Connect with us

RA'AYINMU

Yanzu Ba Jaje Kawai Ake Nema Ba, Hukunci Ake Bukata!

Published

on

Kashe-kashen da ke faruwa a sassa daban-daban na Najeriya ya haifar da tsananin fargaba, fushi da karyewar zuciya a cikin kasar da ma kasashen duniya. A gwamnatance an bayyana cewa akalla mutane 86 ne su ka rasa rayukansu kwanan nan a jihar Filato, amma yawancin rahotannin da a ka damu sun nuna cewa an kashe akalla mutum 200 ko fiye da haka, wadanda su ka hada da yara kanana, mata da tsofaffi wadanda ba su ji ba ba su gani ba; karewa ma ba su da cikakkiyar masaniya kan yawancin hakikanin dalilan da su ka haifar da irin wadannan bambance-bambance da ke haifar da kashe-kashen, amma abin takaici su ne abin ya fi shafa.
Wannan fa kisa ne kawai na kwanan nan; ba a batun irin wadanda su ke cigaba da faruwa a jihohin Taraba, Binuwe, Zamfara, Kaduna da kuma ’yan sandan da a ka kashe a babban birnin tarayya Abuja da wasu sassa na Kudancin Najeriya, baya ga yadda kashe-kashe ke karuwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma. A cikin gida da waje an kiyasta cewa akalla mutane 2,000 sun rasa rayukansu daga watan Janairu zuwa yanzu sakamakon fadan da ke faruwa tsakanin wadannan masu sana’o’i kishiyoyin juna da rikicin Boko Haram da kuma rikicin kabilanci. Za a iya cewa ma yawan asarar rayukan ya fi hakan sosai.
Wannan ba karamin abin tashin hankali ba ne ga kasar da ba yaki a ke yi ba a ce an kashe sama da mutum 2,000. Ko harin 9/11 iyakaci kenan. Don haka ba abin mamaki ba ne kisan ke janyo hankalin kowa da kowa a ciki da wajen kasar.
Bayan da a ka aikata kashe-kashen Filato shi kansa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutierrez, ya nuna matukar bacin ransa kan yadda lamarin ke cigaba da karuwa a kai-a kai, inda ya danganta lamarin da rashin cikakken tsari da hangen nesa, musamman a yankin Afrika ta Yamma da Afrika ta Tsakiya wadanda manoma da makiyaya ke da dimbin yawa. Don haka ya tsawatar da cewa dole ne masu rike da madafun iko su dauki matakin kawo karshen lamarin cikin hikima.
Hatta majalisar dokoki ta kasar Birtaniya ta yi kira da a gaggauta kawo hare-hare fiye da 106 da a ka kai tsakanin manoma da makiyaya a bana da kuma munanan hare-haren mayar da martani guda shida a cikin watanni ukun farko kawai na bana a fadin Najeriya. Don haka su ka nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya ta kasa hukunta wadanda ke haifar da aika-aikar da kuma gazawa wajen samar da cikakkiyar hanyar tsayar da asarar rayukan mai dorewa; ba wai bayar da sanarwar jaje ko ziyarar ta’aziyya kawai ba
Lamarin ya yi kama da amfani da wannan dama wajen samun rinjaye a zaben 2019, kamar yadda lokacin da zaben 2015 ya karato sai kashe-kashen balahirar Boko Haram ya kara ta’azzara. Hakan ya jefa zargi a zukata cewa, karuwar rikicin a wancan lokaci ba zai rasa nasaba da gabatowar zaben na 2015 ba. Idan masu wannan hasashe sun yi daidai, to ka ga kenan za a cigaba da aikata irin wadannan kashe-kashe duk lokacin da manyan zabukan kasa su ka gabato tunda an latsa an ga jini.
Babban maganin wannan matsala shi ne hukunta duk wani mai hannu a irin wannan tayar da tarzoma ko makarkashiya. Mu na ra’ayin cewa, tilas ne gwamnati ta tashi tsaye ta tabbatar da cewa an bankado tare da kamo masu hannu a ciki, sannan kuma ta tabbatar da cewa an hukunta su, hukunci mai tsanani ta yadda ba su kawai ba, hatta wani da ya ke sha’awa ko tunanin bin sahu irin nasu ba zai sake marmarin yin hakan ba.
Tilas ne gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, kamar sarakuna da malaman addini, su a koyaushe su rika tuna cewa, manyan fa’idojin samuwar gwamnati a kowacce irin al’umma su ne tsare rayuka da walwalar al’ummar. Idan har rayuwar dan kasa ta na cigaba da kasancewa a cikin hatsari ko kuma ba ya iya tafiyar da rayuwarsa yadda ya dace cikin walwala da jin dadi daidai gwargwado, to tabbas shugabanci bai sauke muhimmin nauyin da ke kansa ba kenan.
Ya kamata gwamnatocin kasar nan tun daga matakin kananan hukumomi zuwa jihohi da tarayya su bai wa bangaren leken asiri muhimmanci ta yadda za a murkushe matsalar tun daga tushenta. Ba za a ce ba sa yin iyaka kokarinsu ba, amma dai a na bukatar sake mikewa tsaye fiye da yin allawadarai da baki. Wannan ba zai iya sawa a kawo karshen matsalar ba tunda an dade a na yin hakan, amma ba ta kau ba. Lokaci ne na hukunci kurum!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!