Connect with us

RAHOTANNI

NHRC Ta Yi Tir Da Yadda ’Yan Sanda Su Ka Garkame Gidan Dino Melaye

Published

on

Hukumar kare hakkin bil-adama ta (NHRC) ta yi Allah wadai da matakan da ‘yan sanda suka dauka na kakaba shingaye a gidan Sanata Dino Melaye gami da kira ga shugaban ‘yan sandan Nijeriya da ya gaggauta bayar da umurni ga jami’ansa su kauce daga gidan na Dino.

Babban sakataren NHRC Tony Ojukwu shine ya shaida hakan a cikin sanarwar da ya rabar wa ‘yan jarida a Abuja, ya shaida cewar matakan da ‘yan sanda suka dauka na kame Dino Melaye ya keta masa ‘yancinsa.

Sanarwar ta ce; “Shi Sanata Melaye shi daya ne yake da alhakin amfani da gidansa? Ina aka amance da iyalansa da sauran jama’a, sannan ya aka mance da makwaftansa? Sai bai kamata a ce an kulle gidansa babu shiga babu fita domin hakan ya taba walwalar iyalansa da sauran jama’a,” in ji sanarwar

Hukumar ta shaida cewar a fayyace yake, ‘yan sanda suka da alhakin gayyatar kowani mutum domin yi masa tambayoyin da suke da su, amma sam bai kamata su gargame masa gida da barazanar tauye masa hakki ba.

NHRC ta ce, sam ba fa zasu lamunci dukkanin wani yanayin da bai dace ba daga bangarorin jami’an tsaro gabanin babban zaben 2019.

Dino Melaye dai ya mika kansa ga ‘yan sanda bayan rasa na yi biyo bayan jifge jami’an ‘yan sanda a gidansa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!