Connect with us

FILIN FATAWA

Jan Carbi Ba Bidi’a Ba Ne A Musulunci

Published

on

Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Mal. Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci. Ina matsayin haka a shari’a?

To dan’uwa jan carbi ba bidi’a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi (SAW) hakan ba zai sa ya zama bidi’a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.
Yin amfani da ‘yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za’a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.
Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.
Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi (SAW) yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu- dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, sai dai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi.
Sai dai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi’a, ga shi kuma ba’a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.
Don neman Karin bayani duba: Majmu’ul fataawa 22\187. Da Lika’ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.
Allah ne mafi sani

Ina Cikin Sallah, Sai Na Tuna Akwai Najasa A Hulata?
Aslm Mallam, mutun ne yana tsakiyar sallah ya kai raka’a ta biyu sai ya tuna kamar akwai najasa a hularsa, amma bai tabbatar ba sai ya cire hular, ya cigaba da Allah, toh ya sallar sa take?
Wa’alaikumus salaam, wanda ya tuna da najasa a hularsa, zai iya hanzari ya cire ta ya yar, in har ya yi haka sallarsa ta yi, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi (SAW) wani lokaci yana sallah, sai ya cire takalminsa, daga baya sai yake bawa sahabbansa labari cewa: Jibrilu ne ya ce maşa akwai najasa a jiki, hadisin sai ya nuna ingancin sallar wanda ya yı haka, tun da ba’a rawaito Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, ya sako sallarsa daga farko ba.
Allah ne mafi sani.

Zan Iya Yin Sallah A Zaune, Saboda Katon Ciki?
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu Malam. Ina da tambaya ina da tsohon ciki, idan ina sallah sunkuyo da tashi yana bani wahala zan iya yi a zaune?

Wa’alaikum as salam, Za ki iya yi a zaune, in har ba zaki iya yi a tsaye ba, saboda hadisin Imran dan Husain lokacin da ya fadawa Annabi (SAW) Basir din da yake damunsa, sai ya ce maşa: “Ka yi sallah a tsaye, in ka kasa ka yi a zaune, in ka kasa yi a zaune ka yi a gefenka”, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1066.‎
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: wanda yake da lalurar da za ta hana shi yin sallah a tsaye, zai iya yi a zaune, saboda addinin musulunci mai sauki ne, ba ya dorawa rai abin da zai iya ba.
Allah ne mafi sani.

Mai Takaba Za Ta Iya Fita Aikin Gwamnati?
Assalamu alaikum. Malam ina da tambaya, mace ce mijnta ya rasu kuma ta kasance tana aikin gwamnati shin za ta iya fita a lokacin da take takaba?
Wa’alaiku mussalam warahmatullah, a zahirin maganar malamai, mai takaba ba za ta je aikin gwamnati ba, tun da bai halatta mai takaba ta fita ba sai lokacin tsananin lalura, aikin gwamnati ba ko yaushe zai zama lalura ba, tun za’a iya ba ta hutu, in har ta nema, in tana da yadda zata cı abinci ya wajaba ta amshi hutu, ko da babu albashi. Saboda bin sharia shi ne zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah, to shi ma zai kiyaye shi, duk wanda ya yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.
Amma idan ta rasa yadda zatayi ta cı abinci sai ta hanyar aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi (SAW) ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a gidan daya dağa cikinsu domin hira da debe kewa da rana, lokacin da suka takuru da zaman kadaici, duk da ya wajabta musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai takaba fita da rana, kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata a littafinsa na Mugni 8/130.
Duk da cewa wasu malaman Hadisin sun raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan Mas’ud da Abdullahi dan Umar, Allah ya kara musu yarda, maganar Sahabi hujja ce, in har ba’a samu wani sahabin ya saba maşa ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fikh.
Allah ne mafi sani.

