Connect with us

ADABI

Bakonmu Na Wannan Makon Shi Ne Kamal Minna Marubucin Littafin  Muradina

Published

on

Kamar kodayaushe wannan shafin ya sake zakulo muku wani marubucin litattafan Hausan don jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rubutun littattafan Hausa ga kuma yadda hirar ta mu ta kasance:

Ya sunan Malamin?

Sunana Kamal Muhammad Lawal wanda aka fi sani da Kamal Minna.

 

Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinka.

Ni Haifaffen jihar Neja, a nan  na yi karatun firamare da sakandire a cikin Gwada wato kauyenmu, daga nan na dawo Kano, inda na shiga makaranatar makamar kwamfyuta na yi Difuloma. A bangaren addini na yi karatu daidai gwargwado har matakin sauka gami da littafan addini.

 

Idan muka koma bangaren rubutu shin me ya ba ka sha’awa ka tsumduma cikin harkar rubuce-rubuce?

Ba zan iya ce miki ga dalilin fadawata duniyar rubutu ba, kawai tsintar kaina na yi a cikin harkar. Sai dai tun ina kankani Allah ya dora min son harkar rubutun kirkira a rayuwata don a lokacin da na fara koyon kirkira ban wuce aji uku a firamare ba.

 

Lokacin da za ka fara rubutu wane irin tata burza ka fuskanta cikin rubutun kuma ya rubutun ya kasance a lokacin?

Gaskiya lokacin da zan fara rubutu ban  fuskanci wata matsala ko wata fargaba a raina ba.         *

 

Kamar shekara nawa  ka yi kana rubutu?

Shekarun da na fara za su kai goma zuwa sama,  amma zama na cikakken marubuci wanda ya rubuta cikakken labari har ya shiga duniya zan kai shekara hudu zuwa biyar.

 

Wanne littafi ka fara rubutawa?

Littafin da na fara rubutu wa sunansa ‘Muradina’ amma fa maganar gaskiya ba zan ce miki ga duniyar da ya shiga ba yana raya ko ya mutu Allah masani.

 

A kan me ka rubuta littafin ma’ana me littafin yake kunshe da shi?

Labarin ya karkata ne ga ‘yan ubanci, shine babban jigon labarin, a kan wani matashi ne da ya kasance shi kadai a wajen mahaifiyarsa, mahaifinsa na da kudi, tun yana karami mahaifiyar tasa ta rasu sai ya kasance rikonsa ya koma hannun kishiyar mahaifiyar tasa to ita kishiyar mahaifiyarsa ita ce babba kuma ita mai ce manyan ‘ya’ya.

Lokacin da mahaifin nasa ya rasu sai gaba daya kishiyar mahaifiyar tasa suka nemi batar da shi a duniya,  saboda son cinye gado.  Daga karshe suka yi masa kurciya sai ya fada wata nahiyar in da ya hadu da wata yarinya Bafulatana daga yankin Mambali da yake iyaka da Nijeriya to dai rayuwar ta su a nan take tabbata har dai kalmar ta MURADINA ta fito…

 

Me ya ba ka wahala lokacin da kake rubuta labrin kuma wane tsawon lokaci ka dauka kana rubuta wa?

Abin da ya fi ba ni wahala a lokacin daidatuwar Hausata, domin ina samun matsala wajen rubutu wasu kalmomi, ba na saka su daidai domin yadda nake fadinsu a baki haka nake rubuta su sannan kuma kin san Hausar baka daban take da rubutacciya. Abin da ya fi ban wahala ke nan a rubutu daidaituwar kalmomin Hausa.

 

Lokacin da ka gama kammala rubuta littafin shin buga wa ka yi ko kuwa a online ka sake shi?

Gaskiya ban buga shi ba sannan ban rubuta shi a online ba, hasali ma lokacin ban san ana rubutun online  ba.

 

Masu karatu za su so su ji shin ka taba buga littafinka ko kuwa iya online suke futa?

