Connect with us

MAKALAR YAU

Ina Amfanin Tura Manyan Jami’an Tsaro Manyan Biranan Da Ake Rikici?

Published

on

Sakamakon rikice-rikicen da aka rika samu a karkashin wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari wanda ya yi sanadiyar lakumai rayuka ba adadi kuma har yanzu wannan bala’I bai kareba, wannan tasa shi shugaban kasa daukar matakin da yake ganin shi ne mafita.
Daga cikin matakan gaggawa da ya fara dauka shi ne lokacin da aka rika samun bullar rikice can da nan, shugaba Buhari ya yi kokarin ganin ya tattauna da manyan jami’an tsaro Najeriya domin lalubu hanyar da za a warware wannan rikice da kuma daukar matakin dakile shi na har abada.
To amma wani hanzari ba gudu ba, har zuwa wannan lokacin wannan rikice bai kawo karshe ba, ko me yasa? Allah Masani! Masana sun yi maganganu daban-daban akan wannan matsala amma dai kamar ari kamar fanna.
Wani sabon salon da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka a lokacin rikici makiyaya da Manona a jihar Binuwai shi ne ya umarci shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa domin ya je can ya tare sannan ya tabbatar da cewa komi ya lafa an samu zaman lafiya.
Acikin umarnin da shugaban kasa ya bada ba a yi bayanin cewa ga iya lokacin da shugaban ‘yan Sandan Najeriya zai yi a jihar Binuwai ba, an dai nuna cewa ya je can ya tare har sai an samu zaman lafiya.
To amma, wani abu mai kama da almara shi ne, shugaban rundunar ‘yan Sanda Ibrahin K Idris ya je jihar Binuwai amma kwana daya kawai ya yi ya dawo, bayan dawowarsa kuma aka sake samun bullar wani sabon rikici ya barke a wannan jiha ta Binuwai.
Dawowar da shugaban ‘yan sanda ya yi daga aiken da shugaban kasa ya yi masa ya tada mahawara so sai ganin cewa a wannan lokacin idan shugaban kasa ya bada umarni to yana da wahala asamu wani shakiyi ya bijirewa wannan umarni na shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa duniya cewa baya da masaniyar cewa umarnin da ya ba shugaban ‘yan sanda na ya tare jihar Binuwai har sai an samu zaman lafiya, an saba wannan umarni na shi, duk duniya sun ji Buhari yana fadin haka, to amma abinda aka jira a gani shi ne wane mataki zai dauka akan wannan rashin bin umarnin da shugaban ‘yan sanda ya yi?
A takaice dai wannan magana a hankali a hankali ta bi shanun sarki suka shige garka baki daya, a hasashen mutanen Najeriya turo wani shugaba a inda aka samu matsala abu mai kyau kuma zai taimaka wajan warware koma wace irin matsala ce aka samu, sai kuma gashi yanzu shugaban ya je amma ya dawo wannan yana nufin cewa ba da gaske ake yi ba wajan kawo karshen rikice-rikce da suka addabi Najeriya ke nan?
Idan kuwa amsa ta zama a’a, to akwai bukatar bayani dalla-dalla wanda zai gamsar da jama’a cewa ga abinda gwamnati ke nufi da haka, shin shugaban ‘yan sanda ya raina shugaban kasa? ko kuwa shugaban kasa da wasa yake idan ya bada umarni musamman a kan abinda ya shafi kisan jama’a?
Duk da cewa an samu kwanciyar hankali a jihar Binuwai daga baya, wannan salo na turo manyan jami’an tsaro zuwa manyan biranan da rikice-rikice ke faruwa ya cigaba da wanzuwa musamman yankin arewa masu gabas inda har yanzu ana cigaba da sa toka sa katsi akan matsalar rashin tsaro.
A bangare guda kuma wasu na ganin ko dai akwai lauje cikin nadi dangane da matsalar rashin tsaro, ma’ana ayya wadannan manyan jami’an tsaro suna son a kawo karshen wannan balahirar da ake yi wa jama’a kullun yaumun?
Rahotanni masu dadi sun rika fitowa daga bakin manyan jami’an tsaron Najeriya inda suke bayyana nasarar da suke samu akan masu tada kayar baya, a yankin Barno da Yobe da kuma Adamawa sannan da jihar Zamfara wani lokaci ma har da jihar Katsina na cewa sun kusa gamawa da ‘yan kungiyar Boko Harma da kuma barayin shanu da kuma masu satar jama’a domin neman kudin fansa.
