Connect with us

MAKALAR YAU

Falsafar Kyau!

Published

on

A Falsafa idan ana maganar kyau (aesthetics) ba ana magana akan iya kyan da zaka gani da ido bane. Ana magana akan duk wani abu da jinsa ko ganinsa zai sanya kaji dadi a ranka. Tare da cewa da larabci ana kiran ilimin kyau a falsafa (Aesthetics) da “ilmul Jamal” amma masana tarjama sun bayyana cewa mafi kyawun fassarar da ya dace a kira ilimin da shi shi ne “Dayyibat”.
Kalmar “Dayyibat” ta hade duk wani abu da idan ka gani ko kaji zai dadada maka rai. Ta hada da “jamal”, “husn”, “ziyna” da sauran kalmomi makamanta haka. Tun asali kalmar “aesthetics” tana da asali daga kalmar Greeks dake nufin “sensuous” wato abin ji ta hanyoyin ji (kamar ido, kunne, fata, harshe da hanci) da zai kai sako gun kwakwalwarka don ka samu wani yanayi a jikinka.
Wani abu da Allah ya bayar da misali a cikin kyawawan abubuwa (dayyibat) shi ne mace a lokacin da yake maganar yin aure (fankihu ma daba lakum minan nisa’i). Mace gaba dayanta kyakkyawa ce kuma kayan ado ce. Daga muryarta zuwa siffarta har zuwa motsin jikinta. Kallon mace kawai a gurin namiji yana sanya dadin rai. Wannan yana daga dalilin da yasa Allah ya lissafa kayan kawa na duniya sai ya saka mata da gwala-gwalai a ciki (Zuyyina linnas…). Sai dai yana da kyau a gane cewa kyau a idon mai ganinsa yake (subjectibe) don haka Allah yace abin da ya dadada muku (ma daba lakum). Ta iya yiwuwa kana ganin komai na matarka ko budurwarka kyakkyawa ne amma wani shi ba ya gani.
Daga abubuwan da Abu Hamidil Gazzhali ya sanya a cikin kyawawan abubuwa a mashahurin littafinsa na “Ihya’u Ulumudden” akwai jin sauti mai dadi da ya kira “samaa” a yaren sufanci. A gurin sufaye kowane kyau da kake gani to tajallin Ubangiji ne a cikinsa (Tajalliyat Jamalillah) don haka sauraron duk wani abu mai dadi kan iya sanya tunanin Allah da ambatonsa. Wannan ta sanya a darikar Maulawiyya ta Jalaludden Rumi jin sauti mai dadi na daga hanyoyin da yake sanya “whirling derbish” suke shiga “jazba”. A gurin sufaye, ma’anar hadisin cewa Allah kyakkyawane kuma yana son abu kyakkyawa (Innallah Jamilun) ya wuce ganin ido kawai, ya hada da duk wani abu da zai sanya jin dadin rai musamman idan muka hada da hadisin da yake cewa “Innalaha ta’ala dayyibun”. Kalmar “dayyib” tana nufin duk abin da zai sanya jin dadi a rai.
A gurin Plato da sauran tsofaffin masana falsafar da aka yi a zamanin Greeks, kyau ya hada da duk wani abu da kake yi kuma kake jin dadinsa. Lokacin da kake lissafin “geometry” kuma samo amsar dogon bayanin “calculus” ya sanya jin dadi a ranka to hakan ya mayar da “Mathematics” a cikin kyawawan abubuwa. Haka mai binciken Kimiyya da sauransu. Don haka irin su Ibn Sina, Alkindy da Ibn Rushd suke ganin hatta falsafar da suke yi tana daga cikin ibadar Allah domin tana daga cikin tajallin kyawun Ubangiji na abin da suke ganowa na tsarin tafiyar halittunsa ta hanyar izina (contemplation). Shi kam Gazzhali da sauran malamansa kamar Bakillany da Imamul Haramain suna ganin duba sararin subhana (cosmos) don gano yadda za’a dabbaka hujjar “Argument from Design” na samuwar Ubangiji ta fuskar “Ilmul Kalam” shi ma hanyar ibada ne da jin dadi.
Kyau bai tsaya iya nan ba domin akwai maganar zane-zane (fine art) da wakokin zube (poetry) da kuma gone-gine (architecture) kai har da ado na gumaka (statue). A cikin Alkur’ani Allah ya bamu labarin cewa a gidan Annabi Sulaiman (as) akwai gumakan ado wanda ba bauta musu ake ba. A cikin abin da Zahabi a littafinsa na “Tarikhul Islam” daga gurin Azrakiy a littafinsa na “Tarikhu Makka” har a Ka’aba akwai zane-zanen (gumaka, a wata riwayar) da Annabi (saw) bai ce a rushesu ba saboda ba bauta musu za’a yi ba. Zanen Annabi Isa da mahaifiyarsa yana ka’aba har sai bayan da Yazid bn Mu’awiya ya harbowa Abdullah bn Zubair majaujawa ya rushe ka’abar sannan ba’a mayar da su ba daga baya.
