Connect with us

KASUWANCI

Ambaliyar Ruwa Da Rikicin Makiyaya Da Manoma Barazana Ne Ga Noma – Gwamnatin Tarayya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar, rikicin makiyaya da manoma da yaki ci yaki cinyewa a wasu sassan kasar nan, da kuma yawan aukuwar annobar ambaliyar ruwan sama suna yiwa yin noma barazana a kasar nan. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Mista Udo Udoma ne ya sanar da hakan a lokacin gabatar da kundin kasafin kudi na 2019. Ministan ya ce,hakannya janyo an samu kashi 1.19 bisa dari kacal a fannin. A cikin zangon shekarar ta biyu da zango na uku, ya sha ban-ban dana karuwa kashi uku bisa dari na farkon shekarar. An samu annobar ta ambaliyar ruwan a cikin Yuni zuwa Okutoba 2018, inda ambaliyar ta yi mummunan barna a gonakai da kuma a kan dabbobin dake jihohin Abia, Kebbi, Cross Riber da kuma Jigawa. Wakilin mu ya ruwaito cewar, rikice-rikicn na makiyan da manoma da kuma nnobar ta ambaliyar ruwan ta shafi amfanin gona, da za’a iya fitar dasu kasar waje kamar tobacco, Rogo, Man iri, Kayan lambu, da saurannsu da zasu iya samarwa da gwamnatin tarayya kudin shiga. Rikice-rikicennna makiya da manoma musamman a yankin Arewa ta tsakiya ya janyo raguwar samun amfanin gona a kasar nan. Shugaban kungiyar masu fitar da amfanin gona zuwa kasar waje dake reshen cibiyar baje kolin kasuwanci,masana’antu reshen jihar Legas Mista Bamidele Ayemibo ne ya sanar da hakan a lokacin da yake yin jawabinn sa a wani taro da kungiyar ta gudanar a jihar Legas. Shi kuwa Darakta Janar na cibiyar Mista Muda Yusuf, ya dora laifinnne a kknnNijeriya saboda kinnrungumar yin noma na zamani, inda ya yi nuni da cewar, hakan ne kawai zai kawo karshen kalubalen da ake fuskanta a fannin. Darakta Janar ya sanar da hakan ne a hirar da wakilin mu a ranar Juma’ar data gabata. Acewar Yusuf har yanzu a Nijeriya ana yin noman gargajiya, inda ya ce, akwai bukatar a rungumi yin noman zamani. Ya yi nuni da cewar, hakan ne yake janyo ake samun amfanin gona maras yawa a kasar nan idan aka kwatantata da yadda ake samun amfanin gona mai yawa. Ya bayyana cewar, akwai bukatar gwamnati ta samar da zai kyakyawan tsari da zai kare gonakan manoman kasar nan da kuma samar da kayan aikin gina na zamani, magunguna feshe da kuma ingantaccen irin noma. Ya sanar da cewar, wadannan kayan suna da tsada kwarai, musamman ga kananan manoman dake kasar nan. A karshe Yusuf ya yi nuni da cewar, samar da kudi shima yana zamowa barazana ganin cewar bankunan manoma dake kasar nan basa yin aikin su yadda ya kamata akwai kuma bukatar ayi wa bankunan garanbawul kuma gwamnatin ta samar da wadatattun hanyoyi, wadataciyar wutar lantarki, ruwa musamman don a rage kwararowar mazauna cikin karkara zuwa cikin birane musamman matasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!