Connect with us

ADABI

Nijeriya Ya Kamata Mu Kalla Ba Kanmu Ba

Published

on

Allah Sarki wani abu sai kasata  Nijeriya da take da mutanen kasar ta da ake kira da suna ‘yan Nijeriya masu basira da kuma nasibi, kai da dai sauran abubuwa na alkhairi da basu misaltuwa. Sun kuma yi fice a fannoni daban daban duk inda suka samu kansu a cikin gida da  kuma waje saboda sun kasance allura cikin ruwa wadda ake cewa sai mai rabo ka dauka, duk inda suka samu kan su na’am ake dasu tamkar karon Kalgo. Sai dai kuma ba ta nan Gizo ke sakar bai dalilin kuwa shine, al’amarin siyasa ko dai ince al’amarin bambance- bambance na siyasa suna neman batawa maimakon ma su gyara al’amuransu. Kowa dai ya san idan ana maganar siyasaa kasar Nijeriya ba za a taba mantawa da wadanda suka yi gwagwarmaya da kuma gwagwagwa, saboda samarwa ita kasar Nijeriya ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na Ingila.

Sun manta da  duk wasu bambance- bambance waje daya suka maida hankalin su wuri daya ba domin komai ba, sai saboda suna son su cimma ‘yancin kai, wanda a wancan  lokacin  shine muhimmin al’amarin daya fi addabar kowanne daga cikin su. An san ana batawa tsakanin ma Harshe da Hakori wadanda ana cewar ‘yanuwan juna ne wadanda kuma suke kwanciya a wuri daya, ballantana wadannan manyan mutane wadanda duk da akwai bambance-bambance da suka sa suka sha bamban amma duk wannan basu sa sun nuna a fili cewar ga abinda ke faruwa  a tskaninsu ba.

Muna iya tunawa da kafin Najeriya ta samu ‘yancin kanta har aka kai ga 1960 zuwa 1966 da ‘yan kishin kasa wadanda suke na hakika kuma kowa yasan sunan da ya dace a kira su ke nan, kamar su  Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda shi ne Firimiya na farko  a kuma jamhuriya ta farko. Ga kuma Dakta Nnamadi Azikwe wanda shi ne shugaban kasa, sai irin su Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato wanda shi firimiyan Jihar Arewa ne, ko kuma sashen  Arewa, sai kuma Samuel Ladoke Akintola shi  na sashen  Yamma ne wanda  ma fi yawansu duk ‘yan kabila daya ne wato Yarabawa. Ga kuma Michael Okpara sashen Gabas wanda a  lokacin  ya  hada da sashen Kudu-maso-Kudu . Shi wannan sashen na Kudu-maso-Kudu, albarkacin wani sabon jadawalin tsarin siyasa inda aka yi ma abin gyaran komada,wanda ake amfani da shi. Shi al’amarin ‘yan siyasa  na gidi sosai kamar su Malam Aminu  Kano , Chief  K. O. Mbadwe, Sir Kashim Ibrahim, Chief Obafemi Awolowo, Alhaji Shehu Shagari, Chief Alban Ikoku, da daisauran mashahuran ‘yan siyasa, wadanda suka ba da muhimmmiyar gudummowa, ko wanne lokaci ne idan ana maganar kishin kasa dole ne  a rika tunawa dasu.

Duk daga cikin su ba  wanda ya manta da gida wato wurin daya baro, sabanin yadda ake da shi yanzu na yadda mutane su ne za su zabi dan siyasa a mukami, amma kuma da zarar ya samu, suka danne mai kan ya tashi ya manta dasu ke nan. Su lokacin na su basu manta da wadanda suke yi ma wakilci ba, da kuma kasar tasu Nijeriya, ba ana nufin suna yanzun bana gidin ba ne ba, amma ai kowa ya san babban goro an ce sai magogin karfe.

