Connect with us

MAKALAR YAU

Rawar Da ‘Yan Barandan Ekweramadu Suka Taka A Magudin Zaben 2003

Published

on

Ci gaba daga makon jiya
Mista Igaga Ogbonna ya fadi cewa, ya kasance yana Ofishin hukumar zabe na Karamar Hukumar Ani Nsi da misalin karfe takwas da rabi na safe (8:30am), sai ga Sojoji Mota biyu sun shigo tare kuma da wata Mota kirar Fijo 504. Sai wadannan Sojoji suka kwashi kayan zabe na adadin Mazabu goma (10) dake a wannan karamar hukuma ta Ani Nsi, suka fice da su.
Sai Mr Igaga ya bi sawun wadancan Mazabu goma (10) wadanda suke kunshe da tashoshin zabe arba’in (40) da Sojoji suka karbi kayan zabensu da zimmar za su kai. Wani abin mamakin shi ne, sai ya zamana ko Mazaba daya jal ba a kai wadancan kayan zabe ba, hana- rantsuwa, sai Mazabar Mpu ce kawai aka kai mata kayan zabenta. Ko mai karatu ya san dalili? Ita ce Mazabar Sanata Ike Ikweramadu.
Ganin cikin Mazabu 10, tara 9 kadai ne aka sadar da kayan zabensu, sai Mr Igaga ya yanke shawarar zuwa gidan Sanata Ikweramadu don sanar masa halin da ake ciki na kamfar kayan zabe. Da yake abin mamaki ba ya karewa cikin Kasata Nijeriya, ko da Igagu ya shiga gidan Sanatan da yake son gabatar masa da wancan korafi, sai ga idanunsa sun gane masa sauran kayan zaben da ya dace tuni an mika su zuwa ga wadancan Mazabu 9, wasu Katti sun dukufa suna ta faman daddana yatsa bisa takardun zaben, tare da cusa su cikin akwatinan zaben.
Bayan idanun Igaga sun gane masa wancan alkaba’i, sai wani Soja ya ce da shi, ba zai sami damar ganin Sanatan ba. Juyowar nan da ya yi zai tafi, sai ga wata Mota kirar Bas ta kunno kai cikin gidan Sanatan. Gungun wasu Matasa ne makare cikin Motar, hannayensu dauke da muggan makamai. Suna ganin Igaga, sai suka dora fadin;
“…Kai Dan APP, me ka zo yi nan?…”
Ashe zai yu Mutum guda daya zikau fitacce dake da wani banbancin ra’ayin siyasa da babban Mutum irin Sanata ya kwashi jiki ya je gidansa a ranar da ake gudanar da zabe, alhali ma ba wani Dan’uwansa ne ba? Kajima wai ashe korafin rashin kai kayan zabe zuwa mazabu zai gabatar masa. Toh! wai shin, ko sharri wadancan Matasa ne za su yi masa, don su sami wata kafar cutar da shi?.
Ko ma dai menene amsoshin wadancan tambayoyi na sama, wadancan Matasa dai san mangare Igaga ne har kas, sai ga wancan Soja shi ma ya lababo ya kantarawa Igaga gindin bindiga a tsakar -ka. To shi kuma wannan Soja Dan wace jam’iyya ce ke nan?. Haka dai Igaga ya tashi yana tangadi zuwa cikin Motarsa, daga nan, ya zarce zuwa shagon mai magani.
(Election Petition, No. CA
/A/EP
