Connect with us

TATTAUNAWA

Da Fatan Akwai Sunan Obasanjo Cikin Fasfo Din Wadanda A Ka Haramtawa Gudu Daga Nijeriya –Dr. Bature Abdul’azeez

Published

on

Ci gaba daga jiya…

Su wadanda aka kashe din, irinsu Ironsi, Chukuma Njebu, wai wallahi tallahi sun fi wadannan Shugabannin na mu na Arewa gaba daya. To ai abin da ba su sani bas hi ne, Shugabannin namau na Arewa, ka ga ga shi yau shekara 52 kenan da kisan nan na su, amma wanda aka haife ma da shekara 20 ko wanda shekarunsa ba su kai 20 ba yana jin ciwon kisan, kuma duk dan shekara 50 dinnan duk wani dan Arewa ba wanda ya sassauta jin ciwon don me aka kashe su Firimiya. To amma shi Obasanjo su suka fada don menene za a kashe wadannan don sun kashe su firimiya.
Kuma a baya-bayan nan aka zo saboda kinsu dai da Arewa su dai ‘yan tawagarsu ko da ba Obasanjon, balle ma yadda muke ji a wajen jama’a na kafofin yada labarai, cewar Obasanjo shi ya cinna wutar kirikirkr Arewa Ta Tsakiya ‘Midle bens’ ta zauna da gindinta, amma sonanta Arewa Ta Tsakiya. Tun da yah au mulkinsa dawowar nan tasa da ya so ya yi tazarce aka mako shi, wallahi da an bas hi ya zarce da Allah ne ya san bala’in da zai haddasa a Arewacin Nijeriya, amma Allah yana ganin cewa zai zamo matsala Allah ya mako shi.
A takaice ya cinna wutar Arewa Ta Tsakiyar nan ‘Middle Bens’, a lokacinsa aka fara fadace-fadacen nan da su katafawan nan, da su Filato, da duk ba a fada lafiya lau ake zaune, kowa ya san Addinin kowa, kuma mutum daya z aka samu ‘ya’yan wa Kirista ‘ya’yan kani Musulmai, ko kuma ‘ya’yan mutum rabi Musulmi rabi Kirista, ko kuma uban Musulmi uwar Kirista. Haka nan a ke zaune babu zancen nuna banbanci. Amma Obasanjo shi ya kunna wutar nuna banbanci, yadda muka ji a kafofin yada labarai suna fada.
Biyafaran nan, lokacin da suka yi kokarin sa wani karfi, wallahi jami’an tsaron Nijeriya in suka matsa bincike sai an samu da hannun Obasanjo a ciki. domin abin da ya sa nake tsammanin hannunsa yana cikin, na sha fada a maganganuna, za ka ji idan yana maganar yaran Biyafaran nan irin 2016, za ka ji da farko kamar Gwamnati yake yabo, amma a karshen zancen sai ka ji su yake yabo, kuma su yake zugawa. Idan ya yi magana a jarida kamar 10, wallahi idan aka dauko maganganun idan ka karanta a hankali sai ka ji ba wa ‘yan Bayafaran kwarin gwiwa yake yi kuma yana zuga su. Ni a fahimta ta haka yake, ya kamata jama’ar Arewa su san Obasanjo fa ba ya son Arewa ba ya son ‘yan Arewa.
Kuma shi kansa Addinin da ake a Arewa yana da matsala da shi, kuma mu da Kiristan Arewa, in don shi da ya kunna wutar fitinar rigima a Arewa ba, gaskiya ba mu da wata matsala tsakaninmu. saboda haka yanzu kuma na ji shi a karshen nan yana cewa wai ‘’Al’ummar Ibo kada ku zabi Buhari.’’ To kai da ka ce kada a zabi Buharin tun farko, kuma ka kafa al’ummar Ibon kada su zabi Buharin tun farko, da ba su zabe shi ba Buharin bai zama Shugaban kasa ba? Allah ne yake Shugaba ba matsafi ba. saboda haka na tabbata yanzu al’ummar Ibo sun dawo daga irin wannan rakiyar ta da da ba ta yi musu amfani ba, in sha Allahu Rabbi al’ummar Ibo, ko da za su zabi wata jama’iyyar za ka ga mafi yawansu su za su Buhari da ikon Allah.
