Connect with us

WASANNI

Ko Kun San Wacce Kungiya Ozil Yake Son Koma Wa?

Published

on

Tun bayan da sabon kociyan kungiyar, Unai Emery yafara aiki a Arsenal aka fara samun takun saka tsakanin mai koyarwar da kuma dan wasan kungiyar, Mesut Ozil, wanda ya lashe kofin duniya da kasar Jamus a shekara ta 2014

Sai dai tuni kungiyoyi suka fara zawarcin dan wasan inda a baya bayan nan kungiyar kwallon kafa ta Inter  Millan ce akan gaba a masu zawarcin dan wasan domin yakoma kasar Italiya da buga wasa.

Amma kungiyoyin Bayern Liberkusen da Fernabace ta kasar Turkiyya tuni suka kagu wajen ganin dan wasan yakoma kungiyoyin nasu, ko a baya bayan nan ma sai da shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta inter millan ya bayyana aniyarsa ta daukar dan wasan dan kasar jamus.

Amma rahotanni sun bayyana cewa dan wasan yafison yacigaba da buga wasanninsa a gasar firimiya ta kasar ingila ko kuma gasar laliga ta sifen duk da cewa a baya yabuga a kungiyar kwallon kafa ta real Madrid.

An ruwaito cewa dan wasan yafi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester united sai dai abune mai wahala a wannan yanayin kungiyar ta iya siyan dan wasan saboda tanada manyan ‘yan wasa musamman a gaba

Dan wasan har ila yau yanada sha’awar buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sai dai an bayyana cewa Barcelona zasu nemeshi ne indai har suka kasa samun nasarar cigaba da rike Dembele.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: