Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Za A Yi Wake Da Shinkafa A Siyasar Jihar Kebbi

Published

on

Bisa ga dukkan alamu dai siyasar bana ta dauko sabon salo wanda ke nuna za a yi shinkafa da wake wajen zaben yantakara a matakan mukaman siyasa dabam-dabam.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a jihar Kebbi ya nuna cewa duk da wake a ke jam’iyyar APC daya ce amma dai akwai rarrabuwar kawuna wanda ya zamo asali tun wajen zaben fidda gwani don  tsayar da yantakara da aka gudanar watan Oktoba na shekarar  2018 da ta gabata wanda mutane da yawa musamman yan jam’iyya suna cikin jam’iyya amma dai saboda suna ganin ba a yi musu adalci wajen tsayar da yantakara ba su kuma sun sha alwashin ba za su zabi yantakarar da aka tursasa musu ba saboda haka za su yi gaban kansu lokacin zabe duk da ya ke gwamnatin Sanata Atiku ta sha nada kwamitoci domin sasantawa tsakanin yan jam’iyya amma a koda yaushe akan tashi baram-baram tsakanin bangarorin.

Wani dan jam’iyyar ta APC wanda ya ce kada a bayyana sunan sa ya ce su matsalar su da gwamna Atiku ita ce tun lokacin da ya ci zabe sai ya kawar da kan sa ya kuma jiya wa kowa baya sai wadansu yan tsirarru daga cikin yan jam’iyya sai kuma yan gidan su sai kuma babban yaron sa Faruku PA wanda aka fi sani da Enabo wanda a wani kauli ma ganin sa ma ya fi ganin gwamna saboda shi ne ke rike da dukkan madafun iko kuma shi ke rabon kwangiloli da mukamai da kuma motoci da kudi.

Alhaji Aliyu Abdullahi Hard game shi ne Shugaban jam’iyyar APC ta karamar hukumar mulki ta Argungu ya kuma bayyanawa wakilinmu da cewa shi a wajen sa duk yayan APC daya ne saidai wanda ya barrantar da kan sa, wannan matsalar ta soma kamari ne bayan an kammala congress na jam’iyya wanda sau da yawa idan muka kira taro sai wadansu su ki zuwa sai su rinka kawo wani uzuri wanda ya ce ya ta’allaka wannan matsalar ga jiga-jigan siyasar saboda suna kallon yaran su suna neman raba kan yan jam’iyya amma sun ki jan hankali su don cigaban jam’iyya.

Baby a kuma yi kira ga yan siyasa da su baiwa Gwamna Atiku goyonbaya su cigaba da hakuri saboda wannan gwamnati ba irin gwamnatocin da suka shude ba ne da suka yi wadaka da kudi suka yi ta rabon kwangiloli ba.

Alhaji Salihu Ahmed KC tsohon Shugaban karamar hukumar mulki ta Argungu kuma na hannun daman gwamna Atiku ya bayyanawa wakilinmu da cewa wannan matsalar ta samo asali ne tun lokacin tantance yantakara a watan Oktoban shekarar da ta gabata a sanadiyyar samun bambancin ra’ayi kuma sai shugabanni suka kasa zaunawa don warware wannan matsalar amma dai Alhamdu Lillahi yanzu haka dai an dauko tafarkin dinke wannan barakar ta hanyar kiran duk wani jigo da ke da ruwa da tsaki a jam’iyyar APC don a gaya wa kowa gaskiyar sa ko kuma akasin haka kuma a baiwa kowa hakuri  wanda ana sa ran idan an aiwatar da haka ana sa ran cimma nasara.

A daya bangaren kuma wani jigo daga cikin matasan jam’iyyar PDP a jihar Kebbi Alhaji Yahaya Danjada ya bayyanawa wakilinmu da cewa su kam a jam’iyyar PDP ba su da gefe kowane dantakara na su ne kuma yanzu haka sun dukufa wajen yakin neman zabe.

Ya kuma ce ba maganar shinkafa da wake ba ne a wajen su ba su kokarin su kwace kujerin daga APC su ke yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!