Connect with us

TATTAUNAWA

‘Yan Majalisa Sun Kunyata Nijeriya – Imam Ahmad

Published

on

Imama Suleiman shi ne babban Limamin Masallacin Jumma’a na garin Magama Gumau, cikin Karamar Hukumar Toro dake Jihar Bauchi, ya ce, ‘Yan Majalisar Kasar nan sun kunyata Nijeriya, Imam Ahmad Sulaiman ya fadi hakan cikin tattaunawarsa da wakilummu, in da ya tabo batutuwa daban-daban ciki har da batun mika kasafin kudi da Shugaban kasa ya yi ga ‘yan Majalisa. Ga yadda hirar ta kasance.

Akaramakallah zan so ka fara gabatar da kanka ga masu karatu
Suna’na Ahmad Suleiman, ni ne Limamin Masallacin Jumma’a na garin Magama Gumau.

kowance shekara Shugaban Kasa yana gabatar kasafin kudi ga Majalisa, ya kake lallon na wannan shekara?
Gaskiya kasafin kudi da Shugaban Kasa ya mikawa ‘yan MajalisA su yi nazari su mika masa ya sa hannu don a yi wa al’umma aiki abin a ya ba ne ainun, wannan yana nuna cewa Shugaban Kasa yana kishin ganin cigaban Kasar nan. domin idan ka duba kasafin kudin bana ya fi na ko wace shekara ya wa, kuma ya fi na ko wace shekara tsari bisa yadda aka kasafta shi, idan ‘yan Majalisa sun yi nazari sun mika wa Shugaban Kasa a cikin gajeren lokaci ya sa sannu aka fara aiwatar da shi cikin lokaci zai amfanarwa al’ummar kasar nan musamman ma ta wajen gudanar da manyan ayyuka da Gwamnati ta fara gudanar da su ga al’ummar Kasar.

A bara ‘yan Majalisa sun yi jinkirin mika kasafin, mecece shaararka game da na wannan shekarar?
Shawarar da zan bai wa ‘yan majalisar na yanzu da ma wadanda za su zo a nan gaba, duk lokacin da shugaban kasa ya mika masu kasafin kudin to su yi gaggawar yin aiki a kai don mika masa cikin lokaci saboda ya sa hannu a kai don su yi wa talakawan da suka zabe su aiki.
Ba wai sun je ne don azurta kansu ko neman jin dadin kashin kansu ba, kuma duk mutanen kasar nan su fahimci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mutum ne adali da yake shugabacin Kasar nan ba tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba domin idan ka duba irin ayyukan da gwamnati mai ci yanzu karkashin jagorancinsa ke gudanarwa a jihohin kudancin kasar nan da wadansu sassa na kasar, za ka amince shi Shugaba ne na kowa ce kabila dake kasar nan.

To me za ka ce bisa rudanin da aka samu dai-dai lokacin da Shugaban ke jawabin mika kasafin kudin?
Gaskiya ‘yan Majalisa sun yi abin kunya, domin sun kunya ta Nijeriya a idanun duniya, saboda duk duniya ba kasar da aka samu ‘yan Majalisa suna ma shugabansu ihu a lokacin da yake mika kasafin kudi ko yake jawabi ga al’ummar Kasarsa ko dabbobi ba za su yi wa Shugabansu haka ba, domin idan ka duba jerin dabbobi irin su kwari kamar Gwano da tururuwa, Gara da sauran nau’in dabbobi kamar shanu, tumakai, da ire-irensu ba sa wa shugabansu tawaye wajen jagoranci, amma sai ga ‘yan Majalisummu sun zo Majalisa mai makon yin muhawara mai ma’ana sai suka shiga yin shewa da ihu ga Shugaban Kasa, wannan babban abin kunya ne.

