Connect with us

TATTAUNAWA

Me Ya Sa Obasanjo Ke Kiyayya Ga Arewa, Kuma Yaushe Zai Fara Son Arewa? –Dr. Bature Abdul’azeez, MON

Published

on

Wannan wata tattaunawa ce da MUHAMMAD ABUBAKAR ya yi da shugaban hadaddiyar Kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, DAKTA ABDUL’AZIZ BATURE, inda ya bayyana irin kiyayyar da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ke da ita ga arewacin Nijeriya. A sha karatu lafiya.

Shin me za ka ce game da irin maganganun da Obasanjo ke yi a ‘yan kwanankin nan?
Ina son na farad a wata tambaya ta cewa, yaushe ne Obasanjo zai fara kaunar ‘yan arewa? Kuma yaushe zai daina nuna kiyayya a gare su, da ya ce Ibo gabadaya kada su zabi Buhari, gabadaya su zabi wata jam’iyyar daban. Toh Obasanjo, yana so ne ya mallaki mutanen Ibo, ga shi kuma ya kasa mallakar mutanensu na yarbawa, ko da ya mallake su, ba ya iya sarrafa su, baya iya hana su. ‘Yan arewa sun yi sama da shekara 40 suna marawa Obasanjo baya, amma Obasanjo koda wane lokaci ba shi da tunani mai kyau a kan ‘yan arewa, koda wane lokaci burinsa ya ga arewa a cikin wahala. Yana so kuma ya ga arewa a cikin wargajewa, saboda shi a tunaninsa, wato ba ya son arewa, ba ya son ‘yan arewa, kuma ko addini ne baya so, ko mene ne oho. Ba a iya gane kiyayyarsa. Kuma ba shakka bana tsammanin Obasanjo Kirista ne na gaskiya, saboda wannan kiyayya tasa bay au ta fara ba.
Kiyayyar Obasanjo ta fara daga kan shugabanninmu ta farko, su Sa Ahmadu Sardauna, da Tafawa Balewa da sauransu. A lokacin da aka kashe su a juyin mulkin da Ibo ne suka fara yi, wanda wannan juyin mulki ne da ya haddasa bacin ran da har yau bamu taba ganin irinsa ba mu al’ummar arewa, domin an kashe mutanen Allah, an kashe mutanen gaskiya, an kashe mutanen da har yau babu mutane irinsu a wannan rayuwa ta mu ta duniya. Kuma ba su ji ba, ba su gani ba. Kuma yanayin siyasarsu ba ta shafi yanayin siyasar kudanci ko yammacin kasa ba. Irin yanayin siyasarsu daban, arewarsu suka sa a gaba, musamman firimiya. Shi kuwa Firayiminista na Nijeriya ne, amma ba wanda zai ce ina firayiminista ya yi wani abin da za a ce, ya je wani waje yana rigima da su. Bai yi ba. Amma bawan Allahn nan da ya zama wadanda suka zalunci mutanen nan, Ibo. Kuma su suka fara juyin mulki, kusan ma a dukkan Afirka ta Yamma. Saboda haka mutanen Arewa suka ga zaluncin nan ba zai yiwu ba, an kashe mu iyayensu ba gaira ba dalili, wanda ya kashe musu iyayen nan sai suka rama, su ka kashe shi, akan sun rama, saboda shi dama yayi wannan juyin mulkin ne don kabilanci, saboda haka da aka rama aka kashe azzalumi, su ‘yan Ibo da yake ba Nijeriyar ba ce a ransu, Nijeriyar suke so su mulka don su kafa wani yankin da shi ne zai zama gabadaya zai kwace duk wata dama ko duk wani arziki da Nijeriya ke da shi. Barar da wannan mutumin da ya kashe su Sardauna ne fa ya janyo yakin Basasa.
Kuma yakin basasan nan, bangaren Nijeriya sai da suka gwada su ba yi suka yi don ba su kaunar mutumin nan da ya kashe su Sardauna ba, a’a su sun yi ne don su rama, ba wai don basu son Ibo a doron kasa ba. Saboda haka a hade a zama Nijeriya daya. Wanda na sha fada a bayanai na cewa, an yi taro a Landan, an yi a Ghana, an yi a Uganda da Nijar da sauransu don a sasanta. Amma mutanen nan Ibo suka ce ba su yarda a sasanta ba, akan an kashe musu wani wanda yake azzalumi, wani wanda ya janyo jinin sama da ‘yan nijeriya miliyan uku ya zuba a kas. A takaice suka ware kasarsu a ka fara yaki wanda gwamnatin Nijeriya ba ta so hakan ba, aka yi yaki a ka gama, dama karshen azzalumi ya ji kunyi. Kuma alhamdu lillahi nasarar Nijeriya ta tabbata, ta zama kasa daya, al’umma daya.

Mene ne ka ke silar kiyayyar Obasanjo ga ‘yan arewa?
’yan arewa su suka dauko ainihin Gowon suka daura, bayan Gowon ya tafi, Murtala ya zo yayi mulki. Murtala da zai tura Gowon ko Kaza ba a kashe ba, aka yi abin salun-alun. Amma da ya zamana cewar, shi wannan sarkin Sukar yana cikin son rushe arewa da ‘yan arewa, Murtala ko shekara bai yi ba, watanni suka yi masa kisan gilla, kai da ganin wannan kisa ka san kisa ne na hadin baki, kuma Wallahi ina zargi wannan makiyin arewan yana ciki, a ka zo aka yi masa daukar kara da kiyashi, don dai ana so a nunawa mutane cewa ba kabilancin arewaci bane ya sa aka yi juyin mulki na Ironsi. An yi shi ne don dai a tabbatar da Nijeriya ta zama kasa daya.
Bayan an kashe Murtala sai aka dauko wannan kara da kiyashin a ka hada shi da Shehu Musa ‘Yar’adua, wanda a wancan lokacin Shehu Musa ya fi shi nesa ba kusa ba, amma aka hada su don hadin kan Nijeriya, saboda kada ‘yan kudu ko ‘yan yamma su rika ganin kamar ‘yan arewa suna duk wannan kokari ne kawai don Arewa.
Amma bawan Allahn nan ya zo yayi shekara biyu a kan mulki. Alkawarin da a ka yi da duniya kafin a daura shi a kan mulki shi ne ‘yan watanni zai yi a shirya zabe. Bayan an yi zaben, wannan bawan Allah wato Obasanjo, a ka zo Shagari ya hau. A takaice a na nan, anan ya sake dawowa kan mulki a farar hula.
Sai da ya hau ya dare, sai ya zo yana cewa, wai don Kaduna da sauransu sun kashe dabbobi jakai, an kashe Ironsi saboda su. Wato yana nufin wanda suka kashe su Sardauna da Tafawa Balewa da su yake. Wai shi ne Obasanjo ya fadi wannan magana. Wadannan kadan kenan daga irin munanan kalamai da manufofin Obasanjo ga arewa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!