Don haka wutar fituntunu da take Arewacin Nijriyar nan da yawa mutane ana zargin su Obasanjo ne ke kunnawa, don suna ganin sai Arewa ta zauna lafiya sannan Buhari yake da ikon da zai ci zabe. Mutanen nan a ce Obasanjo da kai da ‘yan tawagarka ba ku da aiki sai farfaganda ta karya sai yada kabilanci da kiyayya, ya kamata Shugabannin Nijeriya a dauki mataki kan Obasanjo, domin ba tsohon da zai gyara kasa ba ne, ba tsoho ne irinsu Yakubu Gowon ba, ba tsoho ne irinsu Shagarin nan ba, a takaice tsoho ne da yake da aniyar kafin yam utu sai ya kaskantar da Arewa. Kuma in sha Allahu Rabbi shi zai kaskanta kansa, kuma Arewa da Nijeriaya muna yi musu addu’a Allah ya tabbatar da zama lafiya, Allah ya kawo arziki mai amfani a Nijeriya, wanda arzikin nan da muke addu’a Allah ya kawo wallahi babu wanda zai kawo shi sai Buhari. Saboda kai Obasanjo da masu goya maka baya ai ku kuka sace dukiyar Nijeriya, yanzu haka da za a kwato dukiyar da take wajenku, to Nijeriya ina jin America ce kawai za ta fita arziki a duniya. Amma kun yi rub da ciki a dukiyar jama’a, Nijeriya kasa mai albarka da arziki daban-daban, amma duk da haka ku ne ko da wane lokaci zungure-zunguren fitina.
Ina kira ga Shugaban kasa masu zungure-zunguren fitinan nan tun da ba masu gaskiya ba ne a daiki mataki a kansu don ya zama darasi ga duk wani barawo, na tabbata suna wannan soke-soke ne don bata suna, suna batawa Nijeriya suna wai kawai don su samu mulki. Idan kuna ganin kun a jiya ne da ba a yi muku kallon mutanen kawai, to menene na bace-bace? Sai ku fito ku nuna nagartar da kuka yi a baya a zabe ku saboda ita. Amma ba ku dinga bata sunan Nijeriya ba, kuna amfani da kungiyoyi masu zaman kansu na kasat waje irin masu karyace-karyacen nan da kuma na nan gida wadan da ake saye, da wasu daga cikin ‘yan jaridu kuna amfani da su wajen bata sunan Nijeriya, ai ba sai kun yi wannan za ku ci zabe ba. tun da Allahne mai ba da mulki sai ku bari ya baku, in Allah ya ba ku shi kenan, mu dai abin da muke so shi ne, idan mutumin da ya fi Buhari nagarta a Nijeriya ku fito da shi sai mu zabe shi, amma a yanzu tun da Allah bai nuna mana wanda ya kai nagartar Buhari ba, to Buhari shi ne mafita, shi ne tudun mun tsira a Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya.
Kuma wallahi tallahi wannan magana da muke yi lokaci da hakuri Buhari yake bukata, yadda ya ciccibo ayyuka irin wadanda a da Obasanjo ya dakile ya ki ya yi su a Arewa, yanzu an debo su don a gina Arewa a gina Nijeriya da mutanen Nijeriya, domin akwai ayyuaka da Obasanjo yake tottoshewa ko kuma mutane irinsu suke tottoshewa, ba san arzikin ba wai na Arewa ne kawai ba arziki ne na duk Nijeriya.
Saboda haka ‘yan Nijeriya bala’in da Obasanjo yake son ya ga ya samu ‘yan Arewa da Shugabannin Arewa, dole ne mu mayar da raddi mu juyawa nan wurin baya, kada mu bi shi, domin idan mun bishi kamar muna kiwata abokin gabar mu ne. kuma ba wai Arewa kawai muke kishi ba, muna kishin Nijeriya ne baki daya ta zama daya, a tafi kafada da kafada ban da nuna banbanci kowa ya ci amfanin kowa, dukiyar kasa ta kasa ce, a zaunalafiya, Allah ya taimaki Nijeiya ya taimaki Shugabanninta nagari, domin kowa yana ganin yadda aka fara ayyuka suka fara bayyana, ya far aba da mamaki, ya fara nuna ina aka dosa, kuma muna kan gwadaben da in sha Allahu za mu kai tudun mun tsira, kuma za mu tsira, Buhari yana bukara shekara kwal a fara ganin sabbin ayyuka. Barkammu da sabuwar shekara, amma duk wanda zai karanta wannan jarida Musulmi ko Kirirsta in dai na Arewa ne, to mu nutsu wasu ne suke son su zo su wargaza tsakaninmu mu ci gaba da kashe junanmu, saboda haka ina addu’ar Allah ya taimaki Nijeriya ta taimaki Shugaban Nijeriya ya kara masa lafiya. Salamu alaikum
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!