Connect with us

LABARAI

Albashi Mafi Karanci: Gwamnonin Nijeriya Sun Ce Ba Za A Iya Biyan Naira 30,000

Published

on

Batun biyan albashi mafi karanci na Naira 30,000, wani abu ne da ba zai yiwu ba, ko da an fara kuma ba zai iya dorewa ba, wannan shi ne abin da kungiyar Gwamnonin Jihohi suka tabbatar.
A maimakon hakan, sai kungiyar gwamnonin arewa suka ce za su iya biyan Naira 22,500 ne kacal a matsayin sabon mafi karancin albashin, amma duk wani Gwamnan da yake jin zai iya biyan sama da hakan, yana iya biyan duk abin da yake iyawan.
Kungiyar gwamnonin na arewa suka ce, rahoton da aka kawo mai taken, “Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago ta nemi da a binciki gwamnonin da suka karkatar da kudadan da gwamnatin tarayya ta fanshe su da su” wani yunkuri ne da shugabannin kungiyar kwadagon na NLC suke yi na karkatar da fahimtar al’umma a kan alkawarin da Shugaba Buhari ya yi na sake kafa wani sabon kwamitin wanda zai duba kiki-kakan da ake yi a kan batun sabon albashin mafi karanci.
Shugaban sashen yada labarai na kungiyar gwamnonin ta arewa, Abdulrazakue Bello-Barkindo, ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya aike wa manema labarai a ranar Litinin da yamma.
Kungiyar ta NLC tare da sauran kungiyoyin ma’aikata suna neman a biya Naira 30,000 ne a matsayin sabon mafi karancin albashi a maimakon Naira 18,000 da ake biya a halin yanzun.
Sai dai Shugaba Buhari, ya ki amsar wannan sabuwar shawarar.
Kungiyar kwadagon ta ce, ba za ta sake halartan wani sabon zaman ba a karkashin wani kwamitin na daban, domin tattaunawa a kan biyan Naira 30,000 din ba, ta ce abin da ya kamata Shugaban kasan ya yi shi ne, ya aike wa da Majalisun tarayya sabuwar dokar ta biyan Naira 30,000, a matsayin mafi karancin albashin.
Kungiyar kwadagon wacce ta kunshi kungiyoyin ma’aikata da yawa, ta ce za ta gudanar da wata zanga-zanga ta kwana guda a kan kin aikewa da dokar da Shugaban kasa ya yi a ranar 8 ga watan Janairu, 2019.
Abdulrazakue Bello-Barkindo, cikin sanarwar ya ce, gabaki-dayan gwamnonin sun tabbatar da za su yi farin cikin biyan sabon mafi karancin albashin na 30,000, “amma abu ne da Jihohi masu yawa ba za su iya ba, saboda matsalar karancin kudi da suke a ciki, ya ce tun can baya gwamnonin sun shaida cewa, ba wata Jihar da za ta iya sadaukar da rabin abin da take samu a wajen biyan albashin ma’aikata.
A cewar sa, a kan bukatar da Shugaban kasan ya yi masu na su kawo masa kundin bayanan duk kudaden shigan da suke samu daga tarayya da kuma a cikin Jihohin na su da ma duk wata hanya ta samun kudin na su, gwamnonin sun yi hakan, kuma Shugaban kasa ya duba da kyau, ya kuma gano matsalar da Gwamnonin suke fuskanta, wanda hakan ne ya sanya Shugaban kasan ya goyi bayan matakin da Gwamnonin suka dauka, wanda hakan ne ya sanya ya ce zai sake kafa wani sabon kwamitin.
“A ganawar baya-bayan nan da Shugaban kasan ya yi da Gwamnonin a ranar 15 ga watan Disamba, 2018, ya shawarci Gwamnonin da su tsammaci wasu lokuta na yanayi mai zafi a kan tattallin arziki daga wannan sabuwar shekarar, wanda hakan ya karawa Gwamnonin tsoron irin yanayin da za a shiga, ta yanda hatta Jihohin da suke jin cewa su ba su da matsala, to akwai yiwuwar su shiga cikin halin matsi a sabuwar shekarar,” in ji shi.
Ya ce, ba wata doka da ta tilasta wa Gwamnonin sai sun nunawa kaungiyar ta NLC kundin bayanan abin da suke samu da yanda suke kashewa, amma domin neman kungiyar kwadagon ta NLC ta fahimci halin da suke ciki, sun aikata hakan.
“Amma hakan bai sanya kungiyar kwadagon ta saduda ba, ta dage a kan cewa tilas a tsaya a matsayar nata, ko kuma sama da kasa za su hadu. A yanzun haka, kudaden da Jihohin ke samu sun ragu sosai, a sa’ilin da bukatar kudaden kuma ke ta karuwa a kullum. A shekarar bara kadai, kudaden da Jihohin ke samu sun yi kasa da Naira bilyan 800, a lokacin da aka kafa kwamitin mai kusurwa uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!