Sakin Hannu A Sallah Sunna Ne?
Assalamu alaikum, malam don Allah a warware mana abin da wannan matar take cewa: Ita maganar rike hannu a salla sunna ce ta shugaba saw. haka nan sakin hannu kamar da yake a bukhari da muwadda duk sun nuna cewa Shugaba a farkon rayuwarsa ya saki hannunsa a Sallah, daga baya ya kama hannu daga Karshen Rayuwarsa yaci gaba da sakin hannu, to kunga sunnar da Shugaba yayi sau biyu tafi wadda yayi sau daya. Imamu Malik Imamu Darul hijra a mazhabarsa rike hannu a Sallar Farilla Makruhi ne kuma shine Malamin sauran malaman mazhabar da Saudiyya take bi, don haka sakin hannu bazai zamo bidia ba, kuma ba zamu nunawa imamu Malik sanin Sunnar Annabi saw ba. Ya kamata jamaa musan cewar in mutum bai rushe mana abinda muke kai ba be kamata mu mu rushe masa nasa ba.
To ‘yar’uwa rike hannu a sallah sunna ne kamar yadda Wa’il dan Hujr ya rawaito ya ga Annabi (SAW) yana yi a cikin sallah, kamar yadda ya tabbata a SAHIHI Müslim a hadisi mai lamba ta: 401. Babu ko hadisi guda daya wanda ya tabbata cewa Annabi (SAW) yana sakin hannu a sallah, ko da a kaddara ya saki a farkon musulunci daga baya ya rike, sakın ba zai zama sunna ba, tun da Annabi (SAW) yana aiki ne da wahayi, wahayi kuma a hankali yake zuwa, kamar yadda ba’a shar’anta sallah ba sai a daren Isra’i, babu kuma wanda zai ce barin sallah ya halatta tün da babu ita a farkon musulunci.
An rawaito riwayoyi daban-daban daga Imamu Mâlik akan rike hannu a sallah, daga ciki akwai riwayar Ibnul-kasim a Mudawwanah waccce take nuna hallacin rike hannu a Nafila da kuma karhancin rikewa a Farilla, akwai kuma riwayar Ashhabu da Muddarif da Abdulmalik da Ibnu Nafi’i daga Imamu Malik wacce take nuna halarcin rikewa a Farilla da nafila, kamar yadda Ibnu Abdul Barr ya ambata a Istizkar 2/291 da kuma kuma mai littafin Albayan wattahsi a l /394.
Imamu Mâlik ya rawaito hadisin rike hannu a sallah a cikin Muwadda, a lamba ta: 290, saidai wasu malaman suna cewa ya karhanta rikewa a cikin sallar farilla ne a riwayar Ibnul-Kasim saboda ya sabawa aikin mutanan Madina.
Duk da kasancewar Imamu Mâlik bajimin malami mai tsoron Allah, saidai a matsayinsa na dan’adam yana iya yın kuskure, sannan wasu hadisan da ayyukan sahabbai suna iya buya gare shi, kamar yadda ya tabbatar da hakan a maganganunsa, wannan yasa lokacin da halifan zamaninsa ya so ya iyakance aikin mutane a hadisan da suka zo a Muwadda, Imamu Malik ya hana shi, ya kafa hujja da cewa: a wajan malaman Madina kawai ya yi karatu, akwai wasu malaman da bai hadu da su ba.
Rike hannu a sallah sunna ce tabbatacciya daga Annabi (SAW) kuma hakan shi ne aikin mafi yawan sahabbai da tabi’ai da manyan malamai, ba za’a barta saboda wani malami ba, tare da cewa: wanda ya saki hannu a sallah, bai yi laifi ba, kuma sallarsa ta yi.
Allah ne mafi sani.

Ina Yawan Fitar Da Maniyyi Saboda Mijina Ba Lafiya, Ya Zan Yi?
Salam, Dr. Mace ce mijinta ba ya da lafiyan aure tsawon lokaci, sai ya zamana tana yawan fitar da maniyyi ba sai ta yi wani dogon tunani na sha’awaba, ya matsayin ibadarta yake?

To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, kadange ma’aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.
Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.
Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin? Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.
Allah ne mafi sani.

