Connect with us

WASANNI

Manchester United Ta Fitar Sunayen Masu Koyarwar Da Za Su Nema

Published

on

Kungiyar kwallon kafa fa Manchester United ta fitar da jerin sunayen masu horas wa guda 5 da zata zabi guda ya zama na din-din din a karshen kakar wasannan inda tuni tattaunawa tayi nisa a tsakanin shugabannin kungiyar.
Kungiyar kwallon kafan ta fitar da jerin sunayenne domin samar da mafita daga koma bayan da ta samu, daga cikin sunayen masu horas war da aka fitar har da Ole Gunnr Solskjaer wato mai horas wa na rikon kwarya na kungiyar kenan.
Solskjaer dai tunda ya karbi kungiyar ta Manchester United ya buga wasanni 5 kuma ya lashe su a jere hakan kuma tarihi ya kafa a kungiyar wanda masu horas wa da yawa basu kafashiba a kungiyar kwallon kafan.
Ga jerin masu horas war da Manchester United din za ta yi zawarci a karshen kakar wasannan inda tuni rahotanni suka bayyana cewa kungiyar ta fara Magana da wasu daga cikin wakilan ‘yan wasan.
1. Mauricio Pochettino.
2. Laurent Blanc.
3. Zinedine Yazid Zidane.
4. Ole Gunnar Solskjaer.
5. Marco Rose.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: