Connect with us

WASANNI

Neymar Ya Fi Kowanne Dan Wasa Daraja A Duniya

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta P.S.G kuma dan asalin kasar Brazil wato Neymar ya zamo dan wasan da yafi ko wanne daraja a duniyar kwallon kafa a yanzu kuma ya sami wannan abinne bayan ya sha gaban Leonel Messi da dukkan sauran ‘yan wasan.
Sai dai daga cikin ‘yan wasa guda 10 da kididdigar ta nuna anfitar kwata-kwata babu Cristiano Ronaldo inda wannan hukuma ta KPMG ta fitar, inda tace shi Ronaldo a gasar Serea A yafi kowa daraja amma a duniya jimilla ko a jerin ‘yan wasa 10 babu shi.
Shima Messi reshe ya juye da mujiya domin kuwa shima ya koma mataki na 3 a wannan jaddawalin da aka fitar
Ga jerin ‘yan wasan 10 da aka fitar, amma zamu kawomuku su daga na 10 zuwa na 1.
10. Philippe Coutinho na Barcelona inda darajarsa ta kai €118.2m (£106.5m).
9. Paul Pogba na Manchester United inda darajarsa ta kai €119.3m (£107.5m).
8. Antoine Griezmann na Atletico Madrid inda darajarsa ta kai €125.6m (£113.2m).
7. Kelvin De Bruyne na Manchester City inda darajarsa ta kai €129.4m (£116.6m).
6. Eden Hazard na Chelsea inda darajarsa ta kai €148.2m (£133.5m).
5. Harry Kane na Tottenham inda darajarsa ta kai €151.1m (£136.1m).
4. Mohamed Salah na Liverpool inda darajarsa ta kai €168.3m (£151.6m).
3. Lionel Messi na Barcelona inda darajarsa ta kai €203.3m (£183.2m).
2. Kylian Mbappe na P.S.G inda darajarsa ta kai €215m (£193.8m).
1. Neymar na P. S.G inda darajarsa ta kai €229.1m (£206.5m)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!