Musulinci bai haramta duk wani abu kyakkyawa ba. Sai dai ana iya killace iya ina za’a iya amfani da shi. Misali, kyawun mace ba zai sanya wanda ba mijinta ba ya dinga zuwa ganinta yana jin dadi. Dadin kida (music) bai halatta cewa mutum ya dinga jin wakokin batsa ba. Dadin ganin zane-zane ko gunkin ado (statue) bai halatta mutum ya koma bautar zanen ko “statue” din ba. Masu haramta dadadan abubuwa da masu guluwwi wajen amfani dasu duk sun yi kuskure. Abin da ake dubawa shi ne tsaka-tsaki a kowane lokaci.
Tashoshin Wa’azi
Ina sauraron wannan mashahurin makadin wato Ludwig Ban Beethoben a cikin kidansa na “Egmont, Op. 84 : Oberture” da irin yadda kidan, ba tare da ko waka ba, yake ratsa zuciya kuma ya sanya motsin “dopamine” a cikin kwakwalwa. Masana kimiyya sun tabbatar da cewa jin kida (classical music) yana taimakawa wajen kara farin ciki da fahimta a kwakwalwa. Yi tunanin kidan da aka sanyawa film din “Titanic” ko “Kabhi Albida” a matsayin kidan taushi! Ji sauti mai dadi da ratsa zuciya.
Daga baya sai na tuno cewa masu hayaniyar wa’azi sun dade suna wa’azi akan a dena jin kida amma har yau ba’a dena jin kida ba. Za su kuma ci gaba da haramta abin da ba zai haramtu ba. Su kansu sai sun dinga yi. Nawa ka sani sun zazzagi yan fim amma yanzu duk sabon fim sai an gani a gidansu? Suna ta kokari su haramtawa dan Adam abin da ba zai iya denawa ba ne. Jin kida yana daga cikin abubuwan da ake kira “Aesthetics” a Falsafa. Dukanmu muna son kida don haka bahaushe ya ce ko mallam ba zai ce kida ba dadi ba. Allah kam bai haramta mana jin dadi ba. Hadisan haramcin kida kuwa duka Ibn Hazam Al’andalusiy ya raunanasu a littafinsa na “Almuhalla”.
Abu Hamidil Gazzhali (rh) yana cewa duk wanda ba ya jin dadin kida to yana da matsala a hankalinsa! A cikin mashahurin littafinsa na “Ihya’u Ulumudden” ya yi babi guda da ya ware akan jin kida da ya kira “Assama’a”. Shi kam Jalaludden Rumi ya sanya a cikin darikarsa ya zama jin kida yana daga hanyoyin zikirin Allah. Wadannan su ne malamai da suka san cewa lalle kida yana da muhimmanci a rayuwarmu. Amma wadanda basu san komai na “Usulul Fikh” ba sai dai dauko litattafan hadisai suna fassarar harafi suna ruda kansu.
Hatta dabbobi suna son kida. Bincike ya nuna cewa shanun da ake tatsarsu a lokacin da aka sanya musu kida sun fi fitar da nono mai yawa. Shi kam doki da nishadin da yake a lokacin sauraren kida kowa yana gani a hawan sallah da ake a kasar Hausa. Kamfanonin sadarwa sun gane cewa dan Adam yana son kida don haka suke sanya kida a wayarka lokacin kira (ringtones), ko taken fim din da kake kallo, ko shirin labaran da kake saurare, kai har wa’azi yanzu ana sanya masa kidan taushi don kada mai saurare ya gaji.
Tashar da babu nishadi kuwa, babu wani abin jin dadi a ciki. Sai dai tsoratarwa da kafirtawa da kai mutane wuta. Kowa yana son hoto da zane mai kyau (suma suna daga “Aesthetics”) amma an ce haramun ne. Abin da ba’a so shi ake sanyawa. Ba a gane cewa har Alkur’ani da ake jin dadin saurare saboda sautinsa yana da amo mai dadi ba ne. Don haka Manzon Allah (saw) ya misalta muryar wannan sahabin da cewa karatun Alkur’aninsa yana da dadi domin tamkar an bashi murya mai kama da sarewar Annabi Dawud (as).
Dole a kori mutane daga tashoshin addini su koma kallon Zafafa Goma don a nan ake abin da yayi daidai da tsarin halittar kwakwalwar dan Adam. Ana nishadi kuma ana kallon fina-finai a can. Amma a ce kullum sai wa’azin azabar lahira da kafirta na duniya ai korar mutane ake daga saurare. Ko a gyara ko kuma wallahi sai an rasa mai kallon tashar baki daya a lokaci kadan mai zuwa, sai dai masu ita kadai su kalli abarsu.
Gyara kayanka dai bai zamo sauke mu raba ba. Zan iya karbar kowane zagi a nan daga wadanda ba sa son gaskiya a yadda take. Wasu sun fi so su haramta hoto a yayin da ake ganinsu kan gaba wajen daukar “selfie”. Wasu sun fi son fi son su yaudari kansu don ba Allah suke yaudara ba. Sun fi son su nunawa duniya abu haramun ne amma su labe a baya suna aikata abin. To ni dai ba zan zama daga cikin masu fadar abin da ba sa aikatawa ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!