Connect with us

RAHOTANNI

Yaki Da Boko Haram: Shekaru 6 Gwamna Shettima Na Dauke Da ‘Civilian JTF’

Published

on

A kokarin sa wajen bayar da gudumawa ga jami’an tsaro masu yaki da matsalar tsaron Boko Haram a arewa maso-gabas, gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana yadda ya kirkiro yan sa-kan kato-da-gora (Civilian JTF) tare da daukar nauyin basu boron dabarun yadda za su fuskanci matsalar tsaro a jihar, kana da samar musu abubuwan da suke da bukata; cikin shekaru shida (6) da suka gabata.
Gwamnatin Shettima ta kirkiro yan sa-kai a shekarar 2013, wadanda kuma suka bayar da gagarumar gudumawa a bangarori daban-daban a jihar, musamman wajen ganowa tare da cafke wasu da dama da ake zargin su da kasancewa mambobin kungiyar, kana da taimakon jami’an tsaron da ke filin daga.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin mai taimaka wa Gwamna Kashim Shettima, ta fuskar sadarwa da dabarun yada labarai, Malam Isa Gusau, a cikin tattaunawa dashi ta kai-tsaye, a matsayin babban bako a shirin “The Morning Show”, wanda aka watsa a tashar TV (DSTV) da ke Ikoyi ta jihar Legas, ranar Asabar.
Malam Isa Gusau ya bayyana cewa duk da yadda wasu yan siyasa ke ta kokari wajen amfani da kalaman maras tushe wajen dakushe karfin gudumawar sa a yaki da matsalar tsaron Boko Haram, bai hana lamarin ya fito balo-balo ba, wanda Gwamna Alhaji Kashim Shettima- a 2013 zuwa yau, shi ne yake dauke da nauyin daruruwan yan sa-kan ‘Civilian JTF’ ta hanyar kudi da duk bukatun su, wanda hakan ya kawo dimbin nasarori da ci gaba a yaki da matsalar tsaron Boko Haram, a wannan yankin, wanda suka kunshi sama da matasa sama da 20,000 na yan sa-kan kato-da-goran.
A hannu guda kuma, ya nanata cewa, wannan gudumawa wadda Shettima ya bayar a sha’anin yaki da Boko Haram, ta samu cikakken goyon baya tare da jinjina daga rundunar sojan Nijeriya da sauran bangarorin masu ruwa da tsakin a fannin tsaron kasar nan- tsuffi da wadanda suke a nan, wanda hatta al’ummar jihar Borno sun ji dadin wannan mataki.
Har wala yau kuma, Gusau ya yi mamaki dangane da har yanzu wasu ke ci gaba da yin kunnen-kashi da cewa, “duk da yadda duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara; saboda haka ne masu irin wadannan surutai maras kan-gado, suna iya yin su wajen kushe kokari da gudumawar da Gwamna Kashim ya bayar, a yaki da matsalar tsaron Boko Haram, kana da wanda suka yi tayi dangane da rawar da yan sa-kai ke ci gaba da bayarwa ta wannan haujin”.
Malam Isa Gusau, ya ce, “sannan kuma da gangan wadannan gungu na mutane ke kawar da kan su dangane da gaskiyar abinda ke wakana- a cikin shekara shida, wanda a ciki Gwamna Shettima ya rinka bayar da umurnin cire makudan kudi wajen sayo motoci da kayan aiki, bayar da horon musamman, kudaden alawus- alawus da sauran abubuwan bukata daban-daban ga wadannan gwarazan yan sa-kai na Civilian JTF- kimanin 20,000, domin yaki da matsalar tsaron Boko Haram”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!