Ba laifi ba ne idan muka sake duba wa  da idanun basira ai da tun farko lokacin da aka hada sashen  Arewa da kuma na Kudu cikin shekarar 1914 ana iya cewa shi ala’amari na maganar neman samun madafa ya fara  tasiri ne daga shekerar 1960 zuwa 1966. Akwai dai sassa uku ne, Arewa, Yamma da kuma Gabas, yayin da shi kuma Mid western region an kirkire shi ne a watan Yuni na 1963 daga lardunan Benin da kuma Delta wadanda a farko suna sashen Yamma ne , amma da lardi ne a shekarar 1966. Ritaya janar Yakubu Gowon lokacin da yake shugaban kasa na mukin soja ya kirkiro jihohi goma sha biyu ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 1967, daga nan kuma sai marigayi janar Murtala Ramat Muhammed shi ma ya kirkiro bakwai ranar 3 ga watan Fabrairu shkerar 1976, wanda ya kai jihohin suka zama goma sha tara. Shi kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja ritaya janar Ibrahim Badamasi Babangida  shi ya kirkkiro jihohi har sau biyu ne zamanin mulkin sa abin ya fara ne daga  ranar 23 ga watan Satumba shekarar 1987, sai kuma jihohi tara ranar 27 ga watan Agusta 1991, daganan aka samu jihohi talatin, sai kuma kirkirowa na karshe a tarihin kirkire- kirkiren jihohi a Nijeriya wanda aka yi ranar 1 ga watan Oktoba 1996 lokacin mulkin marigayi janar Sani Abacha inda aka samu shida abinda kuma ya bada jihohi talatin da shida wadanda ake dasu a Nijeriya. Duk wadannan ma basu ishe suba  saboda ‘yan siyasa sun kara samun dama ta sake rarrabar su tsofaffin  sassan biyu wadanda kuma kowa ya san manya ne, wato Arewaci da kuma Kudanci. Wannan lokacin kuma sai suka kira shi da suna geographical location, inda suka fito da sunan  Arewa maso yamma,  Arewa ta tsakiya da kuma  Arewa maso gabas, sai kuma Kudu maso yamma, Kudu maso gabas da kuma Kudu maso kudu. Har yanzun da ganin Biri kowa ya san yayi kama da Mutum saboda kuwa, har yanzu abin bai ishe su ba idan dai masu karatu ba mantawa suka yi ba, saboda kuwa har yanzu suna maganar sake fasalin kasa duk wadannan damarmakin da suka samu har yanzu da alama ba koshi suka yi ba. Wani abu kuma mai daure kai da kuma mamaki idan mutum ya yi tunani, shi wannan duk kiraye- kirayen da ake yi.  Idan ma romon damukuradiyyar ya samu wadanda za a gani daga babban dan siyasa sai kuma wani babban dan Boko, shi kuwa Talaka koma an ce za ayi tafiyar da shi wani lokaci ana barin shi ne a ko daikofar gida ko kuma wani babban zaure, bayan kum ai da bazar shi ce ake taka rawar. Kai koda ma kananan Hukumomi 774 aka ce yau an maida su jihohi, to ba za rasa wadanda zasu ce ba a yi masu adalci ba,  ko kuma ana kwararsu saboda yadda shi al’amarin ‘yan Nijeriya yake, su kan kori Kare gindin Dinya ne saboda su ci. Wani lokaci ma idan irin wadannan mutane wadanda basu da kishin kasa suka kuma sa’a aka kashe aka basu, har suka samu kan su a majalisa, kodai ma ko wanne mataki ne sai mutum ya kasa gane ya  ma shi al’amarin yake ne. Haba ai sai wasu  daga cikin ku, ku yi tunani mana ku gane fa duk karyar Kiri ai ta Mai ce, kar maida abin su ya zama naku, idan da su wadanda suka fara dora tubulin gina siyasar Nijeriya sun yi kamar dai yadda ku keyi ma wasu, kuna tsammani ne da sun yi hakan har zaku samu kasancewa inda kuke yanzu?.

Har yaushe kuma za a ci gaba da hakan wato da an ji an ba wani mukami, sai ka ji wasu na maganar cewa daga wane geographical location yake, wani sabon jadawalin da ‘yan siyasa suka bullo da shi. Daga nan kuma sai a ci gaba da maganar daga wace jihar yake, idan an kammala da wannan sai karamar Hukuma kai har dai a kai ga ward wato mazabar Kansila. Idan ka tambaye dalilin da yasa yake wannan maganar sai ya baka amsar yana son yaje ya gaida shi ne, wanda ba maganar  ayi ma unguwar da yake ko kuma gari abinda zai kawo ci gaba maganar wata matsalar kan shi  ne zai yi. Koda an haifi Kakanni ko kuma iyayen mutum a wata jihar daba ta asalin tasu ba, sai a rika maganar ai su ba ‘yan asalin jihar ba ne, koma wani abu kuke so sai dai ku je jiharku ta asali a yi muku.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!