Connect with us

RA'AYINMU

Tilas Matasa Su Guji Tayar Da Tarzomar Zabe

Published

on

Babu tantama kan cewa matasa ne kashin bayan kowace al’umma. Kamar yanda babu tantaman kasancewa Nijeriya jagaba a cikin kasashen da Allah Ya azurta da yawan matasa a duk Duniyar nan, matasa ‘yan tsakankanin shekaru 18 zuwa 35 ne suka kumshi kashi 50 na al’umman kasar nan milyan 180. Wannan ne kuma ya maishe da Nijeriya jagaban a matsayin mafiya arzikin albarkatun al’umma.
Sai dai abin takaici, duk da tulin matasan da muke da su wadanda sun isa su bunkasa kowane irin tattalin arziki, matasan sun kasance nauyi ne kadai ga Nijeriya, a bisa dalilin rashin aikin yi, da kasancewar matasan a cikin ayyukan assha, shan miyagun kwayoyi, ayyukan asiri da kasancewar matasan mafiya yawa a cikin ayyukan aikata laifuka.
Wani babban abin damuwa a tarihin siyasarmu shi ne, yanda ake amfani da matasan a matsayin ababen aiki na tayar da rigingimun zabe, a inda a kan dauki nauyin su domin su keta dokokin zabe, a bisa kudurin iyayen gijin su na ganin su a kan mulkan al’umma ta ko halin kaka. rikicin zabè yana aukuwa ne tun ma kafiin zaben da lokacin zaben da ma bayan an yi zaben.
Tashin rikici kafin zabe yana faruwa ne a dalilin zage-zage da kalaman batunci a lokutan yakin neman zabe. Yawanci kuma hakan yana farowa ne daga kafafen yada labarai na yanar gizo, a kan yanda magoya baya kan ta kokarin su na ganin sun bata abokan hamayyar su na sauran Jam’iyyu da ‘yan takara ta hanyar kwaba duk abin da ya zo bisa harshen su ga abokan hamayyar na su.
A lokacin zaben kuma, matasan magoya baya a kan yi amfani da su wajen kwace akwatin zabe, siyar da kuri’u da sayen kuri’un, tsokana da sauran ayyukan banga. Shi kuwa rikici a bayan zabe yana faruwa ne daga inda magoya baya suke sukan sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta shelanta. A wannan lokacin magoya bayan dan takaran da bai yi nasara ba mafi yawa sukan tayar da yamutsi, inda suke zargin an yi wa dantakaran su magudi.
A shekarar 2011, Hukumar kare hakkin dan adam ta kawo rahoton da ke nuna cewa, a sakamakon munanan rigingimun zabe da aka samu a arewacin Nijeriya, a sakamakon zaben Shugaban kasa na watan Afrilu na 2011, mutane sama da 800 sun rasa rayukan su, sannan sama da mutane 65,000 ne aka daidaita. Zaben 2015, yana daya daga cikin zabukan da suka haifar da firgici na yiwuwar tashin yamutsi, musamman a sassan arewacin Nijeriya, a kan zaton rashin amincewa da sakamakon zaben na Shugaban kasa.
Sai dai, hakan bai kasance ba, a bisa Shugaban kasa na wancan lokacin, Dakta Goodluck Jonathan, ya dauki matakin da ba a saba da shi ba a siyasar Afrika, ta hanyar taya babban abokin hamayyarsa, Muhammadu Buhari murna, a daidai lokacin da ba a ma kammala kidaya kuri’un ba.
Wannan Jaridar tana ganin mahimmancin tunatar da matasan irin mahimmancin da suke da shi na nauyin da ya hau kansu a wajen ganin an gudanar da zaben wannan shekarar a cikin kwanciyar hankali. Akwai bukatar su fahinci cewa a duk inda aka gudanar da wani zabe, to tilas ne fa a sami wanda ya yi nasara da wanda bai yi nasara ba. Su kuma fahimci cewa, duk masu son ingiza su domin su tayar da tarzoma, mutane ne da ba sa masu fatan alheri, don kuwa in ba hakan ba, kan me su za su zaunar da ‘ya’yansu a can lafiyayyun makarantu da ke kasashen waje, sannan su zo suna amfani da ‘ya’yan wasu a matsayin ‘yan bangan siyasan su, su kuma sanya su suna jefa rayukan su a cikin hadurra.
Nan da ‘yan makwanni za a gudanar da wani zaben, alamu kuma na samun rikici a cikin zaben suna ta kara habaka, bisa kasancewar magoya bayan ‘yan takara daban-daban suna ta jefa kalaman da ba su kamata ba ga abokanan hamayarsu a shafukan yanar gizo.
Don ganin an magance irin wannan abin takaicin, wannan Jaridar tana da ra’ayin ganin an ilmantar da manema labarai, ma’aikatan gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, Jam’iyyun siyasa da ma shugabannin Addinai a kan yanda aka shirya gudanar da zaben.
Sauran masu ruwa da tsaki kamar iyaye, Sarakunan gargajiya da shugabannin Addinai duk ya kamata su taka rawa sosai wajen wayar da kan matasan da ke karkashin su da magoya bayan su a kan su gyara halayen su, su kasance masu rungumar sakamakon zabe. Musamman ma dai iyaye, ya kamata su sanya wa ‘ya’yan su ido kud-da-kud a kan harkokin zaben, su tabbatar ba su kasance a cikin ‘yan bangan duk wani dan siyasa ba.
Su ma ‘yan takaran da suke neman mukamai daban-daban, ya kamata su wayarwa da magoya bayan su kai a kan nisantar aikata duk wani abin da zai iya cutar da wani.
A matsayinmu na Jarida, muna yin kira ga matasa da su gane cewa makomar wannan kasar tana hannun su ne, sannan kuma abu mafi kyau a gare su shi ne kar su aikata duk abin da zai iya lalata masu rayuwar su.
Su fara da cewa na ki, a yi amfani da ni wajen kawo hargitsi a babban zaben wata mai kamawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!