/3/03, Bol. 2: 127-128).
Sunday Onah ya fadi cewa, ranar zaben Shugaban Kasa (19/04/2003), ya ziyarci Mazabu guda tara (9) cikin goma (10) da ake da su a Karamar Hukumar Nsukka, amma bai iske kayan zabe ko wani Malaman Zabe cikinsu ba. Sannan, ga dandazon jama’a na jira a kawo kayan zaben su kada kuruunsu. Cikin wannan yanayi na rashin kayan zabe aka cigaba da kasancewa har zuwa karfe biyu na rana (2:00pm).
A Jihar Cross Riber, 2003
Mr Godwin Ushie dake a karamar hukumar Obudu, ya labarta cewa, ya ziyarci Mazabu shida (6) cikin Mazabu goma dake a wannan karamar hukuma, don ganewa idanunsa irin yadda sha’anin gudanar da zaben ke tafiya. Sai dai fa Ushie ya tabbatar da cewa, har zuwa karfe biyar na Yamma (5:00pm) hukumar zabe ba ta aike da kayan zabe zuwa wadancan Mazabu 6 da ya sami sukunin lekawa.
Ko da Godwin Ushie ya niki -gari zuwa Ofishin Hukumar Zabe na wannan karamar hukuma ta Obudu, don gabatar da korafi game da rashin aikewa da Kayan Zabe zuwa wadancan Mazabu 6 da ya leka, sai ya zamana ko Jami’in Zabe guda daya bai riska ba a Ofishin. (Idem., P. 141).
Mr Godwin ya fadi cewa, washegarin wannan Zabe na Shugaban Kasa (20/04/2003), sai kawai ya ji hukumar zabe na shelanta jam’iyyar…ce ta lashe zabe a daukacin jumlar Mazabu goma (10) da suke a Karamar Hukumar Obudu. (Idem.).
A Jihar Kogi, 2003
Farfesa Usuf Otaru Alia ya shaida cewa, cikin Tashoshin Zabe ashirin (20) dake a Mazabarsa ta Lagia/Obesse, yaziyarci akalla guda goma sha -biyar (15), amma, babu inda ya samu a na gudanar da wani zabe ciki.
(Idem., P. 161).
Hana Jama’a ‘Yancin Kada Kuru’unsu
An samu cikin Zaben da aka yi na Shekarar 2003, akan hana Jama’a ‘Yancin da suke da shi na zabar ‘Yan-Takarar da suka kwanta -musu -a -rai, suke son su jagorance su a matakai iri daban -daban na madafun -iko. A baya can, idan mai karatu bai manta ba, an nusar da cewa, Zabe kan amsa cikakkiyar ma’anar sunansa ne kawai, yayinda aka sakarwa al’uma mara suka zabi abinda ransu ke so ko bege.
A kan turbar bincike za a iske cewa, akwai mabanbantan dalilai da suka yi uwa -suka -yi -makarbiya wajen kange jama’ar Kasa, ga zabar abinda ransu ke da muradin zabe, a Shekarar Zaben ta 2003.
Daga cikin dalilan wancan mummunan tauye hakki na masu zabe, akwai hadin -baki da akan samu tsakanin jam’iyya mai gwamnati da wasu bata -gari daga Malaman Zabe. Wani lokaci kuma, burbushin kabilanci ko bangarenci da suka ginu a zukatan wasu ‘YanKasar, kan jaza afkuwar irin wannan ta’ada. Za ma a iya samun wasu dalilai sabanin wadanda aka gabatar.

