Connect with us

ADABI

Tonon Sililin Mr. Hampher Jakadan Turai A Musulunci

Published

on

Daga karshe dai na riski Basra bayan na shafe tafiya mai tsananin wahalarwa, sannan kai tsaye na nufi gidan ubangidana Abdur-Rida domin na sauka.

Da zuwana sai na tarar da shi a waje yana bacci, bayan ya tashi ne ya cika da murnar dawowa ta, hakika ya tarbeni da girmamawa.

Kashe gari ne yake faɗa mini cewar Muhammad Najd yazo nemana bai riske niba, amma ya bar takadda gareni.

Dana duba takardar sai na samu adireshin sabon wurin daya koma da zama ne aciki, don haka babu wani ɓata lokaci sai nayi shiri na nufi gareshi.

Na samu Muhammad Najd a gida har yayi aure, amma fa duk ya rame, ban kuma tambayeshi dalilin hakan ba sai daga baya, sannan kuma muka yi shawara dashi cewar ya sanar da mutanen garinsu cewar ni bawansa ne daya dawo daga wani wuri daya aikeni.

Na zauna tare dashi tsawon shekaru biyu, inda ya rinka tara mabiya sannu a hankali tun daga shekarar 1143 hijiriyya (1730 miladiyya), ya zamana mutane sun fara taruwa gareshi, nikuma ina samar musu da kuɗaɗen da suke da bukata.

Haka kuma aduk sa’ar da makiyan abinda yake yaɗawa sukayi nufin cutar dashi, nine ke yin ruwa da tsaki don sasantawa.

A wasu lokutan yakanji tamkar ya watsar da wannan kira da yakeyi, musamman dube da yadda wasu mutanen keyin raddi gareshi, amma da yake kullum ina tare dashi, sai na zamo mai karfafa masa guiwar akan cigaba da abinda yasa a gaba.

Na kance masa ya Muhammad, Annabi yasha haɗuwa da irin waɗannan kalubalen, don haka tilas kaima ka jure musu.

Daga nan sai nayi hayar wasu mutane masu yin leken asiri suna sanar mini da duk wani kulli da aka shirya ga Muhammad Najd.

Rannan kwatsam sai suke sanar mini cewar an shirya kisan Muhammad, sai kuwa na tashi tsaye domin ganin na kange shi daga sharrin makiyan nasa.

Haka kuma koda ɗaliban Muhammad sukaji abinda aka kulla ga malaminsu, sai adawa ta kullu tsakaninsu da masu wannan yunkuri.

Muhammad Najd yayi mini alkawarin aiwatar da dukkan muradun hukumar mu ɗaya bayan ɗaya gwargwadon iko, amma da sharaɗin ba lokaci ɗaya ba.

Ya lura da cewar umarni da rushe Ka’aba abune mai wuya, don haka sai ya wofantar da zancen ta, haka kuma yaki samar da kwafin jabun fassarar Alkurani mai girma, domin yana tsoron Sharifai na Makkah da kuma gwamnatin Istambul.

Ya sanar mini da cewa da zarar yayi waɗannan abubuwa, sojojin musulunci zasu kawo masa farmaki a duk inda yake.

Bayan wasu shekaru ne sai hukumar mu tayi nasarar karkatar da wani Muhammad ɗin mai suna Muhammad bin Su’ud sarkin Der’iyya izuwa bukatar mu.

Suka aiko min da haka tare da bukatar na samar da alaka a tsakankanin Muhammadan guda biyu.

A hankali kuwa sai muka soma yin karfi, muka koma birnin Der’iyya da zama tare da mayar dashi cibiyar mu, muka sanyawa wannan sabon addini da muke riritawa suna ‘Wahabiyya’, ita kuma hukumar mu ta rinka aike mana da duk ababen da muke da bukata.

An bamu taimako ta fannin soja, sannan an kawo mana wasu wakilai a matsayin bayi daga Burtaniya su goma sha ɗaya waɗanda sukayi ilimi na addinin musulunci.

Tare da waɗannan mutane muka rinka ɗora Muhammad Najd da Muhammad Su’ud a kan duk wata turbar da mukeso.

Haka kuma mun kulla auratayya tsakanin mu da kabilun wannan yanki, ya zamana mun samar da gagarumar alaka da kabilun su.

Daga nan sai muka shiga murna cewar da sannu layar mu zatayi kyawun rufi matsawar wani abu bai faɗo garemu na bagatatan ba..

 

Kammalawa

Wannan shine karshen abinda Mallam Hampher ya rubuta a tonon sililinsa, sai dai daga baya ‘yan uwansa turawa sun rinka gwama numfashi suna sukar rubutun a matsayin kirkirarren labari wanda sukace mabiya sunnah ne suka samar dashi domin haɗa kawunan mabiyansu.

Sai dai irin wannan tonon sililin da wani bafaranshe yayi mai suna Marcelle Perneau da taken ‘Notes on My Trabel to India’ ya tabbatar da ayyukan gwamnatin burtaniya wajen kokarin kwashe arzikin kasar da kuma kawo karshen musulunci da musulmai a duniya, abinda wani malami a kasar ta Indiya mai suna ‘Allama Muhammad Fadli Hakk Khair abadi’ ya sake tabbatarwa a littafinsa mai suna ‘The Indian Rebolution’.

Haka ma wasu malaman addinin Islama irinsu Ayatullah Hussein-Ali Montazari sun gaskata wannan rubutu na Hampher, sannan kuma wani malami mai suna Ayyub Sabri Pasha ya gaskata shi a littafinsa mai taken ‘The Beginning and Spread of Wahhabism’ wanda ya wallafa a shekarar 1890.

Da fatan Allah ya bamu dacewa Amin.

Sadik Tukur Gwarzo

Karshe!

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!