Connect with us

RA'AYINMU

Bankwana Da 2018 Da Maraba Da 2019

Published

on

Shekara kwana, in ji masu iya magana. Ga mai yawan rai yanzu dai shekara ta 2018 ta kare daga ranar Talatar nan, sannan kuma za mu shiga shekara ta 2019. Tabbas shekara ta 2018 ta zo da abubuwa masu yawa, wadanda su ka hada da na farin ciki da kuma na bakin ciki, sannan akwai na ban mamaki da na ban dariya, baya ga na fargaba da ban takaici, hakazalika akwai na dadi ma duka da su ka faru a 2018 mai karewa.

Amma babban abinda za a iya cewa ya fi jan hankali a shekarar shi ne, gabatowar siyasar babban zaben kasa wanda za a gudanar a 2019 a Najeriya, inda za a zabi yawancin mukaman sisayar kasar, wadanda za su ja ragamar mulkin kasar zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Siyasar ta fara ne da ta cikin gida, inda rikice-rikice su ka dabaibaye manyan jam’iyyun kasar kan fitar da ’yan takara. Hakian ya janyo ficewar wasu daga cikin jam’iyyun da su ke ciki, wasu kuma su ka rika yin tururuwa su na koma wa wasu jam’iyyun. A lokacin da a ke fama ire-iren wadannan rikice-rikice a cikin jam’iyyun abin ya yi kama da wani al’amari wanda kamar ba zai wuce ba, saboda yadda a ke ta faman mayar da yawu da rigingimu.

To, amma daga ranar da a ka tunkari batun tsayar da dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta kasa, sai kallo ya koma sama, musamman ma da ’yan jam’iyyar su ka tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Za a iya cewa, lamarin ya karfafi ’yan adawar kasar, domin gani a ke yi kamar zai iya tika shugaban kasa mai ci kuma dan takarar jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari, da kasa.

Ita dai APC ba ta samu rikicin tsayar da dan takarar shugaban kasa ba kusan ko kadan, domin ba a samu masu hamayyar neman kujerar da Buhari a cikin gida ba. Don haka za a iya cewa, a tsanake ya samu takarar APC.

Daga lokacin da PDP ta tsayar da Atiku Abubakar sai cacar-baki ta balle tsakanin tawagar yakin neman zabensa da ta yakin neman zaben Muhammadu Buhari, inda a ka shiga zargin juna da sukar juna da kuma kokarin haskaka gazawar kowannensu. Haka lamarin ya cigaba da kasancewa har shekarar ta 2018 ta kare.

Amma abinda ya fi bada mamaki shi ne, lokacin da a ka tsayar da Atiku an yi ta tsammanin cewa, zai fito da kudi mai yawa ya sayi ra’ayin jama’ar kasar, to amma kawo yanzu ba a ga hakan ba. A takaice ma dai za a iya cewa, bangaren yakin neman zaben Buhari sun fi nasa bangaren fitar da kudada ta hanyoyi daban-daban, musamman idan a ka yi la’akari da yawaita ziyarce-ziyace da rabon kudade da a ke ganin a yi a fadar ta shugaban kasar.

Wasu na ganin hakan ba zai rasa nasaba da rashin kwarin gwiwar ’yan adawar kasar ba kan ko za su iya lashe zaben ma kuwa ko kuwa a’a. Don haka tawagar Atiku ta ki yarda ta saki kudi, don gudun kada a yi ma sa sakiyar da babu ruwa, musamman ma don ganin yadda a ke ta faman wayar da kan mutane a kan su amshe kudin ’yan takarar da ke ba su kudi, amma su zabi abinda ya fi dacewa ko kuma nagari. Wasu kuma na ganin a’a, kawai wata sabuwar dabara ce, wacce bangaren Atikun su ka fito da ita da nufin sai dab da zaben, sannan su fito da makudan kudin da za su ruda bangaren gwamnati.

To, ko ma dai mene ne daga dukkan alamu yanayin da a ka bar 2018, a cikinsa za a fara 2019, domin duka batun na babban zaben kasar ne. Babban abinda za a fi tunkara yanzu a 2019 shi ne zagayen yakin neman zabe zuwa jihohi da ’yan takarar jam’iyyun za su cigaba da yi daga na har zuwa lokacin da za a yi babban zaben a cikin watan Fabrairu mai zuwa da yardar Allah.

Babbar addu’armu ita ce, a yi zabe lafiya a gama lafiya cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da an kashe ko dan kwaro ba! To, amin summa amin!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!