Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yar Shekara 15 Da A Ka Yi Wa Fyade A Katsina Ta Samu Juna Biyu

Published

on

Wata yarinya ‘yar shekara 15 wacce ake zargin makwabcinsu ya yi mata fyade a jihar Katsina, ta samu juna biyu sakamakon wannan fyade, inda ta sha wahala daga hannun wanda ya yi mata fyade. Wanda ake zargin mai suna Umar Salisu dan shakara 22, dan asalin kauyen Shakafito cikin karamar hukumar Safana da ke jihar, ya shiga da wannan yarinya dakinsa ne inda ya yi lalata da ita. An bayyana cewa, wanda ake zargin da kuma wanda lamarin ya rutsa da ita suna zaune ne a gida daya. A farkon rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa, wani mazaunin yankin ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga sufeto Yusuf Abdullahi da ke shalkwatar rundunar ‘yan sanda a garin Safana, inda jami’an tsaro suka gudar da sintiri a yankin sannan suka cafke Salisu.
Wanda ake zargin an gurfanar da shi a babban kotun jihar Katsina inda ake tuhumar sa da laifin fyade, wanda ya sabawa sashi na 283 na fanal kot. An dai karanta rahoton ‘yan sanda kamar haka, “Sufeto Yusuf Abdullahi wanda yake shalkwatar ‘yan sanda da ke Safana, jami’ansa sun gudanar da sintiri a kauyukan Safana da Gobirawa da kuma Shakafito, inda suka samu bayani daga wajen mazauna yankin cewa, wani saurayi mai suna Umar Salisu dan shekara 22, dan asalin kauyen Shakafito cikin karamar hukumar Safaba ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 15 fyade wacce suke gida daya. Sakamakon haka, a halin yanzu yarinyar tana da juma biyu wanda ya kai wata takwas.”
Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, sufeto Sani Ado ya bayyana wa kotu cewa, a yanzu haka suna gudanar da bincike, ya bukaci a dage sauraren wannan kara domin ‘yan sanda su samu damar kammala bincike.
Alkali mai shari’a Hajiya Fadila Dikko ta dage sauraran wannan kara har sai zuwa ranar 22 ga watan Junairu ta shekarar 2019, sannan ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare Salisu a gidan yari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!