Connect with us

RAHOTANNI

Zoro Ga Osinbajo: Yakamata Ka Ziyarci ’Yan Gudun Hijirar Arewa Maso Gabas

Published

on

A cikin wani sakon jan hankali, a lokacin zuwan sa a birnin Maiduguri, dan majalisar wakilai a tarayyar Nijeriya, Sani Zoro ya bayyana matukar damuwar sa dangane da yadda rikicin Boko Haram ya tagayyara rayuwar jama’ar Borno- musamman yadda hare-hare suka yi kamarin a arewacin jihar, a yan kwanakin nan.

Bugu da kari kuma, Zoro ya ankarar da cewa akwai bukatar mataimakin shugaban kasa ya tashi takanas ta Kano, zuwa yankin, domin ganin hakikanin halin da jama’ar ke ciki, tare da daukar matakin fadada ayyukan jinkai ga yan hijira wadanda ke bukatar tallafi na musamman dangane da yanayin da suka tsinci kan su a ciki.

Ya ce, “yau uku ga watan daya (3/01) na shekarar 2019, wanda a hukumance an tantance karin wasu sabbin daidaikun yan gudun hijira sama da 12, 000 tare da magidanta 3,500 a nan jihar Borno. Har wa yau kuma, adadin yan hijirar kara yawa yake yi, a cikin karancin abubuwan bukatar yau da kullum”.

“Sannan wani babban abin tausayi da tashin hankali shi ne yadda tsuffi- maza da mata, sai tagayyara suke yi (suna faduwa suna tashi, wasu kafafun su a kumbure-suntum), ta dalilin dogon tafiyar kafa; tun daga garuruwan Baga, Doron Baga da Gudumbali, wannan rashin imani har ina.

“A gefe guda kuma, wata babbar matsala ita ce yadda matasa sabbin jini tare da kananan yara ke bin tituna da kwararo-kwararo, maza da mata, suna Allah shi baku mu samu. Wanda kuma wannan rikici na Boko Haram ne ya jefa su a cikin wannan mummunan yanayi na ni’su”.

“Kuma bukatar wadannan jama’a da ke zaune a sansanin gudun hijira bata takaitu ga abin da zasu kai a bakin salati ba (abinci) kawai, suna da karin wasu bukatu da suka hada har da bargunan rufa, don rage kaifin radadin wannan hunturu. Sauran bukatun kuma su kunshi dakunan kwana, shimfidu, kayan girki da tsabtatun ruwan sha da suran kayan masarufi”. Ya nanata.

Alhaji Sani Zoro ya sake bayyana cewa, akwai bukatar daukar dokar-ta-baci wajen bin bahasin lamarin, wanda hakan zai bayar da damar daukar matakin gaggawa ga mutanen da lamarin ya shafa.

Haka kuma, ya ankarar da mataimakin shugaban kasa- Farfesa Yemi Osinbajo da cewa ya zama dole ya kai ziyara ta musammam a jihar Borno, tare da rakiyar shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa (NEMA), da kwamitin shugaban kasa dangane da farfado da arewa maso-gabas (PCNI).

“Wanda hakan zai bashi dama wajen gano abubuwa da dama, dangane da matakin jinkan da ya kamata ya dauka a tattare da wadannan jama’a wadanda ke zaune a sansanin gudun hijira a arewa maso-gabas.”

                                                                               
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!