ta nemi mijinta mai shekara 68 ya saketa a kotu. Miji mai shekara 80 ya nemi matarsa mai shekara 17 da ta bashi dubu 150 don ya saketa ta hanyar “khul’i”. Wannan duk ba fim bane ko almarar litattafai ba. Yana faruwa a cikin musulmi har ta kai ana bawa hakan kariya ta fuskar addini. E, wallahi! Haka za ka ji ana cewa a haka shari’armu ta “rahama” da ta bawa mata hakkokinsu ta ga damar yi, kuma haka zamu yi! Wanda ya ga dama ya yi imani, wanda ya ga dama ya kafirce!!
Ina gaya muku wallahi wannan sai dai ya sanya a kafirce din. Ai ta cewa shari’a sabanin hankali ce. Masu hankali ba zasu tsaya kulata ba balle har su shiga cikinta. Wace irin shari’a ce wannan da ba ta duba tushenta (makasidush-shari’a)? Shari’ar “pedophilia”? Shari’ar “misogyny”? Shari’ar da duk wani zalinci an halattashi an ce a littattafan “Fikihu” yazo da madogararsu a litattafan Hadisai marasa inganci? Shari’ar Ghenghiz Khan da Adolf Hitler! Sannan daga baya kuma a dinga tambayar me yasa ake zama mulhidai!
Babbar musibar ita ce har yanzu mutanenmu basu yarda mace na cikin kunci ba. Har yanzu basu yarda akwai abubuwan da take bukata ba. Ta yaya dan shekara 70 zai iya biyan hakkin yar shekara 15? Ta yaya? Don haka babban malamin Mu’utazila Sheikh Abubakar Al’asam (rh) da Imam Ibn Shubrima (rh) suka bayyana rashin halaccin aurar da karamar yarinya baki daya. Sun yi amfani da ayoyin Alkur’ani kuma sun nuna zalintar yarinya ne. Cewar an yi ijima’in halaccin aurar da karamar yarinya kuskure ne da wasu suka yi. Wadannan malamai ne da sun isa hujja a Fikihu kuma maganarsu a bar dubawa ce.
Ko a kunnen wayayye ko bagidaje, mai ilimi ko jahili; wannan auren na yar 15 ga dan 70 abin kyamata ne. To amma an ce shari’armu sabanin hankali ce! Duk wani hauka sai wani ya kawo mana ya ce ce addini ne kuma kada mu duba! Indai Allah yace aure don soyayya da kauna ne ta yaya dan shekara 70 zai iya soyayya da yar shekara 15? Mutum ya zama tsoho tukuf duk dan ragowar kyawun fatarsa ya kare amma yana son auren yar karamar yarinya! Don Allah wace irin cuta ce wannan? Sannan wani yazo yace wannan shari’ar Musulunci ce!
Mata suna son yaro matashi. Furfura babbar illa ce agun matan da suke son maza kamar yadda Alkama bn Abdata ya fada. Mata suna son saurayi sosai da sosai. Amma al’ummarmu ba ta damu da hakkin mace ba. Ba wanda yake son ya saurari kukan mace. Sai ta yi magana a rufeta da mujalladai a ce dama sun fi yawa a wuta! Allah ya jikan Almardawy Alhanbaly da yake fadin cewa kada tsoho ya auri yarinya in dai ba so yake ta tafi zina ba.
Malamai dayawa na da da na yanzu sun bayyana rashin dacewa kai har da rashin halaccin tsoho ya auri yarinya saboda cutarwa ne ga ita yarinyar. Ka karanta “Ahkamul Usra” na Muhammad Mustafa Al’azhary (rh) da Allama Riwyani a littafinsa “Albahr” da ya ce sharadi ne sai shekaru sun daidaita za’a yi aure. Ba wai ina nufin shekaru su zama daya ba. Ina maganar daidaiton shekaru ne. Daidaiton shekaru yana nufin mutum ya auri wacce ya san idan an gansu ko a ido ba za a ce sun zama wani banbarakwai ba. Har Imam Alkadhy Mawardy (rh) da aka sani shi ma ya bayyana cewa kada a yi aure babu daidaiton shekaru. To amma al’ummarmu tafi son kare karyar da take so akan karbar gaskiyar da ba ta so.

Allah ya kyauta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!