Ga wanda ke biye da mu a tun farkon wannan rubutu, abin yi wa take da, “Zabe A Nijeriya”, an gabatar da rukunin wasu mutane dake haifar da matsalolin dake jaza tabarbarewar lamuran Zabe cikin wannan Kasa ta Nijeriya tsawon lokaci. Ba ya ga aji -aji na Mutanen, an yi bayanin cewa, hatta Kundin Tsarin Mulki na Kasa da Dokar Zabe ma, na da irin nasu tsarmakatai ko a ce matsalolin da kan zama tuntube bisa turbar samun ingantaccen zabe a wannan Kasa.
Kamar yadda aka fara gabatarwa, akwai bukatar gabatar da kura -kuran da zugar wadancan ababe kan haifar ga sha’anin zaben daki -daki. Yin hakan ne kadai a ilmance kan iya tabbatar da wancan ikirari da aka yi a sama. Badakalolin da suka haifar cikin Zabukan Shekarar 2003 da ta 2007 da kuma kyautatuwar lamura da aka fara samu ne cikin Shekarar zabe ta 2011 ne aka nufaci kawowa. A karshe kuma, sai hasashen mafita ne zai biyo baya.
Ba a na gabatar da tarihin ababen da suka faru a baya marasa dadi game da Zaben ba ne kawai don nishadi ko son nuna iyawa. Ko kadan! ba haka ne muradi ba, face, a duk sa’ad da ake son gyara wasu gurbatattun halayya, a Addinance ne ko a Zamanance ne, gabatar da tarihi game da illar da wannan ta’ada ta haifar a baya, kan zama wani abin nema ko ma WAJIBI. Ta hanyar hakan ne, wanda bai riski wancan lokaci ba, da ma wanda ya riska, za su yi tintintuni gami da karatun -ta -nutsu don kaucewa mummunan sakamakon dake biyo baya sanadiyyar aikata waccan halayya.
Sai an kalli Jiya sosai ne za a iya gyara Yau. Idan an yi gyara Yau ne za a mori Gobe. Sabanin haka kuwa, za a yi ta tsalle ne a wuriguda.
Mai karatu kamar yadda kake biye, a wannan gaba, a na gabatar da wasu matsaloli ne da Hukumar Zabe karkashin jagorancin Marigayi Dr Abel Guobadiya ta haifar a zaben Shekarar 2003.
Kungiyoyi da daidaikun mutane, sun zargi hukumar zaben game da halayyar da ta nuna karara, ta kaucewa kirga kuru’u a matakin farko bayan kammala gudanar da zabuka a Tashar Zabe. Aikata hakan, na daga ababen da Masana ke wa kallon wani nau’i na tafka magudin zabe.
Kungiyar sa -ido ta E.U, ta yi bayani game da irin wancan yunkuri na hukumar zabe, na yin mursisin kidaya kuru’un zabe yadda doka da ka’idar zabe suka aje. Kungiyar ta ce,
“…A jihar Imo, akwai kayayyakin zaben da suke bayan an kammala gabatar da zabe, maimakon a tsaya a kirga a shigar da su cikin takardun sakamakon zabe, kawai sai aka sunkuce su zuwa matakin karamar hukuma, alhali tashar zabe ce matakin farko na kidayar kuru’un…”
(The News, May 5, 2003).
Shi ma Chief Sergent Awuse ba a bar shi a baya ba wajen gabatar da makamancin wancan korafi na rinton kidayar kuru’u. Chief Awuse ya ce,
“…Da yawan tashoshin zabe ba a samar musu da takardun cike sakamakon zabe ba. Sai aka rika danga irin wadancan takardu a hannun wasu Manyan Mutane na jam’iyyar gwamnati, sai ya zamana sun hakimce daga can gidajensu, suna cike wadancan takardu da sakamako na aringizon da ko kusa hankali ba zai taba lamunta ba…”
(Ibid.).
A Jihar Cross Ribers, 2003
A kan hayyar Kungiyar E.U. na bayyana rufa -rufar hukumar zabe game da lasafta kuru’u a halastaccen mataki, ta fadi cewa, wani magudin lissafin kuru’u da aka rika samu a wasu tashoshin zaben dake jihar Cross Ribers, ya haifar da kace -nace matuka.
A tashoshin zaben na C.Ribers din ne, ringidi -ringidi za a ga ga wadancan takardun shigar da sakamakon zaben an zo da su mazaba, kuma da farko kamar gaske, za a kirga kuru’un bayan kammala zabe, amma sai a ki shigar da sakamakon lissafin cikin takardun saboda tsagwaron son -zuciya.
Daga bisani, sai aka dinga ganin sakamakon zabe mai daure -kai, rubuce cikin wadancan takardun da ake rubuta sakamakon zabe. Cikin wata takardar sakamakon zaben, sai a ga, ga adadin kuru’un zabe kimanin dari biyar da arba’in (540) rubuce ciki, amma wai kuru’u dari biyar da talatin da biyar (535) jam’iyyar gwamnati ce ta lashe su.
(The News, May 5, 2003 : 27).
A Jihar Enugu, 2003
Game da irin wancan magudin shigar da sakamakon zabe da ya yawaita cikin wancan zabe na Shekarar 2003, ita ma jihar Enugu ba a bar ta a baya ba wajen afkawa cikin bakar ta’adar.
Kungiyar E.U. ta fadi cewa, wasu cikin wakilanta sun gani da idonsu, inda wasu jami’an hukumar zaben ke wa wasu takwarorinsu shiftar sakamakon zaben, su kuma suna shigarwa cikin takardun.
Rufe Tashoshin Zabe Kafin Cikar Lokaci.
An rika samun wani nau’in magudin zabe, ta hanyar rufe tashoshin zabe gabanin sanannen lokaci da Doka ta ayyana za a rufe. Ga wanda ya nitsa cikin hanyoyi na dabarun tafka magudin zabe da aka yi amfani da su a Shekarar zabe ta 2003, zai kai ga fahimtar cewa, rufe wadannan tashoshin zabe ba bisa ka’ida ba, bai rasa nasaba da cewa, muddin za a cigaba da gudanar da zabe cikin wadannan tashoshin zabe, babu makawa jam’iyyun da ba na gwamnati ba ne za su kai ga samun nasarar lashe zabuka.
Da yawan tashoshin zaben da za a ga an rufe, sai a iske cewa, ba wani yanayin ta da hankula ba ne ya jaza rufe sun, face wasu dalilai na son zuciya ne tsagwaro. Domin kuwa kamar yadda aka hakaito a baya, ai za a ga ma cikin wasu tashoshin zaben, a kan sami nasarar afkar da husuma ne ta hanyar hadin -baki tsakanin ‘YanDaba da Jami’an tsaro ne. Ko kuma tsakanin jami’an tsaro da su Honarabul.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!