To ma ye shawararka a nan game da wannan abin kunya?
Ni fahimta ta a nan shi ne, ‘Da kwai walaki goro a miya,’ wala’alla ko buguwa ta shaye-shaye, ko tabuwar hankali, domin wannan ya wuce kiyayya, kuma ina bai wa Shugaban kasa shawara da ya sa a kafa kwamiti na masu binciken tabuwar hankali ko na masu shan kayan maye da za su rika tan-tance duk wani dan takara da zai nemi jagorantar al’ummarsa a majalisa, in an ga shi ba mai shaye-shaye ba ne sai a yarje masa ya sayi fom din neman yin takara a kan kowane mukami na Shugabanci a majalisa, idan kuwa aka ga shi mai shaye-shaye ne ko mai jinin hauka sai a hana shi fom din neman takara.

Kasancewar zaben 2019 sai kara kusanto wa yake yi, ya kake auna wadannan ‘yan takara ko?
Hausawa sukan ce ido ba mudu ba ne, amma ya san kima ni shawara ta a nan a zabi adali a dubi mutumin kirki mumini mai adalci ba sai na ce wane ko wane ba, mutane ne za su yanka wa kansu hukunci.

A kwai daga dattawan Arewa da suke kada a zabi Buhari a zabi Atiku, me za ka ce?
Masu wannan kira sun fadi ra’ayinsu ne kawai, domin ba yadda za a yanke wa mutanen Arewa hukunci a kan su zabi mutum guda daga cikinsu don dukansu fulani ne daga Arewa, ni yadda na fahimci irin wadannan masu kiraye-kirayen biyan bukatun kansu kawai suke nema, saboda shekaru nawa suka yi suna jagaranci, me suka yi wa mutanen Arewa din abu guda da za su fada masu.

Ba ka gani ko sun fadi haka ne don suna ganin Buharin ya gaza cika alkawuran da ya dauka?
To da farko dai ni a gani na duk alkawuran da Shugaban kasa ya yi wa al ummar kasar nan lokacin yakin neman zabensa ya cika su, domin a dai-dai wannan lokaci da nake zantawa da kai a shirinsa na Empower, daga cikin kashi 100 da aka yi wa matasan kasar nan alkawari kashi 60 daga cikinsu yanzu na morar wannan shiri, kuma a bangaren shiyar da yara a makarantu ana nan ana gudanar da shi a ko wace Jiha ta Kasar nan. Ta fannin noma kuwa, yanzu an daina shigo da tan-tan na abinci daga kasa’shen ketare, yanzu mu muke shiyyar da kammu, kuma idan muka koma ta bangaren tsaro an sami zaman lafiya idan aka kwatanta da baya kafin zuwan wannan gwamnati, domin akwai wani lokaci mutanen Kasar nan suna zaman dar, dar ako ina suke cikin Masallatai ne ko Coci-coci da majami’u, kasuwanni da tashoshin mota, duk zaman dar-dar ake yi. Yau an wayi gari duk wadannan abubuwa sun kau da wadannan nake ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taka rawar gani, sabo da haka kada mutane su yarda da irin wadannan kiraye-kirayen.

To idan muka koma jihar ka ta Bauchi wadansu na cewa kada a yi ‘Sak’ me za ka ce?
To ni kam zan ce ‘yan adawa ne kawai suke irin wannan kira domin in dai ba a sami hadin kai a tsakanin al’ummar jihar nan ba kamar zuwar wannan gwamnati na Gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar, kuma idan ka koma ta bangabangaren taimakawa al’umma nan ma Gwamna ya yi rawar gani wajen taimakawa ‘yan kasuwa manya da kanana, ya kuma taimakawa wadanda rikice-rikicen kabilanci da na Boko-Haram ya shafa, kuma suka nemi mafaka a jihar Bauchi. Ta fannin aiwatar da ayyukan inganta rayuwar al’umma kuma, nan ma ya yi rawar gani idan ka duba bangaren gyaran hanyoyi da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, ilmi da aikin gona da samar da ruwan sha wadatacce ga al’ummomin da ke zaune a dukkan sassan jihar saboda haka nake ganin yin ‘Sak’ a jihar Bauchi yana na da akhairi domin hakan zai ba shi damar kammala ayyukan ci gaban al’ummar Jihar da ya farasu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!