Assalamu Alaikum. Dan Allah muna neman fatawar ku game da hada salloli lokacin dokar ta-baci. Domin wasu malamai suna ba da fatawar cewa a hada sallar Magariba da Isha, wasu kuma suna ba da fatawar cewa kowa ya yi sallar Isha a gida, wasu kuma suna ba da fatawar cewa a yi sallar magariba sannan Idan lokacin sallar isha ya yi sai a fito domin yin sallar (duk da hadarin da ke cikin karya dokar). To don Allah ku amsa mana domin anfanin al’umar Musulmi.
Wa’alaikum assalam, A fahimtata mağanar wadanda suka ce a jira sai lokaci ya yi tafi inganci, akan wadanda suka ce a hada sallolin, saboda malamai sun yi itifaki cewa Sallah ba ta ingantuwa kafin lokacinta, in ba a wuraren da sharia ta togace ba, amma sun yı sabani game da wajabcin sallar jam’i inda malakiyya suka tafi akan cewa: sunna ce, a wajan Shafi’iyya kuma Fardhu kifaya ce, idan wasu dağa cikin musulamai suka yi sun daukewa ragowar, duk abin da malamai suka yi ittifaki ana gabatar da shi akan abin suka yi sabani, dön haka ba za’a yi sallah kafin lokacinta ba, saboda a riski jam’i, tun da an yi sabani akan wajabcinta.
Bai halatta mutum ya jefa kansa cikin hallaka ba, don kawai ya riski sallar jam’i, saboda hakkokin Allah an gina su ne akan rangwame, wannan yasa mutum zai iya fadan kalmar kafirci idan aka takura maşa, don ya kubutar da kansa, kamar yadda kissar Ammar bn Yasir da aya ta: 106 a suratul Nahal suka tabbatar da haka, dön haka yın sallarku a gida shi ne daidai, ba fitarku ba wacce za ta iya sanyawa a harbe ku.
A Zance mafi inganci sallar jam’i wajibi ce, saboda karfin dalilan da HANABILA suka kafa hujja da su, saidai abin da ya tabbata a ilimin Usulul Fikh shi ne: Sharadi ya fi wajibi karfi, sababi kuma an fi kula da shi fiye da sharadi, lokutan sallah sabuba ne da sharia ta rataya wajabcin salloli akan şu, dön haka za’a gabatar da su akan wajibai, in ba wurin da Allah da manzonsa suka togace ba.
Allah ne mafi sani.
Zan Iya Wankan Janaba Ba Tare Da Alwala Ba?
Assalamu alaikum. Tambayata a nan ita ce: Menene hukuncin yin wankan janaba ba tare da yin alwala ba?
Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar yadda ya zo a hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi (SAW) ya siffanta mata wankan janaba da cewa: “Ya ishe ki, ki zuba ruwa sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in kika yi haka, kin tsarkaka” kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lam bat a: 251.
A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya nuna wankan ya yi da waccar sifar da kika tambaya.
Saidai sifar da ta zo da alwala a hadisin Nana A’isha ita ce mafi cika, kamar yadda malamai suka bayyana.
Allah ne mafi sani.
Ina Fama Da Ciwon Koda, Ko Zan Iya Ciyarwa A Maimakon Azumi?
Asalamu Alaikum malamai na inada tambaya macece bata da lafiya na ciwon koda yafara zama kuronik sai satinnan likitoci suka bata shawara duk bayan minti Talatin taci wani Abu daga Abinci kartakoshi to malam yaya za’a billowa maganar Azumi ciyarwa za’a cigaba da yi ko jira za’a yi sai ta warke ta rama ?
Wa alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauki kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Bakara ta nuna cewa : wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadhana bayan ya samu dama a wasu kwanakin.
Mutukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu saukin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana.
Allah ne mafi sani.
Hukuncin Sanya Zoben Azurfa A Dan Yatsan Dama
Assalamu Alaikum Malam ga wata tambaya nan kamar haka:Assalam da fatan kana lpy! pls ga tambayana menene hukuncin sa AZURFA ZOBE a hanun dama shin akwai wata illa ne koh kuma manzon Allah baisaba?
To dan’uwa ya halatta a sanya zoben azurfa a karamin dan yatsan hagu da kuma dama, Nawawy ya hakaito Ijma’in kasancewar hakan Sunna, saidai akwai hadisi mai lamba ta :2078 a Sahihi Muslim wanda yake nuna haramcin sanya zobe a dan yatsan tsakiya da wacce take binta, wasu malaman kuma sun dauki hanin a matsayin karhanci ba haramun ba.
Allah ya saka da alkairi.
Don neman karin bayani duba Al-majmu’u na Nawawey 4\340.
Amfani Da Motar Ofis A Harkokin Kashin-Kai
Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma’aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum, a ciki ?
To dan’uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta b\a, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.
Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: “Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da b a huruminsa ba ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika’u babil maftuh: 238.
Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da hakan.
An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul’aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama’a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.
Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.
Allah ne mafi Sani.
Ko Maziyyi Yana Karya Alwala?
Assalamu alaikum wa rah matullah malam ina yi maka fatan alkhairi mal. Tambayata anan itace mutum ne yayi alwala yayi komai sai da yaje masallaci ya tayar da sallah sai maziyyi ya fito masa shin malam mutum za sallame sallar ne ko zai karasa ta kuma yaya hukuncin sallar tasa idan ya karasa allah ya karawa malam lafiya da wadatar zuciya, na gode
Wa’alaikum assalam, ya wajaba ka yanke sallah, ka saké Alwala, an rawaito daga Aliyu (R.A) ya ce: “Na kasance mutum mai yawan maziyyi sai na umarci Mikdad ya tambayar min Annabi (SAW) sai ya ce maşa: Idan ya fito ka sake alwala, ka wanke azzakarinka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 266”.
Allah ne mafi sani.
Mijina Ba Ya Sallah, Ko Zan Iya Neman Ya Sake Ni?
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdhana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi?, na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.
Wa’alaikum assalam To ‘yar’uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi S.A.W ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81. Ga shi kuma aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.
Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta: 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan. Sa idai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.
Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.
Allah ne mafi sani
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!