Connect with us

SHARHI

Shin Ko Yaki Da Cin-hanci Zai  Ci Gaba A Shekara Ta 2019

Published

on

A shekara ta 2015, al’ummar Nijeriya sun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya jagoranci kasar nan tare da cikakken fatan ya kawo karshen fargabar da ake da ita ta rashin tabbas a kan rayuwa da kare dukiya da kuma yaki da cin-hanci da karbar rashawa. Yanzu haka ana gab da sake irin wannan zabe wanda a baya aka zabi Muhammadu Buhari, sai dai a wannan karon ba a sani ko ‘yan Nijeriyan za su sake zabar Burain ko kuma za su zabi tsohon mataiakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ko kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da suka fito daga cikin jam’iyyu hamsin din da Hukumar zabe mai zaman kanta ta yi wa rajista ba.

A sheakara ta 2016, Asusun Tallafi Na MacArthur ya bayar da gudummowa wajen kaddamar da hanyoyin da za a yaki cin-hanci a Nijeriya, kamar zargin da ake yin a badakalar kudin sayar Kamfanin Samar da wutar lantarki a shekara ta 2013. A shekara ta 2015, shekarar da aka zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari aka sa hannu a dokar hukunta masu satar dukiyar kasa, haka kuma duk a cikin wannan shekarar ce aka kaddamar da shirin ciyar da daliban makarantun firamare.

Haka kuma akwai kungiyoyi masu yawa da ke taimaka wa Nijerya wajen ganin ta yaki cin-hanci da rashawa. Akwai hukumomi da kungiyo da malaman addini da malaman makarantu da ‘yan jarida da ke taimaka wa gwamnati wajen cim ma wannan manufa tata ta yaki da cin-hanci da karbar rashawa a dukkan fadin kasar.

Duk da dimbin kalubalen da ke tattare da wannan kokari na gwamnatin za a iya bugar kirji a ce gwamnatin ta samu nasara daidai gwargwado. Saboda haka akwai bukatar a kara kaimi wajen ci gaba da wannan yaki. Domin ta haka ne kawai wata rana za a wayi gari a kawo karshen cin-hanci da karbar rasahawa a wannan kasa baki daya. Shekara biyar da suka wuce, an gurfanar da mutane da yawa da ake zarginsu da laifin cin-hanci sannan kuma wasu na tsare bisa irin wannan tuhuma ta cin-hanci da ake yi musu. Sannan kuma a tsawon wadannan shekaru an kafa kotuna na musamman da suke taimaka wa wajen gaggauta hukunta hukunta wadanda aka kama da laifin karbar cin-hanci.

An samu nasarar karbo miliyoyin Dala da biliyoyin Naira da aka sace daga kasashen waje, haka kuma an bankado asirin ma’aikatan boge wadanda ake karbar kudaden albashi masu yawa da sunansu, wanda kuma aka dakatar da ci gaba da wannan mummunar dabi’u ta sace kudaden al’ummar kasa.

‘Yan jarida su ma a na su bangaren sun taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da bincike tare da fallasa dukkan wata kumbiya-kumbiya,wanda ake amfani wadannan rahotanni domin bin sawun masu laifi, sannan a bukaci gwamnati ta hukunta wadanda suka tabbata masu laifi. Bisa irin wannan binciken nema aka fito da bayani da ke nuni da cewa, wajibi ne gwamnati ta kara sa ido kan yadda ake jihohi kudaden taimako a kan harkar ilimi da kuma yadda ake kasha wadannan kudade. Haka kuma irin wannan bincike ya nuna tsananin bukatar da ake da ita na cewa, wajibi ne gwamnati ta kara sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin wutar lantarki a kasar nan. Haka kuma an kara samun jihohi goma sha biyar da suka hannu a dokar hukunta masu satar dukiyar jama’a  a bana da jihohi takwas da ke da wannan doka a shekara ta 2016. Wannan doka ta samar da sauki kan yadda za abinciki masu manyan laifukan da suka hada da cin-hanci tare da yi musu hukunci.

Duk da haka akwai bukatar gwamnati ta kara kaimi, domin yawan wadanda ake kama wa ya fi wadanda ake yi musu hukunci. Sannan kuma akwai wadanda ke zargin gwamnatin Buhari da saka siyasa a wajen gudanar da binciken masu laifi da kuma kama wadanda suke adawa da gwamnatin sannan suna kawar da kai ga masu laifin da ke cikin gwamnati ko kuma jam’iyya mai mulki. Saboda haka wannan babban kalubale ne da ake fuskanta, musammam a kan yaki da ci-hanci, wanda kuma dole sai kara ba da himma da kawar da son kai. Fatan al’ummar kasa dai shi ne, a samu nasanar wannan yaki da ake da wannan mummunan hali.

Iyayen yara da malaman makaranta da jami’an kananan hukumomi kalilan ne suka san yawan kudaden tallafin da ake ba Hukumar kula da ilimin bai-daya da makudan kudadaen da ake ware wa a kan shirin ciyar da daliban makarantun firamare. Saboda haka a nan ma akwai bukatar ‘yan jarida su kara kaimi wajen fito da irin wadannan bayanai, domin al’umma su san halin da ake ciki.

Hka kuma akwai badakala mai tarin yawa a bangaren shari’a wanda shi ma yana bukatar mafarauta labaran su kara bayar da gudummowa domin bankado dukkan  wata badakala da ta shafi wannan fannin.

A ‘yan sheakaru kadan da suka wuce ne, al’ummar Nijeriya suka damu da yaki da cin-hanci, kuma suka yi imani cewa za a iya kawar da wannan mummunar dabi’a. ‘Yan nijeriya sun dade suna tunanin cewa, idan aka kawo karshen cin-hanci wane irin gagarumun ci gaba za asamu a wannan kasa. Saboda haka idan ana bukatar wannan ci gaba, sai an tabbatar da samun gaskiya cikin al’umma. Hakan zai bayar da dama wajen kawar da kai daga dukiyar al’umma. Baya ga wannan samar da guraben ayyukan yi musamman ga matasa shi ma zai taimaka wajen yaki da cin-hanci a wannan kasa. Haka kuma idan aka kara bunkasa hukumomin kula da yaki da cin-hanci da rashawa, sannan kuma ya zama ana sa ido a dukkan ma’aikatun gwamnati da kuma masu zaman kansu.

Dukkanin wadannan hanyoyi an yi amfani da su musamman a tsawon wannan muliki na shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan kuma ana iya cewa, an samu nasara daidai gwargwado duk da yake dai ana zargin wadansu gungun mutane da yi wa wannan yunkuri zagon-kasa.

Ganin yadda wannan kokari na gwamnati ya sauya yadda al’amura ke guna dangane satar dukiyar al’ummar kasa, kamar kirkiro da tsarin ajiya na “STA” ya sa al’ummar ke da fatan dora wa a kan ire-iren wadannan tsare-tsare ga duk wanda ya samu nasarar zama shugaban kasa a zabe mai zuwa.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!