E, na taba bugu littafi kuma ya shiga kasuwa mai suna  ‘ABIN SIRRI NE’ shi ne littafina na farko da na buga shi ya shiga kasuwa shekara daya da rabi ke nan.

 

Ya karbuwar littafin ta kasance wajen makarantan?

Maganar gaskiya littafin ya karbu sosai ga makaranta don ban taba tsammani ba da fitarsa kasuwa ko sati bai cika ba, na fara samun sakonni da kira ta waya abin ya yi matukar ba ni mamaki

 

Shin littafin ‘ABIN SIRRI NE’ wanne sako yake isarwa kuma me ya ja hankalinka har ka rubuta shi?

Eh to labarin ‘Abin Sirri Ne’ na yi shi ne a kan ‘ya’yan riko a hannun kishiyar’uwa da yadda suke fuskantar rayuwa ta rashin jindadi, Sannan na tabo bangaren yadda ake safarar ‘ya’ya mata da sunan fid da su daga kauye zuwa birni da sunan aikatau gidan masu kudi bayan kuma da yawan wasu ba hakan ne ba. Kai su ake yi ana sayar musu da yancinsu, sannan kuma ya tabo fannin da wasu masu kudin suke ganin ba za su iya aura wa ‘ya’yansu samarin kauye ba, da sunan wai ba su waye ba.

 

Kamar littattafai nawa ka rubuta tsawon shekarun da ka dauka kana rubuce-rubuce?

Gaskiya ban yi wani rubutu masu yawa sosai ba, a kalla dai za su kai goma ina daukar lokaci kafin na daura alkalamina, bayan na gama nazarin abin da zan rubuta a kwanyata sannan nake daura alkalamina.

 

Ko za ka iya fada wa masu karatu sunayen littattafan da ka rubuta?

E, jerin sunayen littattafan da na rubuta su ne. Muradina, Ingantacce, Namiji…, In Da Ranka…, Abin Sirrin Ne, Ra’ayinmu Daya, Ranar Nadama, Duniyarmu, Uku Bala’i, Makauniyar Biyayya, Kudirina, da Kazamin Buri.

 

Wane marubuci ne ya fi burge ka a salon rubutu?

Ni ko wane marubuci yana birge ni in har na karanta labarinsa domin na tabbata ba zan rasa abin karuwa a cikinsa ba. Bayan nan ina da zababbun marubuta da suka yi tasiri sosai a rubutu, don har ga Allah ina jinsu kuma ina gode musu duk da dai ba wai mun hadu da su fuska da fuska ba ne, na dauki darasi ta salon rubutunsu  da nake karantawa a littattafansu. Ya yi tasiri a alkalamina, musamman irin su: Maimuna Idris Sani Beli, Sumayya Abdulkadir Takori, Abubakar Auyo, Lubabatu Maitafsir. Maganar gaskiya ina alfahari da tsarin su da salon rubutun su in har na karanta labaransu har wani karkasashi da zakuwa na nishadi nake ji game da rubutu in ji a duniyar ba abin da nake so na ci gaba da yi kamar rubutu.

 

Mene ne burunka na gaba game da rubutu?

Burina a duniyar rubutu a kullum shi ne, Allah ya tsare mani alkalamina da duk kalmomin da zan yi har karshen numfashina sannan Allah ya ba ni ikon yin rubutun da har in mutu ba za a taba mancewa da shi ba, a filin duniyar nan a koyaushe a dinga tuna wa da ni sannan kuma rubutun ya zamo sanadi na gyaruwar wasu matsaloli na al’umman duniya.

 

Allah ya yarda, shin kana cikin wata kungiya ne na marubuta ko kuwa baka ciki?

Eh to ina cikin wata kungiyar marubuta amma fa online mai suna ‘Zamani Writter Association’. Sannan kuma a zahirin marubuta masu buga littafi ina zuwa taronsu na kungiyoyin amma dai har yanzu ban zama cikaken dan kungiya ba, wato dai ban yanki fom ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!