To amma, maganar gaskiya shi ne, abubuwa da suke faruwa a kullin na nuna shakku game da wancan magana da jami’an tsaro ke yi, shin ina matsalar take? Sannan ana ji a kafafen yada labarai cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da duk abinda ake bukata domin yin wancan aiki.
Kazalika duk lokacin da aka samu labarin an kaiwa sojojin Najeriya mumunan hari, sai shugaban kasa ya sake bada umarnin manyan jami’an tsaro sun tare a wannan wuri da wannan matsala ta faru sannan su tabbatar sun yi maganin matsalar kafin su dawo, amma wannan magana ko umarnin tuni ta zama kamar busar sarewar a kunnan bebe…
Sannan duk lokacin da za a turo manyan jami’an zuwa wuraran da ake fama da matsala sai an ba su duk abinda suke bukata, kafin su bar Abuja, amma daga karshe ba zaka taba jin wani karin haske ba na irin nasarar da suka samu ba, bayan sun tare inda aka umarce su, sai ma dai ka fara ganinsu a wajan taruruka a cikin birnin tarayya Abuja.
A gefe daya kuma, jaridun Najeriya na cigaba da ruwaito irin nasarar da ‘yan kungiyar Boko Haram ke samu akan jami’an tsaron Najeriya wannan lamari da me ya yi kama?, ina maganar tsari da bin doka a wannan kasa Najeriya? Su wanene ke san a cigaba da zubda jini ba tare da dakatawa ba? Me wannan abu zai zama idan ba a yi maganinsa ba?
Masana al’amuran yau da kullin sun sha hasashen cewa wadannan mutanen da ake kiran manyan jami’an tsaron Najeriya idan har suna saman mukaman su babu ranar da wannan matsala zata kare, saboda haka kashe al’umma sai ma abinda ya yi gaba, su kuma suna cika aljihunsa da kudade.
Abinda har kullin ake bada misali da shi akan wannan matsala shi ne su wadannan manyan jami;an tsaron sun ki yarda cewa akwai wannan babar matsala, abinda suke cewa matsalar wai ba ta kai yadda wasu kafafen yada labarai suke bayyana ta ba.
Wannan yasa wani lokacin ake cin karo da wasu labarai wanda yanzu haka ana maganar cewa wasu kananan hukumomi a jihar Barno suna karkashin ikon ‘yan kungiyar Boko Haram, amma jami’an tsaro na fadin wannan magana karya ce, kuma har yanzu ba daina jin labarai ana kai hare hare ba akan sojojin Najeriya ba.
Kar a manta yanzu haka manyan jami’an tsaron Najeriya an ba su umarnin su tare can har sai an samu zaman lafiya, kodayake a wannan karon ba shugaban kasa ba ne ya bada umarnin, amma duk da haka irin wannan take cigaba da faruwa, shin in amfanin turo manyan jami’an tsaro irin wadannan wurare ba tare da an ga amfanin hakan ba? Me suke yi idan sun je can? suna shiga ayari ne a shiga da ji ko fagen fama tare da su? ko kuwa suna zama ne a manyan birane tare da masu ba su kariya?
Maganar da ake yi yanzu shi ne, an sake bada irin wannan umarnin a jihar Zamfara bayan an kusa karar da mutanen jihar a kan idon duniya ake kai masu munanan hare-hare ba tare da gwamnatin tarayya ta ce uffan ba, sai bayan mutane sun fara daukar matakin yin zanga-zanga wato rayar da gwamnatin Najeriya kawai take ji, sai ga shi shugaban kasa ya bada umarnin cewa shugaban hafsan hafsoshi sojin sama ya tare can sai an samu zaman lafiya.
Duk da kasancewarsa a can jihar Zamfara, har yau ba a fasa kai munanan hare-hare ba akan jama’a ba, kuma ko kafin wannan umarnin sojojin saman Najeriya sun fi sama da wata bakwai suna aikin samar da tsaro a wannan jiha ta Zamfara, amma akan idonsu ‘yanta’ada ke cin karansu babu babbaka.
Wannan yana nufin haka jama’a za su zura idonu suna kallon ana yi masu kishin kiyasa,? a gefe guda kuma gwamnati na cewa jami’anta suna can ba dare ba rana suna aiki, wane irin aiki suke? ya kamata a duba batun turo wadannan manyan jami’an tsaro zuwa manyan birane a sake karatun ta nutsu wajan lalubu hanyar da za a yi maganin wannan matsala.
Jama’a na sane da cewa yanzu shuwagabanin ta yakin neman zaba kawai suke, amma kar su manta wannan ne Allah zai tambaye su, ya kamata a sake sabuwar dibara wajan ganin wannan matsala an daina siyasantar da ita, harkar tsaro dole ce ba alfarma ce, idan kuma ba za a iya ba, to akwai mafi sauki, shi ne a sauka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!